NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
AKWAI ILLAH!
ALKALAMIN MARYAMERHABDULWannan rubutu ba rubutu ne da kuka saba cin karo da shi ba, rubutu ne da ya dauko zallar gaskiya. Na so publishing dinsa a lokacin da na bada tsokacinsa, amma hakan bai yu ba saboda dalilan da na bar wa kaina sani.
Ga Akwai Illah ba a dunkule ba, ga akwai Illahn da mutane da yawa suke neman hanyar samunsa, ya sameku cikin sauki.
Gyara, kushe komai ma ina maraba dashi in ya zo ta hanya mai kyau. Nagode
MAIDUGURI BORNO STATE 8:50am
"Duk da rayuwa tana ci gaba da juya ni yanda ta so, ban fasa jin sassauci cikin lamurana ba tunda na riski labarin salwantar Kaltum".
Murmushi take sakarwa kanta tana k'arewa surar jikinta kallo a doguwar mirror [standing mirror] d'in da ke mak'ale jikin bangon fankacecen d'akinta.
Juyi tayi mai ban sha'awa tana k'ara fad'ad'a murmushinta.
"Wayyo ni Fanne dad'ina, ko ba komai zan fara sabuwar rayuwa, ga dukkan alamu Na'eem ya k'yasa cikin kwanakin nan. Me ya fi min hakan dad'i? Duniya juyi-juyi".
Murmushinta bai b'ace ba, tsantsar farincikinta da annurinta na bayyana saman fuskarta.
Ji take kaf duniya a yau, babu mahaluk'in da ya kai ta farinciki.
D'ago kanta tayi tana daidaita dubanta a kan k'aton hotonta da wata matashiyar budurwa, wanda a kallo d'aya zaka bawa kowaccensu shekaru ashirin da 'yan kai.
Murmushinta bai gushe daga fuskarta ba ta shafa hoton tana mai kad'e jikin, duk da ba k'ura ko kad'an a jiki.
"Allah sarki Kaltum aminiya, ina rasa dalilin da yasa wani lokaci nake jin ina tausaya miki a cikin zuciyata, bayan kwata-kwata bai dace inyi hakan ba, farinciki da annashuwa yakamata in dauwama a ciki, rashinki a gareni alkhairi ne.
Me nake k'aruwa da shi a wurinki a lokacin da muke tare? Meh kike saka min da shi a duk lokacin da alhairaina suka yawaita gareki? Sam babu komai, sai bak'in ciki da tashin hankali"
A lokaci d'aya annashuwar fuskarta ya kau, ta shimfid'a b'acin rai da tantsar tsanar da take yi mata bisa fuskarta. Abubuwan da ya faru a baya ya shiga dawo mata cikin kwanyarta.
"Na tsaneki, na tsani duk wanda zai baki farinciki, na tsani murmushinki, na tsani..."
Bata samu damar k'arashe zancenta ba, sakamakon k'arar wayarta da ya katseta.
Nauyayyar numfashi ta sauk'e tana mai kai dubanta kan gado inda wayar ke ruri.
Hannunta da ke kan hoton ta janye sai dai cikin rashin sa'a, hoton ya gauce yana barazanar fad'owa. A hanzarce ta cafke sannan ta janyo wayar tana duba mai k'iran nata.
"Na'eem!"
Ta karanta a fili tana mai wadata fuskarta da murmushi, bata d'auki wayar ba sai da ta kalli hoton hannunta, ta kad'a gashin idanunta murmushi bai bar leb'b'anta da ke wadace da jan baki mai d'aukan hankali ba.
"Bai kamata in rasa ki kuma in rasa hotonki ba Kaltum".
Danna wayar tayi ta mak'ala a kunnenta tana mai lumshe idanunta.
"HELLO"
Ta furta cikin sanyayyar muryarta.
LAGOS NAJERIYA
YOU ARE READING
AKWAI ILLA
Historical FictionTafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa. Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska. Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa...