(2).

2 1 0
                                    

FREE BOOK.

(2).
Ban sani ba, a rayuwarmu sa'a ce bama da ita ba ko kuma Ƙaddarar rayuwarmu ce tazo a haka.

Mun ci gaba da rayuwa cikin gidan Alhaji Tahir. Tun da naga hankalinmu ya kwanta babu wata mtsala na ɗan kauda maganar Dacta Jabir a raina tunanina ya ta'allaƙa ga ciwonta. Ban taɓa fita ko ƙofar gida ba haka Imaan har haske ta yi sosai mai ɗaukar hankali da 'yar ƙiba ta samun kwanciyar hankali, Burina bai wuce ta haihu lafiya ba.

Ranar wata Asabar da safe na shirya cikin doguwar riga cikin siyayyar da Alhaji yay mana, Na ce da ita ta kula zan shiga gari na dawo.

Na fito fuskata lulluɓe da niƙabi. Na nufi Asibiti don ganawa da Dr Jabir domin ko da yaushe zuciyata cike take da matsananciyar fargaba da ruɗu.

Mun tattauna sosai akan matsalar Imaan na fahimci inda ya dosa. Sai dai bayaninsa na ƙarshe ne yay matuƙar ɗaga mun hankali.

“Ilhaam so nake ki fahimta Cutar da take ɗauke da ita tana da hatsari ga ciki a jikinta, Baku fara neman magani da wuri ba bata samu kyakkyawar kulawa ba, damuwa ta yi mata yawa sosai jininta ya hau fiye da zato Ubangiji ne ya ƙaddara ba ku da rabon wahala”

“Haba Dr Taya kai ko da yaushe baka faɗin Alkhairi, Shi kenan idan ƙaddara ta sami mutum yana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki a dinga saka masa mutuwa. Babu komai”

Na miƙe cikin ɓacin rai na bar ofis ɗinsa.

Babu inda zan iya zuwa dan ko ƙawa bama da ita daga ni sai 'yar'uwata muke rayuwa.

Na shigo gidan na tarar da ita zaune ta yi tagumi tayi zurfi sosai cikin tunani har na zauna kusa da ita bata motsa ba.

Ban san sa'adda hawaye suka wanke mini fuska ba, Ina tsananin tausayin imaan fiye da zato ko tsammani ƙaunarta a raina da zuciyata ba zata ƙayyadu ba Allah ne ya dasa ta.

Na kama hannunta a hankali cike da matsanancin tausayinta da ke ratsani.

“Ki yi haƙuri, Ki yi haƙuri Imaan! bani da magani sai Allah shi zamu gayawa kukanmu ban san yaya zan yi da raina ba ko da yaushe a rayuwa ke ce fatana ina son ki samu waraka, ina son farin cikinki fiye da nawa bana son kina jefa kanki damuwa, Ki jure don Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe kin ji ko”

Ta share mini hawayen fuskata, Ta ƙawata fuskarta da murmushi mai kyau wanda har duniya ta naɗe ba zan manta da shi ba.

“Ilhaam ina sonki tsakanina da Allah. Zaki yarda da ni? Ban taɓa damuwa da halin da nake ciki kuma ba zan taɓa ba wannan ita ce Jarabtarmu. Ke ce mafarkin rayuwata da komai ina kuka da ne damuwa akan halin da zaki shiga bayan ba ni. Duk yadda ubangiji ya tsara mana rayuwa mu yi haƙurin akwai riba a gaba. Jikina yana bani ba zan rayu ba, Idan har Allah yayi ikonsa na haifi abin da yake cikina na bar miki duniya da lahira Allah ya tayaki riƙo, Kar ƙauna ta rufe idanunki ki kasa bashi tarbiyya Ke ce mahaihiyarsa Ilhaam”

Kuka sosai ya ci ƙarfinta ta dinga shi kamar zata shiɗe tana tari. Zuciyata na mun raɗaɗi sosai na kasa tsayar da nawa kukan.

*
Duk da Zuciyata bata aminta da Alhaji Tahir ba amma ina kyautata masa zato.

Cikin barcin da ya fige ni nake jin ana yamutsa mini kaya amma tsabar nauyin barci ko motsi ban yi ba sai da na ji an kamar an ɗauki sannan na fara mutsu-mutsu. Buɗe idon da zan yi dishi-dishi na ga abin da ya harba mini zuciyata da ƙarfin gaske.

Ya kulle ɗaki da mukulli ya jefa aljihu sannan ya dire ni saman gado.

Na buɗe idanuwana tangaram ƙirjina na duka.
Cikin wani irin ɓacin rai da ɗacin zuciya na ce, “Alhaji miye haka?”

Ya ƙyalƙyale da dariya.
“idan baki gane ba, Ina son fanshe wahalar da na muku, Idan baki bani haɗin kai ba wallahi saina kashe ki kuma na kashe banza”

Ya zaro bindiga ya saito ni da ita cikin tsantsar mugunta.

#Khadija Muhammad Shitu.

#09117440993.
#Free book.

KURARREN LOKACIWhere stories live. Discover now