SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_13FULANI MAMI POV
Aisha ce tsaye sanye da bakar silk riga doguwa har ƙasa hannun damar ta mopping stick ce da bucket cike da ruwa yayin take ta kai kawo wajan ganin ta goge ɗakin da kyau.
"Huhhh na gode Allah, na kawo karshen aikin nan, Fulani Mami ma da rikici bata san bayi su shigo mata ɗakin ɗa ala dole nice zan goge, "To dai na gama" Aisha ta faɗa a daidai lokacin da take mika wa Iya mopper tana cewa Iya ungo bari na kulle sashin, dogarai dake a kofar sashin Yarima suka kar ɓi key tana musu kashedin kul kar su kuskura suba ma wani makullin ɗakin Yariman.
Kai tsaye sashin ta ta nufa ta na cewa,"Yanzu kam wanka zan yi, na gaji da yawa babu wani sauran aiki"
"In ji wa ya faɗa miki, ai kizo maza maza mu jera warmers a ɗakin cikin abinci inji Mami" cewar Othman yana mata dariyar ƙeta a guje ta biyo shi tana cewa,"Zo nan na kama ka, zo nan" suna ta kyalkyatan dariya, Sun saba hakan ita da kanin nata musamman ma da yanzu yake makaranta a ƙasar waje cen wajan wani abokin Abba ya haɗa su da ƴaƴan sa suna secondary school ya dawo biki ne shima kuma da anyi biki zasu koma In Sha Allah. Suna tsaka da tsokanan juna dai dai lokacin da motocin suka je ɗauko Abbu suka kunno kai cikin masarautar dutse, Othman ya daga tsalle yana tafi ya ce,"Yaya Yarima!!!!!!!
"Sha sha sha ka bari sai ka ga ya fito tukunna, don bana da tabbacin wannan mai ilimin taurarin zai bi shawarar Abbu, nafi zaton tunanin kwanyar sa zai bi wato sai ya cimma mafarkin sa kafin ya.............Ta faɗa tana juya baya hannayen ta sun akan kirjin ta ta nannaɗe su tana cigaba da magana kai tsaye, shirun da tayi ya yayi daidai da jiyo sautin muryar kanin nata jin dariyar su shi da Othman hakan ya tabbatar mata da cewa YARIMA OMAR ya dawo ƙasar sa, cike da zumuɗi ta waiga fuskar ta ɗauke da murmushi hannayen ta na kan bakin ta ta ce,"Look who's here"
"Yaya Aisha" Yarima ya faɗa yana karasowa in da take, Ya ce,"gani na taho, wannan karan ba zan tafi ba har sai na kai ki ɗakin mijinki kamar yadda nake yawan faɗa miki a waya"
Aisha ta harare shi playfully cike da tsokana ta ce,"Kafin nan give your sist a hug" suka rungume juna tana kara mishi sannu da isowa yayin da ita da Othman suka gaishe da Mai martaba da Galadiman Dutse da kuma sauran Hakiman da ke biye da su zuwa Fada.
FULANI HAƊEJIA
3:30pm
Kwance take saman gadon sarauta dake kunshe cikin ɗakin ta, bacci take yi duk da daddaɗar iskar da yake shigowa ta kananun tagar dake jikin ko wani bangon ɗakin kursurwa huɗu, amma kallo ɗaya za kayi mata ka hango zufa kwance a fuskar ta wanda yayi mata dabaibayi da ɗaurin goro tuni ta gaza fahimtar cewa mafarki ne ta ke yi ba da gaske bane yayin da take ta yamutsa fuska kamar wacce a ke ma ukuba mai tsanani.
Jakadiyya zaune gefe ɗaya na daddumar dake shimfiɗe a ƙasan filin ɗakin gaban ta tarun kayan marmari ne cikin babban kwando, yayin da take ta jera su a ma'ajiyar su, bata ji motsin komai ba illa ihu da kwarmaton da F_ Haɗejia take ba kakkautawa, faɗi take ,"Ah ah, ah ,ah ,ah ah nace ba shi bane, Ba shi bane, na ce muku bai dawo ba, Ba shi bane fah......Daga karshe ne ta saki tsawa ta ce,"Na ce mukh ba shi bane fa" a daidai lokacin ta farka tana muzurai kallon ceiling ɗin ɗakin ta shiga yi tana mamakin irin wannan mafarki da baya da ma'ana awajan ta sai dai ma ya tayar mata da hankali.
Jakadiya ta cigaba da abin da take, daga bisani ta ce,"Mafarkin ki ma gaskiya ne domin kuwa YARIMA OMAR ya dawo ɗazu ɗazun nan Ranki shi daɗe" Jakadiyyah ta faɗa tana yi wa Sarauniyar tata kallon gefe cike da son tayi dariyar mugunta don ita a ƴan kwana kinann Uwargijiyar tata gaba ɗaya kamar ta fara haɗuwa da
"Ni Do Allah bani son maganar tashaa, Jakadiya wau yaushe na fara wasa dake ne haka"
"Tun lokacin da kika fara sani na binne miki asiri" Jakadiya tayi maganar a zuciya a fili kuma ta ce,"Ranki shi daɗe sauko a hankali man ta da zancen ya kamata kizo kisha kayan marmari ya wanke miki zuciya ko za tayi fari"

YOU ARE READING
SOFIA ✔
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...