(8).

0 0 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

(8).
Har safiya ban fito ba iyakata cikin ɗaki tsoro ya gama lulluɓe ni da tunane-tunane. Ina son fitowa kuma ina jin tsoron abin da zan gani.

Ina tsaka da wannan tunanin na ji bugun ƙofa har sai da na razana na ƙarasa cikin ƙasa da murya na tambayi waye muryar direba da na ji ce ta sani buɗewa ina kallon sa.

“Kina lafiya, Ya aka yi baki sanar da mu Yallaɓai na cikin wani hali ba, Da ya illata kansa fa ya kamata ki dinga faɗa mana duk halin da yake ciki” Nayi shiru ina auna maganganunsa da hankali.

Ki girka abincin da za a kai masa Asibiti ya faɗa yana juyawa ya bar ni nan tsaye.
Jiki a sanyaye na shiga Kicin na fara aikin dafa farfesun kaji. Ina ta tunani to shi ina iyayensa amma zuciyata na kwaɓata kar na zaƙe ni miye nawa.

Na gama na sanya a kula Direba ya karɓa a cewarsa zai kai asibitin da yake na ce Allah ya bada lafiya ina tunanin abubuwa da dama.

*
Kwana na Huɗu gidan babu ɗuriyar Maman Afrah ko mijinta na sawa raina haƙuri da tsumayen zuwansu. Mutumin kuma bai dawo ba. A lokacin na fara tunanin ko dai matsalar ƙwaƙwalwa ce da shi sai dai na kan kauda zancen.

Na fara gane lallai babu wanda zaka ce ba zaka iya rayuwa babu shi, Shi kenan rayuwata da Imaan ta zama tarihi sai dai ba zata taɓa mantuwa cikin zuciyata da ƙwaƙwalwata da ruhina ba haka ƙaunarmu.

Amma yanzu babu ita ban fasa komai na rayuwata ba sai dai damuwa Lallai duniya ba tabbs.

Ban samun wata matsala sosai Ɗana yana ɗan wayau da gane ni, Yana murmushi kullum sai na masa addu'a da karatu.

Rayuwa ta ɗan ci gaba babu laifi, Yau kwanakina Ashirin cif a gidan. Ashe mutumin da nake yiwa Aiki Taɓin hankali ne da shi, Lafiya lau yake komai sai dai idan abin ya motsa masa ya bani tausayi sosai, Wajen direba na samu labarin.

Ina kiyaye duk wani abu da zai haɗa mu ina komai tsakani da Allah da iya gaskiyata.

Maman Afrah ta zo sau biyu ta nuna mini abubuwa sosai kuma Alhamdulilah na ƙara gogewa wajen girki. Kullum ina yiwa 'yar'uwata Addu'a Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ta, ta huta da ƙuncin Rayuwa.

Kwanci tashi babu wuya a wajen ubangiji Rayuwa na ta garawa Hankalina ya kwanta bani da wata matala na karɓi albashina dubu hamsin ranan na yi kuka na bawa maman Afrah da mijnta dubu talatin Na yi sayayyar dubu goma ta sutura da ɗana da Alƙur'ani.

Sun ji daɗin girmamawar da na musu don rantsewa na yi sai sun karɓa.

Ɗana ya yi wayau yana rarrafe ya gane ni sosai Mutumin da nake ma Aiki Alhaji Umar farouku yana ɗaukarsa yana matuƙar ƙaunar yaron idan lafiyarsa ƙalau wajensa yake wuni.

Mun ɗan yi sabo da shi Na faɗa masa Mamata ta rasu Abbah kuma ya ɓata daga nan kuma 'yar'uwar tagwaicina ta rasu shi ne na dawo Kaduna. Ya yi Alƙawarin taimakona ni ma ɗin na yi fatan haka.

Ya tamabayen miye burina na ce karatu daga nan bai sake bin ta kan Lamarina ba Na daina ganinsa sam.

Direba ya kawo mani ƙaramar jaka ya ce inji shi. Waya ce a ciki sai ATM ɗinsa da Pin ashe ciwonsa ne ya tashi yana wajen mahaifiyarsa.

Na karɓa cike da farinciki Ina tsaka da murna cikin kwanakin Mahaifiyarsa ta diro gidan na sha Zagika da cin mutunci Ashe ba musulma ba ce Babanshi ne musulmi kuma ya daɗe da rasuwa.

A taƙaice ranar na bar gidan ina kuka da ɗana Allah ya taimake ni na ɗauki wayar da ya bani da atm daga su ko tsinke ban ɗauka ba.

Na wuce gidan Maman Afrah suka amshe ni hannu biyu. Na yi ta godiya hankalin ya ɗan kwanta.
Sai washe gari ne yake faɗa mini maganar da ta kusa zauta ni saboda murna, Farouk ya biya mini Kuɗin makarantar da zan fara Germany tare da 'yar'uwarshi Rufaida A wata makaranta.

Na ji daɗi sosai ina ta musu godiya.
Ranar na shaida Allah na sona da Rahama yana ta chanja mini al'amura zuwa alkhairi.

Saura sati biyu tafiyata Muka samu saɓani da Aunty Fa'iza wanda ya tsaya mini a rai..
09117440993.
K_SHITU MULTIMEDIA.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now