1

43 5 6
                                    

Nadia's POV,

24th April, 2024

A gaggauce nayi saurin bude idona jin kamar rana na haske min idanuna na. Bude idona keda wuya kuwa naga kaman har safiya ta fara yi ae tuni na tashi a guje na fada bayi na dauro alwala nazo na tayar da sallah.
Bayan na idar na shafa addu'a ta, nan na tashi kannena guda biyu domin suma su gabatar da tasu sallar sannan su fara shirin makaranta inda ni kuma na fara shirin dora mana karin kumallo.
Saboda yanayin damuna, dakyar na samu wutar ta kama domin itacen duk a jike yake. Nan da nan na dama mana koko da yar ragowar gasarar data rage mana na zubawa kowa a kofin sa hakanan domin kuwa ko sukari bamuda shi.
Nan na dauko naira 100 na bawa Mus'ab da Jalila hamsin hamsin daganan na raka su soro ina me kara tuna musu dayin azkhar da kuma addu'an fita daga gida.
Nan na zauna na bawa Maryam nata kokon ina me Mata wasanni ita kuma tana min gwaranci irin na yara. Anan na zauna nasha nawa kokon inda daganan na gyarewa baba dakinsa.
Daga nan nayi wanke wanke na gyare gidan wanda ya dauke ni tsahon lokaci domin kuwa ina da nauyi wajen yin aiki.
      Suna na Nadia kuma nice 'ya ta farko a gurin iyayena. Mahaifiyar mu ta rasu shekaru biyu da suka wuce bayan ta haifi Maryam a sakamakon cutar yoyon fitsari data kamu dashi. Ta rasu a lokacin ina da shekaru goma sha hudu a aji na karshe a secondary kuma ta bar mana Maryam tana da karancin shekara daya a duniya.
Nan na bar ta ta cigaba da wasan ta inda ni kuma na nufi dakin girkin mu domin dora girkin rana domin nasan baba yana gab da dawowa daga aikin kwanan daya je domin kuwa baba ya kasance lebura ne a wani karamin asibitin gwamnati dake unguwar mu, da kuma wannan aikin ne muke samu muna lallaba rayuwar mu.
Nan da nan na dafa mana taliyar hausa wadda na murza da kaina sannan na goya Maryam domin zuwa shago siyo manjan da zamu hada da taliyar. Ina dawowa na tarar da Baba a kofar gida yana kokarin bude kofar da nashi mukullin. Nan nayi mishi sannu da zuwa inda ya amsa min da murmushin nan da baya rabuwa da fuskarshi a kullum, murmushin nan dake yaye min duk wata damuwa danake ciki da zarar nayi arba dashi.
Muna shiga na sauke Maryam a tsakar gida na nufi dakin girki domin soya manjan inda baba kuma ya fada bayi domin yin wanka. Ina daga ciki na jiyo sallamar Jalila da Mus'ab sannan suka fara kwala min Kira kaman sun bani ajiya. Nan na leko na musu sannu da zuwa sannan na koma kitchen inda na zuba mana abincin a babban tray domin kuwa in dai har baba yana gida, haduwa muke muci abincin tare.
       Nan na shimfida mana katuwar tabarma a tsakar gida inda nan muka baje muna cin abincin mu cike da kaunar juna inda su Mus'ab ke bawa baba labarin makaranta ni kuma na maida hankali na wajen bawa Maryam abinci. Muna gama cin abincin muka shirya muka tafi Islamiyyah inda muka bar baba a gida yana huta gajiyar aikin kwanan da yayi.
    Gab da magriba muka shigo gida inda nayi maza na cire uniform dina na fada kitchen domin dora tuwon dare. Nan da nan na tuka tuwon nayi sallah sannan na kada miyar kuka na sa mana man shanu. Bayan an idar da isha nan muka kuma zama muka ci abincin mu inda baba ke hira dasu Jalila. Muna gamawa kowa yayi shirin bacci ya kwanta a yayin da ni kuma na goya maryam sannan na harhada kayan da muka bata nayi wanke wanke.
    Nan na kwantar da maryam sannan nima na kwanta a gefan ta bayan na shafe mu da addu'a. A kullum dare sai nayi da gaske bacci ke iya daukata domin kuwa lokacin ne kewar umma take kamani a yayin da nake tuna irin rayuwar da muke yi kafin rasuwar ta. Ban taba tunanin akwai ranar da zamu wayi gari ummah bata duniyar ba amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi. Nan na mata addu'ar samun rahamar ubangiji inda daga nan bacci barawo ya sace ni.



Assalamualaikum jama'aaaa
Kaunar dake tsakani  na da fara rubutun novel lokacin exams na 5&6
Allah ya dai ya bani ikon cigaba da rubutun
Wannan littafin is very dear to my heart.

Rayuwar Nadia Where stories live. Discover now