(5).

1 1 0
                                    

*ƘURARREN LOKACI*

(5).
Idan ubangiji ya nufa sai abubuwa su yi ta faruwa tamkar almara. Bayan na cire rai da sake jin daɗi ko kwanciyar hankali Allah ya chanja mini al'amarin.

Tabbas har in koma ga mahaliccina ba zan mance da halaccin Maman Afrah da Mijinta ba.

Ni ce cikin inuwa zaune ba tare da Imaan ba. Hawaye suka wanke mini fuska na kasa riƙe kukana na dinga raira shi a hankali ina shessheka.

Abubuwa masu muni waɗannan da suka shuɗe cikin rayuwarmu da ƙaddarorin da suka kutso kai cikin Ƙurarren Lokaci suka dinga dawo mini cikin ƙwaƙwalwata tamkar a lokacin ne komai ke faruwa..

*
Aliyu Aliyu Shi ne sunan Mahaifinmu wanda ya haife mu. Kaf Unguwar da muka zauna babu wanda bai san Mahaifinmu ba Gogagge ne a harkar Caca ba shi da wata sana'a da ta wuce ta, Mahaifiyarmu Khadija ta rasu bayan ta haife mu 'yan tagwaye da mu. Abbahnmu yana tsananin Ƙaunar Mahaifiyarmu wannan ne dalilin da ya sanya bayan rasuwarta ya mayar ma tagwayen da ta Haifa masa sunanta wanda mutane suka dinga mamaki. Khadija Imaan, Khadija Ilhaam su ne Yaran da aka haifa masa.

Ba za a ce Zuciyarshi ta mutu murus ba domin bai ragi 'ya'yansa da komai ba, bugu da ƙari Allah ya hore masa ilimin addini matuƙa; Sai dai talauci ne ya sauya masa halaye, Ƙwaro ne a harkar saide-saiden Miyagun ƙwayoyi da ƙananun laifuka.

Wannan ita ce sana'arsa da kowa ya masa farin sani da ita. Yana kuma shan wahala matuƙa wajen jami'an tsaro, Da yake abokan harƙallansa manya ne idan aka kama shi baya daɗewa.

Mu dai tun da muka taso da Abbahnmu mun san Mahaifiyarmu ta rasu sai Ƙanwarshi Hindatu wacce Muke kira da Ummah.

Kaf layinmu ba uban da ya isa taka mu, Muna makaranta mai tsada islamiya ma haka. Bakin gwargwado muna shanawa domin Mahaifinmu na tsananin sonmu.
Khadija Imaan Tana da kyau sosai dangin Mamarmu ta ɗauko 'yan Sumaila.

Fulani ne masu kyau da gashi, Sai dai Abbahnmu sam bai taɓa yarda mu je ba ko su su gana da mu hakan ya sa suka haƙura da mu.

Imaan tana da sanyin hali da haƙuri sosai, Bata da matsala Tana da kyawawan halaye masu siye zuciya, Kalamanta tamkar zinare Ubangiji ya bata baiwar sarafa harshe tana da lafazi mai tasiri matuƙa. Burin Rayuwarmu Abbah, Ilhaam, Imaan.

Ilhaam Tana da sanyi da zafi bana ɗaukar wulaƙancin da Imaan xa ta ɗauka, Ina da kyawawan halaye Sai dai Zuciyata bata jurar cin mutuncin Imaan da Abbah.

Wata irin ƙauna muke wa juna da bamu san iyakarta ba, Allah ne ya dasa mana son junanmu, Burin Imaan a rayuwa Ilhaam, Burina A rayuwa komai Imaan duk da ƙarancin shekarunmu a lokacin bama jin daɗin ɗabi'un Abbah.

Zubinmu ɗaya kyawu ma haka sai daa Imaan ta fi ni Fari sosai dan shi ne ma abin da ya banbanta mu. Muna da farin jini kamar hauka saboda kyawu da kuma yanayinmu.

Sai da kowace cikinmu tayi hankali sannan muka fara fahimtar abubuwa da dama, Mun sani A duk duniya babu wani wanda yake tsananin sonmu da ƙaunarmu tsakani da Allah irin soyayyar nan mai narkar da zuciya irin Abbahnmu, Baya iya ɓoye sonmu gaban kowa.

Bashi da kyawun hali Amma yana da shi a wajenmu, Duk irin yanda yake bamu kulawa da lokacinsa duk da baya zama tare da mu ko yaushe amma bamu isa fahimtar komai na al'amuransa ba, komai nasa a sirrance yake gudanarwa.

Daga sanda muka fara fahimtar Lallai Ummah fuska biyu ce da ita Ƙaunar da muke yi mata ta ragu soaai.

Bamu gasgata hakan ba sai da rayuwa ta ci gaba, Muka samu wayewa da kaifin ƙwaƙwalwa.

Ta kowane ɓangare bama da wata matsala sai wadda baa rasawa, duk wani mai son kawo mana cikas to ya san Abbahnmu ya dame shi da tashanci ya shanye shi sa muke samun sauƙin mutanen banza.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now