🌷Shafi na 58🌷

77 7 3
                                    

Bayan Watanni Biyu

A hankali Anty Hafsah ta bude kofar dakin saboda bata son ta tashi Alamin ya dan samu bacci kafin ta fita. Tana shiga ta tarar da shi a kishingi de. Kokarin mikewa zaune yayi, tayi sauri cewa "Kayi zaman ka mana, ba sai ka tashi ba. Me kake so a miko maka."

Ruwan da ke cikin glass cup ya nuna mata sannan ya koma ya kwanta. Karasowa inda yake tayi ta dauki ruwan ta zuba acikin glass cup ta mika masa.

Karba yayi ya kai bakinsa da yake a bushe, ya dan sha a hankali sannan ya mika mata kofin.
Ragowar ruwan da ke kofin tace "Shikenan ya ishe ka?"

"Eh," ya bata amsa da kyar.

Ajiye kofin Anty Hafsa  tayi sannan ta koma ta zauna. "Tun safe baka ci komai ba, na hada maka tea?"

"No, I am okay. Bana jin yunwa Yaya."

Bata rai Anty Hafsah tayi tace "Ni na rasa wani irin taurin kai ne wannan, baka da lafiya gashi baka son cin abinci, ta yaya zaka warke?"

Murmushi Alamin yayi ya juya ya kalli Anty Hafsa, a hankali yace "Baki na ne baya min dadi and bana jin yunwa kwatakwata."

"Zan yiwa likita magana, ko da akwai abunda zasu baka wanda zai washe maka bakin. Kaga na sa a dafa maka favorite food dinka, nan ba da jimawa ba Basma zata kawo maka abincin."

"Yauwa, har na manta Hajiya Kaka za ta zo duba ka."
Mikewa zaune Alamin yayi "Meyasa kuka fada mata ina asibiti Yaya? Kun san ba cikakke lafiya gare ta ba yanzu sai jininta ya hau."

Numfasa Anty Hafsah tayi "To ya zamu yi Alamin, wata biyu fa kenan kana jinya, kaga ai dole ta sani."

"Amma Yaya ai da kun ce mata na tafi aiki wata kasar, ni wallahi bana son abun da zai daga mata hankali."

"Baza ta yarda ba, bayan ta saba kusan kullum sai kunyi waya gashi wayarka bata nan likita ya hana ka danna waya. Dole zata gane mana."

Komawa Alamin yayi ya kwanta yace "Dan kun bani wayata ai da duk haka bai faru ba."

"Lallai a baka wayar ka cigaba da Kallon hoton Jasmine Bp dinka yana kara sama ko, to an ki a baka wayar."

Kasa Alamin ya yi ta idanunsa ya dan jima bai ce komai ba, sannan yace "Yaushe Hajiya Kaka zata zo? I need to change idan ta ganni a haka baza ta ji dadi ba."

Murmushi Anty Hafsa tayi "Ko kai fa, idan ka chanja ma sai ka fi jin dadin jikinka. Kaga ban san lokacin Hajiya Kaka zata zo ba, maybe ka ganta tare da Basma, ko yanzu zaka iya ganinta."

Anty Hafsah bata gama rufe bakinta ba aka kwankwasa kofar dakin, Alamin ta kalla sannan tace "Shigo,"

Basma ce ta shigo tare da Driver a bayanta yana dauke da Basket din Abinci. Anty Hafsah ta fara gaisarwa sannan ta juya ta gaida Alamin. Bayan sun gaisa da driver ajiye abincin yayi ya fita ya jira Basma awaje.

Flask din abincin Anty Hafsah ta fara fitowa da su tana dorawa akan dan center table din da ke dakin, tayata Basma tayi suka jere abincin.

"Wanne zaka ci?" Anty Hafsah ta tambaye shi.

Mikewa Alamin yayi ya zauna yana kallon flasks din abincin.

"We have Dambu with fish sauce ko kuma Tuwon shinkafa da miyar taushe," Anty Hafsah ta fada tana murmushi dan tasan yadda yake son abincin gargajiya.

Murmushi Alamin yayi yace "Tuwo,"
Kalamar Tuwon da ya furta ce ta tuna masa da lokacin da Jasmine ta yi masa girki a karo na farko, tuwo as an apology gift. Murmushi fuskarsa kara fadada yayi da tuno yadda ta zauna ta kafe shi da idanu yana cin abincin har ya gama ci.

Jasmine Baturiyya ceМесто, где живут истории. Откройте их для себя