(15).

0 0 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

(15).
Ko kusa ban yi tunanin samu  wata matsala ba ta ɓangaren Aikina har wata guda da na fara amsar Albashi. Sai da wani case ya ɓullo na wata matashiyar budurwa da aka yi wa fyaɗe, Mahaifiyarta da ita kanta suna kuka cikin ofishina suna roƙona na tsaya musu basu da wani wanda zai tsaya musu an fi ƙarfin su babban mutum ne ya illata musu rayuwa ƙarfin su bai kai ƙalubalantar sa ba. Na tausaya musu sosai har na ji zan iya tsaya musu da dukkan ƙarfina wajen ƙwato musu haƙƙin su.

A cikin wannan Case ɗin na fuskanci ƙalubale sosai na nuna jarumta da taurin zuciya har na cin-ma Nasara. Al'amarin da ya zo mini da sauƙi shi ne 'Yar mutumin da ta bani haɗin kai ta bankaɗa sirrin mahaifinta da wasu hujjoji ta tabbatar mini ba karo na farko kenan ba ya aikata laifi irin wannan.

Shari'a ta yi zafi sosai na ƙarfafa kaina na ƙalubalance su wanda kai tsaye Muka yi zaman shari'a tare da Lauyan da ke kare Alhaji Yusuf Ma'aji babban lauya ne mai lasisi bai taɓa faɗuwa a shari'a ba.

Mutane na matuƙar yaba jarumtata da tsaiwa kan gaskiya da na yi duba da yanda Iyayen Yarinyar da nake Nemar ma Haƙƙin ta Bilkisu basu da ƙarfi.

Duk irin arziƙin Alhaji Yusuf ɗin na gaban misali sai gashi na yi nasara kan su a shari'a Alƙali ya yanke masa hukuncin zaman Gidan kaso na shekaru masu tsayi sosai. Da kuma tara mai yawa da ɗaukar nauyin Ita Yarinyar.

Ƙarara za a iya fahimtar fusatar makusantansa da lauyan sa. Na yi farin ciki matuƙa da iyayen yarinyar suka dinga jera mini addu'o'in fatan sa'ar rayuwa da nasara har sai da na yi hawaye.

Na yi mamakin yanda shari'ar ta zagaye Gari da gidajen talabijin da na Rediyo ta ko ina ana jinjina wa ƙwazon Matashiyar lauyar.

Ƙalubale na farko da na fara fuskanta; Cin mutuncina da bibiyar rayuwata da Mutane biyu ke yi Matar Alhaji Ma'ajin da Ɗansa suna ta bibiyata da goranta mini a kan mahaifina na rasa inda zan tsoma kaina na ji daɗi.

*
Ina tsaka da bibiyar su Ummah na ci karo da abin da ya kusa dakatar mini da numfashi.
Dattijo mai matuƙar kamanni da Imraan ɗina ta fuskar gashin jikinsu da yanayin maganansu, sai dai ba kowa ne zai iya gane hakan ba sai mai zurfin tunani da kaifin ƙwaƙwalwa Domin dukkanin zanen fuskarsa nawa ne.

Ta ina zan fara bayyana wa Duniya ɗana ba ta tsaftatacciyar Hanya Aka same sa ba, Sunan sa Imraan Aliyu Aliyu. Na so na haƙura saboda kar na tuno da wasu abubuwa da suka shuɗe marasa daɗi a rayuwarmu sai kuma na dinga jin ban yiwa Imaan Adalci ba.

Me sunan abin da na yi kenan. Idan ta tabbata lallai Mahaifin Mutum mai karamci da girma a idona ne ya lalata mana rayuwa?

Abin yayi mini girma a ƙwaƙwalwata ta ina zan fara Ina tsananin ganin girman Dacta Jabir a idona Ya yi mana halacci a rayuwa bai duba rashin gatan mu ba ya cutar da mu ya tausaya mana yay tsaye kan al'amuran rayuwarmu ya bamu kariya ya ciyar da mu ya ƙarfafa mu, ya nuna mana muma mutane ne kamar kowa har abada ba zan mance da Karamcinsa ba ina matuƙar jin kunyar sa.

Shin nayi masa sakayyar mutuntaka idan har na tona wa mahaifinsa asiri a idon duniya, bana fata wani ya kunyata a rayuwata sai a kan wanda ya wulaƙanta mana rayuwa ya jefa 'yar'uwata cikin mummunan yanayi a Ƙurarren lokaci da aka san bamu da gata sai mahaliccin mu an cuta mana
Yanzu abin da yake mini yawo ya hana ma idanuna runtsawa yake mini barazana a kwanyata shi ne ta ina zan fara, Shin shi Dacta Jabir ɗin yana da sani akan al’amarin idan bai sani ba fa, kenan ni ce zan jefa shi cikin ƙunci?

Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un kawai nake maimaitawa, na rasa wa zan tunkara na faɗa wa Matsalata.

Cikin watanni huɗu da nayi da Fara aiki na ji zan iya ci gaba da rayuwa cikin 'yanci da farin ciki don a gani na bani da wani dalili na ƙuntata duniya ta komai muƙaddari ne daga Ubangiji.

Amma yanzu na yi ma kaina adalci idan na binne wannan al'amarin a zuciyata ni ɗaya, Ban manta ba kuma ba zan mance ba har numfashina ya tsaya zuciyata ta daina bugawa Irin wahalar da Imaan ta sha Bana fata ko maƙiyina ya ɗanɗana ta.

Gaba ɗayan rayuwata na tashi da burin ganin bayan ko waye ya wulaƙanta mu haka, Har 'yar'uwata ta rasu da ƙaddarar samun Ɗa Namiji.

Tun da na mallaki hankalin kaina ƙwaƙwalwata ta kan banbance abubuwa masu kyau da akasin su. Na sani dai Ummah ba zata taɓa nuna mana wannan zallar ƙiyayya da tsana hakan nan ba ina yi mata uzuri ba don ta chanchanta ba, Sai dai ni a iya sani na ba mu taɓa aikata mata wani abu ba daidai ba wanda har muka chancanci wannan ƙin.

*
Na ɗauki hutun sati biyu wajen aiki saboda na nutsu na samu hutun ƙwaƙwalwa abubuwa sun cunkushe mini.

09117440993.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now