22

16 3 2
                                        

SOFIA
NOBLE WRITERS
EP_22

*BONUS PAGE FOR FREE*

SAGEER POV
9:00pm
Ya yi ɗai ɗai a katafaren ɗakin Ahmad wanda yake gidan Arc. Lawal, Saboda girman kan shi ba zai iya kwana gidan Baffah ba sai ya je gidan surukan shi mahaifin Nadiya, gidan da Ahmad ya taso tun yana karami nan ɗakin ya yi masauki ma kan sa.

Misalin karfe tara daidai na dare aka kirawo shi a waya, yana ɗagawa ya ce " Sam na san ka ba wasa shiyasa na nemo ka" Ya saurara yaji abin da Sam zai faɗa, cen kuma ya kwashe da dariya ya ce" Don Allah da gaske kake Sam kana ina ne yanzu?"

"Continental Hotel, Okay gani nan" ya dakata yana jin abin da Sam yake faɗa sai yace,"Kai kasan yadda na ba ma mission ɗinnan muhimmanci kuwa, ba zaka gane bane, to ba ire ire mission ɗin da ake yi a american bane years back" suka sake kwashewa da wata dariyar Sageer yace,"Gani nan dai"

DUTSE EMIRATE
9:00pm

Farkawa ta yi daga nannauyan baccin da ya ɗebe ta tun bayan da ta yi sallar magrib, a wajan ta kwanta.....a hankali ta ke kwala kiran Badi'a kasancewar Mai martaba ya ce ta rinka kwana a saahin saboda Sofia ko zata bukaci wani abun, nan da nan ta shigo tana durkusawa har ƙasa,"Barka da tashi ranki shi daɗe, tun ɗazu nake zagayo wa na duba ko kin tashi"

"Wallahi baccin yayi nauyi, Badi'a, me kika dafa?"
"Shinkafa da wake da miya, sai nayi farfesun kayan cikin da Mai martaba ya aiko da shi ɗazu, sai......" ya isa hakanan kawo mun shinkafar kawai Farfesun kuma ki ɗiba ki sa sauran cikin frij gobe sai a karya da shi"...Idan kin kawo kije sashin Fulani Mami ki ɗauko min wayar tarho ki kawo mun" ta karashe maganar da hausar da tasan zata gamsar da Badi'ar don bagidajiya ce.

Sofia ta gyara zaman ta na zaune ta lumshe idanu zuciyar ta yafi karkata ga tunanin halin da Abhi ya ke ciki, ta wani ɓangare kuma ta damu ta kira Yarima ne saboda bazata manta da irin taimakon da yayi mata ba a rayuwa, tana wannan tunanin sai ga Badi'a ta shigo ta ajiye kayan abinci sannan ta koma ta ɗauko aikin a hankali ta ce mata ki samin ruwan zafi a bayan gida na idan na gama zan yi wanka sai ku kulle kofofin da suke a buɗe. Badi'a ta amsa cike da ladabi.

A hankali ta kai hannu ta latsa lambar da Mai martaba ya bata, ta danna kira , Bugu ɗaya biyu ya ɗauka tun kafin yayi magana ta furta sallamarta cikin siririyar muryar ta mai daɗin sauraro.
9:00pm
MAITAMA DISTRICT ABUJA

Keɓantaccen corridor ne wanda aka ƙawata shi da ado, yana kwance saman lallausan couch wanda ya lume cikin lallausan bargo, saman cikin sa system ne yana nemo bayanai akan daɗɗaɗan mafarkin yana son yayi karatu akai wato ilimin taurari.....Karar wayar sa ta sanya ya juyo a hankali saman karamin mini table ɗin dake kusa da shi, lambar wayar tayi daidai da lambar da aka kira sa ɗazu, ya ɗauka babu bata lokaci ya yi sallama"Assalamu alaikum"

A tare suka saki sallamar yayin da duk suka ɗauke wuta, lokaci guda numfashin su ya soma bugu sama sama musamman na ta...Tattaro natsuwar ta wace guda kafin ya tsinkayi siririyar muryar ta tana amsawa,"Amin wa'alaikums salam wa barakatuhu" "Ina yini" ta numfasa sannan ta yi shiru, ya rasa me yasa idan yana tare da ita yake jin bugun zuciyar sa ta sauya, ya amsa yana cewa,"Lafiya lau, ya kike?"

