(4).

1 1 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

(4).
Irin yanda zuciyata da ƙwaƙwalwata suka taɓu abin ya matuƙar girgiza likitocin.

Satina guda a asibitin bana cin komai bana magana sam babu abin da zuciyata ke juya mini
Komaina ya tsaya chak.

*
Yau tun da na tashi zuciyata ke juya min abubuwa da dama, Na miƙe zaune daidai lokacin aka turo ƙofa.

“Sannu Ilhaam” Dacta jabir ya ce yana zama.
Na gyaɗa kaina ba tare da na ce komai ba.

Cikin kulawa yake mini magana.
“Dan Allah ki yi haƙuri komai ya wuce an sallace ta, mun binne ta maƙabarta addu'a ya kamata ki dinga mata”
“Na gode Allah ya biya ka da Aljannah, Allah ya tsaya maka a rayuwa” Na faɗa cikin sanyin murya.

Wata Nurse ce ta turo ƙofar ta shigo hannunta riƙe da yaron na karɓe shi ina ƙare masa kallo.

Wata irin ƙaunar jaririn ce ke ratsa ni sosai, Ba abin a ya raba shi da Imaan tamkar kuma ni na haife shi, Idanuwanmu iri ɗaya sak.

Na sumbaci goshin Yaron fuskata cike da Fara'a na Ambaci Sunan Imraan a hankali. Sunan da imaan ke matuƙar so.

Na juya ga Dr Jabir cikin Girmamawa na jera masa godiya da addu'a, ya cire mini cannular na saka hijabi na rungume yaron na ce zan tafi.

Ba irin magiyar da be mini ba amma sam ban tsaya ba na bashi haƙuri akan garin zan bari. Daga nan na fito yay mini kwatancen Maƙabartar da suka binne Imaan tare da tabbatar mini yaron yana lafiya baya ɗauke da wata Cuta.

Na fito da ɗana Imraan A hannu har wajen asibitin ina tunanin inda zan dosa.
Ko a mafarki ban taɓa zaton rayuwa zata juya mana irin haka ba, Duk da Azabar da muka sha ta rayuwa ban sa ran abubuwa zasu faru haka ba, A ko dayaushe Ina mana fatan alkhairi.

Da ace wani ne zai faɗa mini ana rayuwa haka kuma al'amura na chanjawa cikin ƙanƙanin lokaci ba zan yarda ba sai gashi hakan ta faru a kaina da 'yar'uwata.

Ban san Inda zan dosa ba, Ba mu da kowa dama Mune 'yan'uwan junanmu.

Cikin sauri sosai tsaya gabana ya ɗaura kuɗin hannunsa a Jikin jaririn ya juya ya koma.

Na tsaya ina kallon bandir ɗin 'yan dubu-dubun, Wani Sanyi na ji a raina cikin sanyin jiki na ɗauka ina riƙewa a hannuna na ci gaba da takawa har bakin titi.

Na shiga adaidaita zuwa Tasha.
Na yi sa'a saur mutum ɗaya motarKaduna ta tashi na biya kuɗin mota na siyi abin da zamu ci na shiga.

Tun da muka fara tafiya nake addu'a cikin raina, Wace irin rayuwa kuma zan ci gaba, A da komai ni da 'Yar'uwar tagwaicina muke yanzu kuma Ƙaddara ta sauya al'amura ni ce da ɗana zan ci gaba da fuskantar ƙalubalen rayuwa.

Matar da ke Kusa dani ta ce, “Baiwar Allah naga yaron”Na miƙa mata shi Ta dinga santi Turbakallah.

“Sunana Fa'iza ga d’iyata kuma Afrah”.

“Khadija Ilhaam, sai shi kuma Imraan”

Na bata amsa da ganin matar zata yi kirki na ce, “Dan Allah ke 'yar Kaduna ce?”
“Kwarai kuwa Chan nake aure babana ma d’an chan ne me ya faru ko ke bak’uwa ce??”
Na gyaɗa mata kai daga nan muka yi shiru babu wanda ya sake cewa komai.

