SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_21
*BONUS PAGE FOR FREE*
ANNA SPECIALIST
Ba tare da bata lokaci ba,bayan fitar Hadiza Anna ta sanya Dr.Eshaan ya taimaka aka fito da Abhi aka sanya shi motar ambulance haɗe da oxygen ɗin, Baffah da Nainah suka bishi yayin da Sageer tuni shima ya fice daga asibitin yana huci.
Anna na offishin ta ta haɗa kai da desk kan ta ne yake sarawa hankalin ta ya yi matuƙar tashi da maganganun Sageer, tunawa ta yi da kuma kaman gaskiyar sa ne kamar sakacin su ne ya sa suka rasa SOFIA kuma da ƴar su ce ba za su bari ta kai wannan lokacin ba a samo in da take ba, ta shi ta yi ta bisu gida ta same su suna ta shirya ɗakin da aka kwantar da Abhi Dr.Eshaan ne ke ta ɗawainiya yayin da Anna ta wuce ta shiga sashin sofia da ya jima a kulle ta ɓalla kwaɗon ta shiga duk yana ya ɓata ɗakin saboda babu mai shiga, babu mai rayuwa a sashin kamshin kayan ta yana nan kamar dai tana nan, keken guragun ta na nan a gefen gadon ta shafa sunan SOFIA da ya fito ɓaro ɓaro saman wheel chair ɗin, wasu hawaye ne masu zafi suka sauka zuwa kuncin ta ta ce,"Ina kika shiga ne ƴa ta Sofia Anna na kewar ki, Anna na tantama akan riƙon da tayi miki, Sofia ki gafarce ni ni da Baffah bamu baki tsaron da ya dace ba gashi kin yi nesa da mu"......Karar wayar ta ne ya sanya ta yin shiru asibitin Maitama ta maimaita, da kamar ba zata ɗauka ba daga baya ta amsa wayar tana mai yin shiru ta kara wayar da kunnen ta.
"Madam.....ma'am your daughter Hadiza Ibrahim Baffah was admitted in Maitama district hospital now"
"What???
""Yeah Ma'am, Sorry ma'am" mai bada sakon ta kashe wayar.
Da gudu Anna ta fito daga ɗakin, ta samu Baffah a ruɗe take magana tana faɗa masa, Hadiza ba lafiya an kwantar da ita a asibitin maitama" ai bata rufe baki ba, Dr Eshaan ya ce suje zai kula da Abhi shi da Nainah, Chioma na gefe ma tana tausayin yanda Madam ɗin ta ta rude a kwanakin nan.
Cikin mintuna kalilan suka karasa asibitin, suna zuwa emergency ta samu Yarima Omar zaune a kifar mashigar ɗakin, kamar za ta mishi magana sai kuma ta tura kofar ta shiga ciki ita da Baffah, sun samu Dr.Ema yana ta rubuce rubuce yayin da Hadiza idon ta biyu tana shan drip, Dr.Ema ya ce,"Dr.Anna welcome, muje office ɗinki mu tattauna a cen zai fi"
Hadiza na kallon Anna, sai ta share wani guntun hawaye ta lumshe idanuwan ta juya kanta tana kallon gefen bango., suna shiga office ɗin Anna suka shiga, Anna ta ce,"Dr. Ema me ke faruwa ne?
"Doctor kiyi hakuri ko, Daughter ki ta yi ɓari, saboda jinin ta da ya sauka sosai maimakon ya hau sai ya sauka, to mun bata drugs amma mun kasa ceton 4month pregnancy ɗin da yake jikin ta", Ya na kai wa nan, Anna ta ce,"Subhanallahi" ta manna kanta da desk ɗin dake gaban ta, azababben ciwon kan dake addabar ta shine ya kara tsananta ya kuma haifar da jiri tana kokarin mikewa ne Baffah yayi saurin taro ta, yana cewa "Anna calm down, Zauna ko Rayuwa cike yake da jarabawa kala kala, mai kyau da mara kyau, duk karfin mu ba za mu iya canja shafin jarabawar mu ta kowacce rana ba, ki kwantar da hankalin ki don Allah kafin mu bar asibitin nan, Baffah ya kalli Dr.Ema ya ce ,"Dr. my wife needs attention right now, tana cikin damuwa sosai and she needs something that will calm her down"
"Alright am coming" Dr. Anna come and relax here please"
Anna ta kwanta saman gadon da take kwantar da marasa lafiya a times, ya duba BP ɗin ta, jinin ta na hawa yana sauka, don haka ya rubuta ma Baffah magunguna ya ce, "a je ya siyo a pharmacy" jim kaɗan Baffah ya dawo da aka bata har da allurori, sannan ya fita ya kulle office ɗin ya tai wajan Hadiza, a bakin kofar ya ci karo da samari guda biyu ya ce,"Ku ne kuka kawo Hadiza asibiti?
"Eh Baffah mune" Abdussamad ya faɗa yana shafa ƙeya ya ce,"Na san ma baka gane ni ba, Abdussamad ne jikan Talba"
"Okay sai yanzu na gane ai duk dama ban san ka sosai ba ka san jikokin da yawa kuke" cewar Baffah
YOU ARE READING
SOFIA ✔
Короткий рассказNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...
