🌷Shafi na 24🌷

2.9K 304 54
                                    

Bayan sun shiga cikin jirgin sun zauna Jasmine ta kalli Alamin tace "How did you do all of this a kankanin lokaci?"

"I fulled a few strings." Ya bata amsa.
Girgiza kawai Jasmine tayi tace "I'm impressed, and my password?"

"Gashi nan." Ya mika mata Passport dinta.

Mamaki ne ya bayyana akan fuskarta "Taya ka sami passport dina?"

"I'm sorry for invading your privacy, I wanted to surprise you shiyasa na dauka." Alamin ya bata hakuri.

Harararsa tayi tace "Apology not accepted."

"Amma ai..." Alamin ya fara kokarin kare kansa amma Jasmine taki barinsa.

"Amma meh? Abunda kayi is called trespassing M, idan akwai abunda bana so ka gani a cikin kayana kuma fa." Ta balbale shi da masifa " Ni dakina na da zan koma bangaren su Basma." Ta juya masa baya tana turo baki.

"Are we seriously fighting over this." Alamin ya dora hannunsa akan goshinsa yana kallonta a kasale.

"Yes" Ta bashi amsa.

"Okay, I am sorry bazan kara miki bincike ba daga yau, shikenan?"

"

Fine, na hakura amma Ina zamu?" Ta tambaye shi.

"Idan munje zaki gani." Ya bata amsa a takaice.

"Okay, how many hours ne Flight dinnan?"

"5 hours 15 minutes." Ya bata amsa.
Shiru tayi bata kara cewa komai ba har bacci yayi awon gaba da ita. Alamin da ke aiki a laptop dinsa ya dago ya kalleta ganin tayi bacci yasa shi rufe system din tasa ya mike ya nufi inda take. A hankali ya dauketa ta ya nufi wani sashe na cikin jirgin da ita a hannusa da dabara ya bude kofar sashen ya shiga ya kwantar da ita akan gado, ya lullubeta sannan ya sumbaci goshinta ya fita daga dakin.
Sai bayan awa uku 3 da rabi Jasmine ta farka daga bacci, a hankali ta mike zaune tana karewa dakin da take ciki kallo. Murmushi ne ya ziyarci fuskarta da ta gano Alamin ne ya kawota dakin. Fitowa tayi daga dakin ta nufi inda Alamin yake, tana isa ta tarar da shi a zaune da takardu masu yawa a gabansa ga system a kunne yana ta aiki. Ƙare masa kallo tayi ta lura ko rintsawa bayi ba.

"Baka yi Bacci ba?" Ta tambayesa muryata a ƙasa ƙasa.

Dagowa Alamin yayi ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yace "Kin ta shi kenan."

"Baka ka yi bacci ba?" Ta sake maimaita masa tambayar.

"I have so much work to do, ga shi lokacin yana so ya kure." Ya bata amsa tare da maida idanunsa kan takardun da ke gabansa.

"Amma ya kamata ka ringa samun lokaci kana hutawa, wanne irin aiki ne haka da zai hana ka bacci? Mu gani maybe I can be of help." Ta mika hannunta zata dauki takardun gabansa.

Da sauri Alamin ya dauke takardun yace "Relax, wannan aikin nawa ne ki bari na kusa kammalawa."

Girgiza kai Jasmine tayi tasa hannu tayi sauri ta dauke system dinsa daga gabansa sannan tace "Ka san ko illar rashin bacci ga lafiya, shiyasa kake yawan yin ciwon kai, wai ma ina PA din ka can't she do it for you?"

"Tana nan, wannan aikin is very essential dole ni zanyi." Ya bata amsa idanunsa a kanta, ya ajiye takardun.

"Well, you're not getting your hands on this laptop har sai mun isa inda zamu, you need your revitalizing sleep." Agogon hannunta ta duba tace "Kaga muna da saura 1 hour 15 minutes kafin mu sauka zaka iya hutawa kafi nan."

Shafa sumar kansa Alamin yayi a gajiye yace "Bana jin Bacci."

"Shikenan sai mu cigaba da zama amma aiki sai mun sauka." Jasmine ta samun waje ta zauna da system din a hannunta.

Jasmine Baturiyya ceDonde viven las historias. Descúbrelo ahora