Shafin na Biyar

21 2 0
                                        

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na biyar

10years later

Monday 18th Dec
The Regent Secondary School
*Speech and prize giving day*

Babban hall ɗin Regent Secondary School dake kan titin Maitama Abuja, taron motoci ne bila adadin na masu kuɗi da sauran su.....cunkoson dake kofar mashiga makarantar shi ya janyo traffic ɗin da motoci suka yi layi suna ta shiga ciki don amsa gayyata.

Manya manyan shahararrun mutane daga kowanne sassa da nahiyar najeriya masu mulki da sarauta kama daga kan fitattun fuskoki, mawaƙa da jaruman film. A yau ne ake bikin yaye ɗaliban Regent Secondary School, yayin da iyayen su suka samu damar halartar taron da makarantar ta shirya na musamman.

Katafaren filin makarantar cike yake taf da mutane da ɗalibai, da kuma malaman makatantar. Mutanen da aka gayyata da suke zazzaune akan kyawawan kujerun roba masu kafa huɗu, matsakaita an rufe su ruf da fararan yadi mai riga hakan ya taimaka wajan sake ƙawata harabar filin makarantar daya wadatu da kayan ado cikin mabanbanta launika tun daga kan baloon baloon, tutoci, flawoyi, kyallaye da suka haɗu sai suka bada wani irin launi mai shagaltar da mai kallon su, Gefen ɗaliban da za a yaye suna sanye cikin kayan makaranta wanda kowannen su ya sha guga bugu da kari suka ɗaura graduation gown.

Wani ɓangare shuwagabannin makarantar da malaman makarantar suna zaune a keɓance wato kan stage, Tsakiyar filin da aka bari don gabatar da wasanni nan aka soma gabatarwa babu kakkautawa, daki daki daga bisani aka fara kiraye kirayen best student wanda sai daga karshe aka kirawo sunan ta cike da shauki suna kara jinjina mata domin itace ɗalibar da ta fi kowacce ɗaliba hazaka kaf cikin makarantar an bata lambar yabo na ɗaya.

*SOFIA IBRAHIM BAFFAH*

Shine cikakken sunan da take amsawa tun fara makarantar da har kawo yanzu data girma kuma ta kammala sakandiri.

Harabar filin kowa yayi shiru an baza idanuwa kowa yana son idanuwan sa su gane masa yarinyar.....yayin da karar tura keken nata ne yake amsakuwwa a cikin kunnuwan bil'adama, fuskar ta na sauke kasa annurin daya bayyana a fuskar nata mai cike da kunya da gogewa irin ta masu ilimi da sanin abin da suke yi, ta fito kan dandamali gaban taron jama'an da duk hankalin su yake kanta.

A lokacin da kalma ta fara fitowa daga bakin ta cikin sautin ta mai taushin amo sai duk mafiya yawan mutanen wajan hankalin su ya koma kanta Yayin da sukayi kasaƙe suna sauraron lafazinta tana larabcin ta duk da cewa addu'a takeyi amma sai suka gwammaci dama ta cigaba da magana da larabcin saboda daddaɗan kalmomin yadda suke fitowa daga bakin ta abin ya matukar bada citta.

Daga nan aka bata kambun girmamawa, haɗe da kyautuka masu ban mamaki da girma...Baffah da Anna suna kan stage suna ɗaukan hoto da Sofia.

Karfe huɗu kowa ya soma watsewa bayan an sha shagalin yaye ɗalibai, Baffah na kujerar gaba tareda direba, Anna na baya Sofia ta kwanta a cinyar ta idanuwan ta biyu ta faɗa zurfin tunani.

*Few Month Later*

Kamshin turaren miss anna cherie ya mamaye lungu da sako na cikin ɗakin nata wanda tun daga bakin kofa yake fara yiwa masu shigowa maraba, ɗakin duhu duhu yayin da lallausan karpet yake manne da katakon gadon nata mai kama da gadon sarauta na yara.

A hankali ta tashi zaune ta linke tattausan blanket ɗinta, ta sanyo kafafuwan ta kasa tana shirin janyo kekenta kawai ta turguɗe ta faɗo ƙasa kara tayi kaɗan haɗe da ambaton sunan Allah daga cikin karamin laɓɓanta mai kalar pink....ta ciza yatsa tana kokartawa don ganin ta mike ta zauna amma da kamar wuya tun tanayi da karfin da Allah ya bata har ta soma hawaye komawa tayi saman lallausan karpet ɗin tayi lamo tuni hawaye suka som sauka daga idanuwan ta zuwa kuncin ta, adaidai lokacin Anna ta shigo sanye cikin doguwar riga da shirin tsab zata tafiba asibiti.

SOFIA ✔Where stories live. Discover now