(18).

1 1 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

(18).
Duk da ciwon da nake ji a zuciyata na abubuwa masu yawa na rayuwata amma idan na tuna da Duk yadda mutum ke burin tsara rayuwarsa Ubangiji da nashi ikon Ƙaddara da nata tsarin sai na yi haƙuri.

Na kan zauna a duniyata nay tunanin mene amfanin matacciyar rayuwa da burin ƙyale-ƙyalen duniya da zarar na tuna irin wahalar da muka sha ta dalilin Mahaifin mu, Na daƙile ta dalilin abinda ya aikata, me yasa bai duba goben sa ba da zuri'arsa, Bani da wani Dangi da zan kalla na ji daɗi. Shisa Masana suka tabbatar abin da ka shuka shi zaka girba.

Wacce riba na samu da farin ciki a rayuwata tun da na tashi Mahaifina ya rasu ba a daina aibanta shi ba, Shi yasa ake gujewa Ɗan'adam nadama a ƘUARREN LOKACI ina ace zai dawo duniya ya ga yanda al'amura ke wakana. Bani da wani bango majingini taya matsayina na mace budurwa na yi rayuwa ni kaɗai da aiki ba abu bane mai yiwuwa.

Matsalata Asaad.  na san ina matuƙar son shi amma Abubuwan da ya tsira a kwanakin nan sun sha min kai bana son duk wani abu da zai kai ni ga Da na sani a ƙurarren lokaci.

Dare da rana ina yiwa Iyayena da 'yar'uwata addu'a ubangiji ya ƙaddara mutuwa ta zame musu hutu. Kullum damuwa na danƙare a zuciyata na rasa nutsuwar rayuwata.

Ashe daman haka rayuwa take?
Mahaifinmu bai shuka alkhairi ba, Abin ya dawo mana, Bamu aikata wani mummunan laifi ba amma saboda shi da ya aikata ma 'ya'yan wasu da iyayen wasu abin ya dawo kanmu da 'yar'uwata wanda yay silar rasa rayuwarta, Shi ma ya rasu, Ya tuba a ƘURARREN LOKACI. idan haka za a ci gaba da yin rayuwa ba za a taɓa ci gaba ba har abada!

Abu mafi dacewa duk abinda mutum baya fatan ya same sa kar ya aikata laifin da zai munana rayuwarsa ta gaba.

Daga Lokacin da al'amura suka fara daidaita na sa haƙuri a rayuwata na fahimci dukan duniyar nawa take kowane lokaci ma mutum zai iya koma wa mahaliccin sa. na daina damuwa da wasu abubuwa marasa muhimmanci.

Zuciyata na matuƙar son Asaad da Ƙaunar sa Ta ɓangaren sa kuma ba hakan bane ba tsakani da Allah yake so na ba. Na yi duba na hankali da irin matsayinsu da darajar su taya zai iya aure na abin da yafi mutuntaka mu rabu da juna na fuskanci rayuwarmu da Ɗana.
*
Ban sha wahala ba rabuwar mu da Asaad ta dalilin Alhaji farouku da ya nemi aure na. Na yi kuka na gode wa Allah na so na ƙi, Amma na ga ban yi ma ubangiji butulci ba duniya ba jindaɗi aka zo yi ba na amince da auren sa. Alƙalinmu shi ne ya zama wakilina ya bada aure na. Muka tare a Abuja babu wani shagali ban tsawalla ba.

Kuka muka yi sosai nida Imraan bayan ɗaura aure na. Ina tausar zuciyata sosai Ya zan yi rayuwa da mutum mai irin lalurarsa ba kowane lokaci yake hayyacin sa ba.

Rayuwa ta miƙa muna zaman lafiya da mahaifiyarsa duk da ba musulma bace, ban taɓa samun wata matsala daga gare su ba.

Haka imraan ɗina babu wanda yake takura sa yana karatu.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now