(1).

2 1 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

Khadija Muhammad Shitu.
(1).
“Ranar da Dr Jabir ya tabbatar min Imaan ba zata ƙara wata ɗaya ba a duniya za ta mutu, Na ji a raina komai ya fita da raina na tsani rayuwata na tsani kowa da komai, Raina ya sosu na bar Asibiti ina kuka bugun zuciyata yana fita da raɗaɗin ɓacin rai”

Ko a mafarki ban taɓa kawo ma Raina Imaan mutuwa za ta yi ba. Zuciyata ta dinga ayyana mun Na kashe kaina, Ilhaam ba zata iya jurar ganin Imaan cikin wannan yanayin ba.

Ban san ina zan dosa ba, Na dawo gidan ko sallama ban iya yi ba sai kuka da na shigo mata da shi.

Hankalinta ya tashi sosai ta ruɗe tana tambayata Ilhaam me ya ya faru ki faɗa min kar zuciyata ta buga.

Na durƙushe bisa gwiwoyina ina raira kukan da nake jin raɗaɗinsa har cikin ruhina.

Ta yi juyin duniya na yi magana na kasa sai kukan da nake yi wanda ya tabbatar mata lallai akwai matsala.

Sai itama ta fashe da kukan Sosai, Muka rungumi juna muna sake fashewa da kuka.

Ita ta fara tsayar da nata kukan ta dinga lallashina da daɗaɗan kalamai. Imaan tana da kyakkyawar zuciya da lafazi mai tasiri.

Kalaman Ummah ne suka dakar mini zuciya, Jikina har kyarma yake yi “Da kika Tasa ta a gaba kina kuka dan Ubanki warkar da ita za ki yi ne?” “Ummah kika ce me?”

Jikina har kyarma yake yi na ce, “Ba zan warkar da ita ba amma zan iya musayar rayuwata da tata”
Cikin tsananin mamaki take dubana dan bata zaci zan iya faɗa mata magana haka ba. Imaan ta dafe kai cike da tsoron uƙubar da zata biyo baya.

“Ilhaam ni kike faɗa wa magana haka dan uban ubanku?”

“Eh na faɗa miki ki yi duk abin da kika ga za ki iya yi, Ke Imaan tashi”. Yanda na yi magana ba sai na faɗa ba ɓacin raina a  bayyane yake zuciyata tafasa kawai take.

“Wallahi daga yau ni Khadija Ilhaam ba zan sake bauta a cikin gidan nan ba bare Imaan! Ba zan sake ɗaukar kowane irin cin zarafi ba, Zan iya aikata komai a kan Imaan”.

Ba ita Umman kawai ba hatta Imaan ta girgiza da jin furucina.

Na kama hannunta na miƙar da ita tsaye.

Ban bata damar magana ba na shiga ɗaki na ɗauko mata hijabi na sanya mata. Bata iya ce mini komai bai sai hawayen da suka turu mata a ido.

Na kama hannunta na riƙe gam muryata na rawa na ce, “Umma za mu tafi ba zamu sake dawowa ba har abada kuma ba zan taɓa mantawa da zaluncinki da Azabtarwarki a gare mu ba, zaki yi Nadama a Ƙurarren Lokaci da duk wanda ya lalata mana rayuwa..”

Muka fito ni da Imaan tana kuka sosai.
Ita ba dutse bace dole duk rintsi ta gaza,dan haka bata ce da ni uffan ba. Muka tsayar da Ɗansahu.

Babbar Tasha na ce ya kaimu Cikin Adaidaita babu wanda yay magana daga ni har ita sai ajiyar zuciya da nake saukewa Imaan na kuka sosai.

Lokacin da ya ƙaraso tashar muka sauka sai kuma kallo ya dawo kanmu dan ko sisi babu hannuna.

Muna tsaka da hatsaniya Allah da nashi ikon ya jeho Alhaji Tahir Yusuf Ɗankwangila.

Ya fito cikin danƙareriyar motarsa ya ƙaraso gare mu yana jin ba'asi ya biya kuɗin.

Na sha Jinin jikina ganin sa da na yi amma na dake.
“Ilhaam ya jikin Imaan ɗin ko zamu je na taimaka muku?” Gaba ɗaya a rayuwarmu bama da zaɓin da ya wuce bin sa na ce,
“Mun gode” a hankali cikin sanyin murya. Muka shiga cikin motarsa.

Babu alamun nadama tattare da ni ko fargaba na janyo Imaan muka sauka daga motar dan zuciyata ta bushe.

Madaidaicin gida ne ɗan daidai muka shiga ya nuna mana ko ina. Bamu yarda Zamu zauna ba sai da ya tabbatar mana da babu Sanin Ummah ya kawo nan ɗin.

Alƙawari muka ƙulla na aurenshi, shi kuma zai mallaka mini duk adadin dukiyar da nake buƙata sannan zai bamu damar hutawa har Imaan ta haihu.

Na amince masa kai-tsaye ina jin sanyi a zuciyata. Ko babu komai zan bawa 'yar'uwata lokacina da kulawata irin wacce bamu samu daga iyayenmu ba.

Na sani ba zan taɓa samun matsala akan Masoya ba sai dai matacciyar rayuwa ce bana buri.

Ban sake tada mata kowane zance ba.

09117440993.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now