NADIA.
Mummunan gani idona ya sake yi min domin kuwa Baba na hango ya fadi kasa hannun sa dafe da zuciyar sa nan take tsoro ya kamani domin kuwa baba yana da ciwon zuciya kuma likita ya tabbatar mana yana gejin karshe a ciwon.
Ae bansan sanda na saki wani razananne kara ba Wanda ya firgita Maryam dake bayana ya kuma janyo hankalin mutane dama. Ganin hankalin mutane yayo kanmu nan na fara rokon da su taimaka su daukar mun Baba da Jalila domin muyi gaggawar kaisu asibiti. Da kyar dai na samu aka tarar mana adaidaita sahu aka saka min Baba da Jalila a ciki muka rankaya zuwa asibitin da Baba ke aiki.
Muna zuwa na fito ina kwala kiran likita, likita, likita, ku taimaka mun dan Allah ku taimaka mun kar na rasa su suma. Nan da nan aka zo da keken marasa lafiya aka dora su a kai domin shigar dasu asibitin.
Nan likitoci suka rufu a kansu domin ceto rayuwarsu a yayin da ni kuma na kasa zama ga Maryam tana ta kuka Mus'ab ma nayi. A lokacin nikam ko kukan ma kin zuwa min yayi domin ji na nakeyi kaman ba zuciya a jikina. Duk bayan dakika nake kallon dakunan da aka shigar da Baba da Jalila.
A lokaci daya kofofin dakunan suka bude inda likitocin suka fito a tare kaman hadin baki suka bude bakin su wajen sanar min da mummunan labarin daya tarwatsa duk wasu gabobin jikina, labarin da zai ta min amsa kuwwa a kunnena har karshen rayuwa ta. Kai anya ma kuwa kunne na gaskiya ya jiyo min, ae da gudu na bangaje likitan na fada dakin da aka ajiye Babana abun sona amma sai naga anja bargo an lullube mishi fuskar shi dashi. Nan take nayi saurin janye mishi bargon inda kamilalliyar fuskar shi Wanda bata taba rabo da murmushi ta bayyana. Fuskar nan tayi fayau tana fitar da annuri naga kaman murmushi yake min. Nan take na hau jijjiga shi sai dai ba alamun yana motsi ko kuma jina, Baba ka tashi Baba ka tashi, ka tashi dan girman Allah Baba, banda kowa idan ba kai ba kar kasa na kara zama maraya Baba.
Janye ni wasu dasu cikin ma'aikatan suka farayi amma ina, sun kasa matsar dani daga jikin shi domin ba karamin riko nayi mishi ba. Kamar wadda ta tuno wani abu kuma nayi saurin sakin shi na fita da gudu daga dakin na fada dakinsa Jalila take. Nasan ita bazata taba tafiya ta barni a wannan duniyar ba. Itama dai a kwance na hangota ba alamun rai a tare da ita. Jalila, Jalila ta, ki tashi dan Allah kinga Baba ya tafi ya barmu karki min haka Jalila ki tashiiiii na fada ina jijjiga ta ina jin ina ma nima Allah ya dauki raina a wannan gabar.
Jin da nayi ana taba ni yasa na waigo domin ganin me taba ni. Mus'ab na gani rungume da Maryam yana kuka shima. Nan na rungume su ina me goge hawaye na, astagfirullah Allah ka barni a raye ko dan in kula da yan uwana da suka rage min a duniya.
Yaya, yanzu shikenan Baba da Jalila sun tafi sun barmu mu kadai kaman yanda ummah ta tafi ta barmu. Kayi hakuri Mus'ab ko wani me rai mamaci ne, Wanda yafi mu son Baba da Jalila ya karbi abun sa. Addu'ar mu kadai suke bukata a halin yanzu kaji dan uwana.
Nan da nan aka saka mana su a motar asibiti inda nida Mus'ab muka zauna a gaba domin tafiya gida. Muna shiga unguwar mu na nuna musu gidan aka sauke mana gawar sannan suka tafi.
Rashin sanin abunyi da rashin madafa yasa na zauna ina kallon su kawai domin kuwa kaina a kulle yake bansan ya zanyi ba. Nan na aika Mus'ab ya sanar da liman tareda wasu makotan mu. Cikin mintuna kalilan gidan ya fara cika da mutane, kowa yazo kallon tausayi yake jifa na dashi.
Nan liman da wasu maza suka yiwa Baba wanka inda wata makociyar mu ts taimaka mun muka wanke Jalila aka shirya su domin kaisu gidan gaskiya.
Duk abunda ke faruwa ganin shi nakeyi kaman almara, kaman wani mummunan mafarki Wanda nake fatan wani ya tashe ni cikin gaggawa.
Kaman daga sama na fara jiyo muryar Baba Musa wanda ya kasance Kani ne ga Baba. Cikin fada da daga murya yake cewa, yanzu a ce dan uwana ya mutu amma a rasa me sanar dani sai dai inji a gari, kaman ya damu da dan uwan nasa na fadi haka a zuciya ta. Hango ni da yayi a gefe yasa ya karaso gabana yana me fadin nasan bame yin haka sai ke fitsararriya me bakin hali irin na uwar ta. Ban dago kai na kalle shi ba domin in da sabo yaci a ce na Saba da yadda yake nuna min kiyayya kiri kiri ko kokarin boyewa bayayi amma ni yau bashine a gabana ba, mutuwar Baba ta Jalila ta taba ni fiya da zato ko tsammani.
Bayan an gama shirya su, nan liman ya umarci nida Mus'ab da mu shiga muyi musu addu'a da bankwana.
Dagaske dai Baba da Jalila sun tafi sun barmu kaman yadda umma ta barmu, ya Allah ya Allah, Jalilan da tace min tana so in soya mata wainar fulawa in ta dawo itace a kwance a gabana bata cikin duniyar mu.
Nan na tsuguna a gabansu na musu addu'ar samun rahamar ubangiji, Allah yasa kunje a sa'a baba da Jalila, Allah yasa Annabin rahama yasan da zuwan ku, Allah yasa aljannar ku ta zama bi ghairi hisab ya hada mu a aljannah firdaus gabadaya na fada ina share hawayen da yayi nasarar saukowa tun bayan rasuwar su. Nan Mus'ab ma yayi musu addu'a sannan maza suka shigo suka fitar da makarar mu kuma muka bisu da addu'a ina me kara rungume Maryam dake bacci a jikina.
Kafin magriba kowa ya watse mun dawo daga mu sai halin mu. Ina sallar Isha kuwa na rufe mana gidan da mukulli domin lokaci guda naji wani irin tsoro ya shigeni. Kallon Mus'ab daya fara bacci nayi ina me jin tausayin kanmu. Kaman ba jiya a daidai lokacin nan muke zaune muna hira ba, ashe hirar bankwana mukeyi ban sani ba.
Allah ka bani iko da juriyar kula da yan'uwana na fada ina me lumshe idanuna domin yau ko bacci dayake barawo bai isa ya sace ni ba.Baba da Jalila sun tafi sun barmu 😭
Ko wani irin hali Nadia da Mus'ab zasu tsinci kansu a ciki?
Kome rayuwa ta tanadar wa Nadia?
Duk wadannan tambayoyi ne da ni kaina bansan amsar su ba.
Mu cigaba da zuwa domin kuwa yanzu rayuwar Nadia zata fara.
YOU ARE READING
Rayuwar Nadia
General FictionShin ko me rayuwa ta tanadar wa Nadia da yan uwan ta???