10 Junairu 2017 10:00am
MAIDUGURI BORNO STATE
Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida.
Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa.
Kafin ta iso ya sak'ala wayar a aljihun bayan kujerar da zata zauna, d'agowarsa ya yi dai-dai da bud'e k'ofar tana masa sallama, fuskarta cike da murmushi.
Zama tayi ta rufe k'ofar tana mai ajiye jakarta a k'asa wurin k'afafunta.
"Ina gaisuwa ranka ya dad'e!"
Murmushi ya sakar mata, kansa kwance bisa kujerarsa yana kallonta cikin wani siga.
Bai iya amsa ta ba, yana kallonta cikin lumshe idanunsa.
Hannunta ta d'ago dai-dai fuskarsa, ta had'e babbar yatsarta da na tsakiya ta murza ya yi k'ara.
Hakan bai sa ya da'uke idanunsa daga kanta ba.
"Na'eem mana, kallon nan yana kashe min jiki".
Cikin sigar shagwab'a ta yi maganar ba tare da ta kallesa ba.
"Fanne kin min kyau kamar in sace ki in gudu, in ban kalleki ba wa kike so in kalla? Uhmm?"
Ko kifta idanunsa bai yi ba, bare yayi haramar tada motar su bar harabar gidan ya kai ta makaranta kamar yanda ta nema.
"Ki kalleni mana, me yasa kike min rowan fuskarki?"
"Ba rowa bane..."
Bata iya idasa maganar ba taji d'umin hannunsa cikin nata. Ba fatar jikinta kad'ai ba, har cikinta sai da ta ji ya amsa.
Bata san lokacin da idanunta suka lullub'a ba, tana jin bak'on yanayin da tun da take bata tab'a jin irinsa ba.
Ba dan ta so ba, ta samu kanta da janye hannunta daga nasa, bata saba ba, iskanci irin wannan bai samu gurbi a zuciyarta ba.
A barta da d'aukan wanka da rawar kai, amma keb'ancewa da namiji har ya samu damar rik'e hannunta bata tunanin ta tab'a yin hakan.
Yaushe ma Kaltum ta barta ta yi saurayi da zata yi irin wannan?
"Yi hak'uri Sweetheart, na kasa sarrafa kaina ne. Allah sarki Kaltum, ta yi k'ok'ari sosai wurin gyara min rayuwa, ina ma zan sake ganinta in kyautata mata kamar yanda ta kyautata min wurin gyara min lahirana".
Lokaci guda ta ji annurinta ya kau, zuciyarta ya tsananta bugu, bak'in ciki da b'acin rai ya bayyana a fuskarta.
Ta gefen ido yake kallon yanayinta, bai bari ta furta komai ba ya lalubo maganar da ya dace da yanayinta dan ya samu karb'uwa da yardarta.
"Samunki ya fi min komai, kin fiye min ita d'ari-bisa-d'ari, kina sona nima ina sonki, kina kulawa da ni fiye da yanda ita ta ke yi, kinsan ita Kaltum akwai d'agun kai wai gudun raini, amma ke? Ban ma san me zance miki ba, ina sonki dai sosai, fiye da yanda kalamai zasu iya furtawa".
A hankali ta ke jin b'acin ranta yana tafiya, kalamansa da ke fitowa cikin muryarsa mai sanyi ya sa ta fad'a duniyar farin ciki.
"Ka daina kawo min zancen Kaltum in muna tare, bana so".
A dake ta furta kalaman, tana nuna iya gaskiyarta a fuskarta da muryarta.
Kallonta ya tsaya yi da alamar tambaya.
"Kaltum ce fa? Aminiyarki, kishi ki ke yi da ita?"
"Ba kishi nake yi da ita ba, bana son jin sunanta a bakinka, bata kasance aminiya mai lura da yanayin aminiyarta ba, bata kasance mai k'aunata da bani abunda nake muradi ba, komai nawa take bin duk wata hanyar da ta san zata iya samu ta k'wace.
ESTÁS LEYENDO
AKWAI ILLA
Ficción históricaTafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa. Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska. Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa...