SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na HuɗuPRISON CENTER ABUJA
Babban gate ɗin kurkun dake garin Abuja wanda ake buɗe karamar kofa a yayin da idan mutum zai fita kwalli ɗaya.
Guguwar da take tasowa haɗe da iska mai daɗi tana karka ɗawa kasancewar dajin wajan na ɗauke da shukoki da bishiyoyi sai ni'imar wajan ya ba da wani kala mai ban sha'awa.
Fitowar sa da taka ƙasar da yayi sai ya kasance kamar dokin da ya buga kafar sa a ƙasa yake sukuta yayin kilisa., Kafafuwan sa suna ɗauke da wani mutaccen takalmi wanda ya sha ɗauri sau ba adadi, wandon jikin sa baki ya sauka kasan gwiwa wanda da alama nannaɗa ya sha, rigar jikin nasa kuma babba ce dark bliu ɗinkin yadi wanda ya sha jiki mai guntun hannu, fuskar sa kuma gashi mai haɗe da furfura ya taru yayi yawan da ya rufe masa ainahin surar fuskar ta shi kamannin sa na ƴan sudan yana nan.
Aka miko masa ragowar kayan matar offisan na cewa,"Ga gayan matan ka Laila wacce ta jima da mutuwa"
Runtse idanuwan sa yayi yana jin zafin rasuwar matan na sa, yadda kasan suka yaji a cikin zuciyar na shi, nan da nan rayuwa da shekarun baya suka dawo kwanyar kansa ya karɓi kayan ya wuce.
Kai tsaye gidan Arc.Ibrahim Baffa ya nufa ya samu securities da yawa a kofar gate ɗin.
"Wa kake nema ne? Ya ji wani murya da alama soja ne, kallon matashin yayi wanda bugu ɗaya zai masa ya aikashi lahira amma sai ya saukar da kai ya ce,"Anna nake nema"
Security officer ɗin ya ce,"Anna sun fita, babu kowa a gidan"
Ya gyaɗa kai sannan ya samu waje daga gefen bangon gidan ya zauna ya ajiye kayan dake hannun sa, ya ce da security ɗin,"Yunwa nake ji"
Tausayi yasa security ya taimaka masa da breakfast lin da aka kawo musu na safe wanda ko ci ma ba suyi ba, Irish ne da kwai har da fanta ga kawo masa"
Yayi godiya bayan ya gama ci ya sha ruwa ya tashi ya bar wajan da niyar gobe ma zai dawo, duk dama bai san ina ne zai je ya kwana ba.
MAITAMA DISTRICT ABUJA
11:00amNa jima da likita ya sallame ni, idanuwa na da suka gama jikewa da hawaye na sanya tissue na share ragowar hawayen ina zaune ne ni kaɗai a office ɗin Anna, yayin da sanyin A.C ke ratsa ni na tsinci kai na da son fita wajen asibitin don nayi was saboda Anna ta ce tayi waya da teacher na kuma ta shada mata bani da lafiya sai gobe zan zo Ida Allah ya kai mu.
Na kunce gefen keken ina turawa a hankali bayan na ɗauki karamar wayar Anna saboda koda ace ma zata kira ni da shi sai na faɗa mata in da nake.
Har na karasa kasa farfajiyar filin asibitin wajan da ake parker motoci, na nufi wani ɓangare da naga ana zama, sai dai wajan da tsantsi ɗayan wajan kuma matakalar bene ne na sauka zuwa ƙasa...na jima zaune a wajan ina kare ma duk wanda yazo wucewa kallo.
YARIMA OMAR POV
Yana tsaye a gefen Mami tun da suka gama da likitan ya basu magunguna, Mami tace zata biya bill wai ga wan da zai yi ne ya hango wata karamar yarinya fara zaune cikin keken guragu tana tura kanta, ta ɗauke mishi hankali, Fulani Mami ta janyo hannun sa tana cewa zo mu je mu karɓo sauran maganin a pharmacy kwanar da suka sha shiyasa ya dena ganin Yarinyar.
![](https://img.wattpad.com/cover/352888948-288-k908000.jpg)
YOU ARE READING
SOFIA ✔
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...