"Alhamdulillah, dama na kira ɗazu ne in gaishe ka kuma......." sai ta dakata maganar ta sarƙe wanda shi kuma ya samu kan sa da murmusawa ya ce,"Kuma sai ban ɗaga ba ko, To afuwan katsewa ta yi kafin na ɗaga"

Kasa tattaro natsuwar ta tayi saboda bata taɓa tsammanin zata kira har ya ɗaga wayar ba da sauri ta tattaro sauran kuzarin ta ta ce,"Allah ya kara sauki, sai da safe" kafin ma ya kara kalma ɗaya dif ta kashe wayar abin ta.....Ya yi murmashi, shi ba don yadda yake ganin duhun fatar wannan Sofiyar ba da zuciyar sa zata yardar masa ita ce Macen da ya jima yana nema.....Zai so ya kula da ita amma zuciyar sa tafi yarda da ya nemo ɗayar Sofia don ba zai karaya da wuri ba duk da ance ta ɓace ne....ama bai san ta ina zai fara neman ta ba, Ya kishingiɗa yana tunano siriryar muryar SOFIA matar sa, ya tuna ranar da ya ɗauko ta cak daga wannan ɗakin sam bata da nauyi ama kuma akwai dirin jiki dk da a zaune ya hango ta kallo ɗaya yayo mata ya tabbatar da cewa Allah yayi halitta a wajan....ya lumshe idanuwan sa ya ce,'He's no after that, he only wanted to help shiyasa har ya yarda ya aure ta, if not da zasu iya sake kawo mata farmaki' duk cikin zuciyar sa yake wannan tunanin tuni ya manta da zancen Sofia wacce yake nema har bacci ya ɗauke sa.

10:00pm
SUMMERSET CONTINENTAL HOTEL

Da misalin karfe goma ya parker a harabar hotel ɗin yana kira lambar wayar SAM, ya ɗaga yace,"Okay kana Swimming pool" Yayi maganar yana karasawa ta bayan building ɗin ya samu Sam zaune a fancy chair dake gefen wasu rumfuna haka yana shan barasar sa.

Sageer ya zauna, Sam ya mika masa cup akan ya zuba, Sageer ya ce,"Man na jima da dena sha ai, i prefer mocktail" Sam ya kira waiter ya bashi order sannan suka fara hira.

"To wai dama a Jigawa yarinyar take ne?"

"Eh mana, tun da Abhi ya ɗauke ta ya gudu da ita cen Dutse and da ga nan suka fara bara dama abin da nake so kenan.

Sam ya kwashe da dariya ya ce,"Baka da kirki Sageer, Ka san wani abu ina mai tabbatar maka wabillahillazi aikatau take yi a gidan sarkin dutse"

"Kai haba don Allah" Sageer ke tambaya yana kai mocktail bakin sa yana sipping, iskar wajan tana kaɗawa yayin da sanyin swimming pool ɗinnan yana bada wani daddaɗan sanyi mai sanyaya zuciya....ya ma manta da batun iyalan sa, yadda ya rungumi damuwan neman wannan yarinyar Sofia bai san ya damuwan son ganin ƴaƴan sa a rai ba kamar son a nemo masa Sofia ko a rai a mace......ya buɗe jajayen idanuwan sa ya kalli babban aminin nashi wanda tare suka yi karatu a UK shi yanzu yana aiki anan ne.....ya san mutane da yawa shiyasa ya ɗaura sgi akan aikin, a hankali ya ɗaga waya ya kira a bokin sa police ya masa magana a waya daga bisani ya kashe wayar ya kara lumshe idanuwan sa yayi relaxing yayin da ya ɗaura hannayen sa saman keyar sa kamar mai nazarin wani abu.

"Sageer ina fa maka kashedi, killing her won't be the solution to your problems"

"Really?", How sure are you Sam" Sageer ya tambaya ya buɗe jajayen idanuwan nasa yana huci, abokin sa ya ce,"Take it easy man"

"No,nooooo, you have no clue on how those people both kill and ruin my family"

"Duk da haka, kai na miji ne, kai babba ne think of other way out, but not killing i guess"

Sageer yayi shiru yana kallon shi sannan ya ce,"Are you sure she is a maid in the Emirate palace of Dutse?"

"Am very very sure Sageer"
"Okay i'll make sure she live as a maid till eternity of her life"

"Better" Cewar Sam yana ɗaura agogon sa ya mike yana cewa,"Man i've to go, my family are in need of me right now"

"Alright, see you later" suka kayi musabaha da hannu, sannan ya tafi.

©FADILA IBRAHIM

SOFIA ✔Where stories live. Discover now