17

7 1 0
                                        

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_17

"Aure Sofia na"

"Da wa, Abhi aure fa ka ce, Abhi me yasa ka aurar dani, Abhi buri na shi ne nayi karatu mai zurfi ban tsammaci auren gaggawa a cikin rayuwa ta na yanzu ba "

Abhi yayi saurin kama hannayen Sofia ya ce,"Look Sofia ban amince ba sai da na tabbatar za a kula min da ke ɗari bisa ɗari, kuma sannan aure baya hana karatu, "Sofia na ki kwantar da hankalin ki domin kuwa Yarima da kan sa ya amince da auran ki don ya rufe baƙin tabon da aka yi miki"

"Abhi amma ina tsoron masarauta koma wacce iri ce, Abhi ta yaya zan fara rayuwa da mutanen da ban san su ba,ta yaya zan faranta wa Yarima bayan ni nakasasshiya ce, ta yaya komai zai faru Abhi?, "Wa zai kula da kai?

Wani zafi Abhi ya ji a kirjin sa yayi saurin dafe wajan da hannun sa yana yamutsa fuska,baya son Sofia ta gano ainahin ciwon da ke addabar zuciyar sa a ƴan kwanakin amma daga jiya zuwa yau matsalar ta fara yawa gakan baya da nasaba da jarabawar da ta samu Sofia a daren jiya.

Ni kuma ina zaune waje guda na runtse idanuwa na ban san me ke faruwa da Abhi na ba, da ƙyar ya mike tsaye har ina tambayar sa me ke damun sa? amma sam ya ce min babu komai.

Bayan fitan sa, Jim kaɗan Maman Ummi ta shigo ta na guɗa, hannun ta ɗauke da bokiti wanda ban san ko miye a ciki ba, ta ce,"Ma Sha Allah, Tabarakallah Sofia ina matukar taya ki murna da zama matar ɗan sarki guda mai jiran gado"

"Ina nan zaune kamar yadda Abhi ya fita ya bar ni,"Maman Ummi wallahi bana farin ciki da wannan auren, wallahi har cikin zuciya ta bana fatan shiga wata matsalar da ban san hanyar ɓillewa ba"

"Rayuwa a gidan sarki shine shiga matsala Sofia, ko dai karshen wahalar ki ta kau, ni taho muje kiyi wanka da ruwan lallin nan, Tun kafin Abhi ya fita ya bani umarnin na gyara ki kafin ya dawo," Maman Ummi ta zauna ta kalle ni ta ce,"Ya kamata zuciyar ki ra yarda da cewa Abhi ba zai taɓa kai ki ga halaka ba, ba kuma zai kai ki inda baza a daraja ki ba, ban shiga gidan sarki ba yau da naji abin da ke faruwa amma duk abin a ke ciki tun da anan nake aiki zaki rinka gani na kullum Sofia ina tare da ke a ko wani hali"

Da taimakon Maman Ummi nayi wanka, na shafa mai zuwa wannan lokacin Abhi ya dawo da kaya niqi niqi a hannun sa, daga ciki muka duba wanda zan yi amfani da shi, kayan shampoo muka ɗiba Maman Ummi ta wanke min kai na sil sil har tana min tsiya wai ita bata taɓa ganin macce mai gashi iri na a najeriya ba a cewar ta wai kamar ni ba ƴar ƙasar najeriya ba.

Na yi wanka babu yabo babu fallasa, abaya na sanya sabuwar abayar da Abhi ya siyo min ruwan madara, sannan na yafa wani babban gyale fari ta tafi da ni uwar ɗakar ta, yayin da ta gyara falon ta ta sanya turaren wuta sai kamshi ke tashi saboda ainahi daman Maman Ummi mace ce wanda bata yadda da ƙazanta ba.
04:20
Da misalin ƙarfe huɗu da minti ashirin muka jiyo sallamar ƴan ɗaukar Amarya, Maman Ummi ita tayi musu iso har falon ta, suka shigo da akwatuna dozen sha biyu daga nan Maman Ummi ta kwaso musu tukwicin da Abhi ya siyo ɗa zu.

Tun kafin isowar su gidan idanuwa na suka cika da hawaye ina mamakin wai ni aka ɗaura ma aure da wani kafar zan yi rayuwa da miji, Wata zuciyar ta ce, Nakasa ba kasawa ba ce Sofia, ki fawwala wa Allah koma yanda ya yi farko haka zalika zai yi karshe mai kyau In Sha Allah.
Ina sauraron lokutan da suke ciro alkyabba suna miƙawa Maman Ummi suna cewa a sanya mata yanzu zamu tafi da ita gidan auran ta"

Maman Ummi ta same ni kan gaɓar da na ke son yin kuka tana shigowa na rungume ta tsam ina kuka wiwi wiwi kamar dai jaririyar goye, da kyar na san ya alkyabbar wanda ta maruƙar amsar fatar jiki na, da taimakon ta ta ɗaura ni saman katakon ta tura ni muka fita zuwa falo, haƙiƙa na tsinci wasu daga cikin masu ɗaukar Amarya suna kus kus akan dama ca gaske Amaryar gurguwa ce kuma mabaraciya ce?

SOFIA ✔Where stories live. Discover now