Mun yi tafiya sosai mun yi sallah har na ƙosa da zaman motar, dan ma imraan ɗin ba mai rigima ba ne, bawan Allah yaron da ya ɗan yi kuka sai na ba shi ruwa ya yi barci ya tashi har Allah ya isar da mu Kaduna birnin Shehu.

Fasinjoji suka fara sauka na bi layi ina rirriga Imraan da ke kuka na yi hanyar da naga ana ta bi jikina a sanyaye dan ban san inda na dosa ba.

Ta taɓo ni na juya ta ce, “Idan baki da masauki mu je gidana” Nay saurin jijjiga mata kai ina sauƙe ɓoyayyar ajiyan zuciya. Na sani Allah ne ya dube ni da na sha wahala.

Muka hau adaidaita zuwa gidanta tana jana da hira ina amsa mata kaɗan-kaɗan. Muka sauka wata unguwa mara hayaniya ta masu rufin asiri ta sallame shi muka doshi wani madaidaicin gida mai ƙaramin gate da ƙofa. Ta sanya mukulli ta buɗe ƙofar muka shiga ina addu'a cikin raina.

Gidan na da kyau sosai a gyare tsaf muka shiga da yin sallama. Ta buɗe ƙofar Falo muka shiga tare ta zaunar da ni bisa kujera ta haye sama ta bar ni da 'yarta na dinga rirriga Imraan.

Bata jima ba ta dawo hannunta riƙe da Faranti da kuloli biyu da Plate ta ajiye mun da ruwan roba ta ce na samu na kimtsa na bawa yarona ya sha shi ma.

Sai na ce mata ina son yin sallah, ta buɗe mini ɗakin hanyar kicin ɗinta ta aje min abincin ta juya ta fice.
Sosai ya bani tausayi na san yayi haƙuri dan haka na kurɓi ruwa kawai na saka masa nono a baki a runtsa ido, Ya fara ja cikin jin yunwa duk da ba ruwa amma bai saki ba. Na ji ƙwallah ta cika idona ina jin zafi sosai amma na daure zan iya jurewa saboda Imraan ɗina. Cikin ikon ubangiji ruwa ya fara zuwa, Na yi mamaki sosai, sai dai bani da wani sani ya sa na yi shiru na san wani taimako ne na ubangiji. Na dinga cin abinci yana shan nono har ya ƙoshi sannan na bashi ruwa. Na kwantar dashi saman sallaya.

Na yi Alwallah da sallah. Na zauna ina addu'o'i sosai da tausayin kaina da ɗana. A haka ta shigo ta same ni muka sake gaisawa na dinga mata godiya ta ce, “Hala dai baki san kowa a garin nan ba?” Na gyaɗa mata kai na ce, “Yar'uwar tagwaicina ce ta rasu, Inda nake kuma akwai matsala iyayenmu sun daɗe da rasuwa shi sa na taho nan ɗin”

“Allah ya gafarta musu. To amma so kike ki zauna nan dindindin?”
“To gaskiya sai kin tashi tsaye kin nemi na kanki ko ki nemi aiki”
“Dan Allah ki taimake ni idan kin ji wasu na buƙatar mai aiki zan iya in sha Allah” Ta amsa mini sannan ta fice daga ɗakin.

Da dare na ga karamci ƙwarai ta kawo mini kunun tsamiya da Shinkafa miyar taushe da ta ji tsoka zaƙo-zaƙo sai Pampas. Na yi godiya Na ci na ƙoshi ɗana ma haka,  ina gode muka kwanta barci.

K_shitu Multimedia.
09117440993.

            (Ku yi haƙuri masu ƙorafi, haka salon labarin ya xo🫣)

*WaTtPaD@KSHITU*
Vote, Comment nd Follow Please..

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now