🌷Shafi na 35🌷

1.2K 128 52
                                    

Sautin kiran Sallah dake tashi daga wayar Alamin ne ya tayar da Jasmine daga bacci, dogon nunfashi taja takara kwantar da kanta, jin babu laushin filo a inda ta saka kanta ne yasa ta kai hannunta ta shafa. Da sauri ta bude idanunta tana kokarin tashi amma Alamin ya riketa, cire kanta tayi daga kirjinsa ta danyi baya amma yaki cika ta, hannu yasa ya gyra mata gashinta. Dagowa tayi ta kalleshi taga yana mata wani irin kallon tamkar yau ya fara ganinta.

Hannun biyu tasa ta dan tura shi amma ko motsi bai yi ba kuma bai ce mata komai ba sai na mugiya da ya zuba mata "Alamin, let go of me," shirun da taji yayi mata ne yasa ta cigaba da cewa "An kira sallah fa,"

Janyota jikinsa ya kara yi sannan ya kai bakinsa daidai kunnenta yace "Na sani," cikata yayi a hankali ya mike ya zauna a bakin gadon. Jasmine ma mikewa tayi ta zauna, a hankali ya juyo ya kalleta bai kara ce mata komai ba ya tashi ya fita daga dakin. Binsa da kallo tayi har ya fita daga dakin, itama tashi tayi ta nufi banɗaki domin yin alwala.

Sai kusan karfe goma Jasmine ta tashi daga bacci bayan tayi sallar asuba, a hankali ta sauko daga kan gadonta ta shiga bathroom tayi wanka sannan ta fito. Closet dinta ta shiga tana duba kayan da zata saka dan ta gaji da saka doganyen rigunan da Alamin ya siyo mata. Acikin kayan da tazo da su ta dauko wata farar blouse ta hada da bakin pencil skirt daidai gwiwarta, curling din gashinta tayi ta feshe shi da turaren gashi sannan ta raba gashin gashi biyu, wani ta sake shi ya zubo gaba dadai cibiyarta ya tsaya, sauran kuma ta saki shi ta baya ya dan wuce kugunta a tsayi, bata shafa komai ba a fuskarta ta dauki turarurakanta ta shafa a jikinta sannan ta saka bakin takalmi mara tudu sosai ta sauko kasa, dinning table ta nufa taga har masu aiki sunyi setting din table din amma ba'a taba abincin ba. Gym din bangarensu ta duba taga Alamin baya nan, Wayarta ta dauka ta kira shi bai amsa ba haka ta fita waje ta tambayi ma'aikatan ko ya fita aka ce mata bai fita ba. Kitchen ta shiga ta dauko tray ta jera masa abincin breakfast dinsa ta hau sama zata kai masa.

Tunda Alamin ya dawo daga sallar asuba ya kasa komawa bacci saboda tunanin Jasmine ko tasbir din da yake kullum kasa yi yayi saboda tunani, yasan zamansa da ita ya kusan zuwa karshen muddin bata fara sonsa ba, dan bai jima da yin waya da mahaifiyarta ba wato Anty Kaulat ta sanar masa zata dawo Nigeria. Duk da baya son Jasmine ta tafi yasan hanata haduwa da mahaifiyarta kamar zalunci ne sannan shi ba zai so ya zalunce ta ba ko da hakan zai cutar da shi, tabbas ya kamata ya haɗa Jasmine da mahaifiyarta. Amma idan tace bata son zama da shi ya zai yi? Anya kuwa zai iya rayuwa babu ita? Shin zai iya komawa rayuwar da babu wani annuri ko haske acikinta sai neman kuɗin da aiki? Lumshe idanunsa yayi yana ganin sufarta a cikin kansa a hankali ya fara furta addua "اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ، ابْنُ عَبْـدِكَ، ابْنُ أَمَتِـكَ، نَاصِيَتِي بِيَدِكَ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ، أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ، سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ، أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَداً مِنْ خَلْقِـكَ، أَوِ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الغَيْبِ عِنْـدَكَ، أَنْ تَجْعَلَ القُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي، وَنُورَ صَدْرِي، وجَلَاءَ حُزْنِي وذَهَابَ هَمِّي"
[ O Allah, I am Your slave and the son of Your male slave and the son of your female slave. My forehead is in Your Hand (i.e. You have control over me). Your Judgment upon me is assured and Your Decree concerning me is just. I ask You by every Name that You have named Yourself with, revealed in Your Book, taught any one of Your creation or kept unto  Yourself in the knowledge of the unseen that is with You, to make the Qur'an the spring of my heart, and the light of my chest, the banisher of my sadness and the reliever of my distress.] Ahmad 1/391, and Al-Albani graded it authentic.
Ajiyar zuciya yayi kafin ya cigaba da cewa "Ya Allah, kaine ka hallice ni, kaine ka sanya min kaunar ta a cikin zuciyata, Allah ka dafa min ka sanyaya min zuciyata ka bani ikon yin tawakkali, Ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar."

Jasmine Baturiyya ceOù les histoires vivent. Découvrez maintenant