NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
AKWAI ILLAH
Alkalamin MaryamerhAbdul
03.
DAMATURU YOBE STATE 12:30pm
"Ahshh!!!"
Sautin muryarta da ke fita cikin wahala kad'ai zai sanar da akwai baiwar da ke kwance a wannan harabar.
Zafin ranar da ke setinta na k'ara mata azaba bayan na ciwon cikin da ke addabarta.
Kwance take, ta kasa motsin kirki a bakin kangon da kullum take samu ta rakub'a. Azabar ciwonta ya hanata shiga ciki ko ta samu inuwar da zai kareta.
Duk da lalurar hauka da ke damunta, bai hanata jin ciwon cikin nata ya kad'a mata hankali ba.
Idanunta rufuwa ya shiga yi a hankali, hannunta da sauran sassan jikinta na rawa, jinin da ke zuba mata ya yi yawan da ya b'ata kayanta.
A hankali muryar nata ya shiga disashewa, daga k'arshe ta daina furta komai idanunta ya rufe ruf.
••••••••••••••••
"Yusufa, yunwa nake ji gida zan wuce. Ban ci komai ba tun safe".
Yusufa ko kallonsa bai yi ba, ya ci gaba da waina keken d'inkinsa yana bin wak'ar Arashi da ke fita cikin wayarsa.
Wayarsa Jamilu ya d'auka ya sa a aljihunsa yunwa na ci gaba da nukurkusar cikinsa. Bai sake furta komai ba ya fice daga shagon.
Tun rabuwarsa da wannan mahaukaciyar hankalinsa bai kwanta ba, tunanin rayuwarta ya ke yi, me zai sameta a yanayin da take ciki? Shin zata samu mai taimakonta? Ko kuwa haka zata yi ta yawo?
Tafiya yake yana wannan tunanin, ganin wani abu kaman maciji gabansa ya sa shi dakatawa, ya kalli gabar, ya kalli yamma bai ga giftawar kowa ba.
'Me ya biyo dani hanyar nan dama? Neman sauk'i ko? Na had'u da rabona'
Ya fad'i a zuciyarsa.Idanunsa yake wullawa ko ta ina ko zai samu abun da zai kare kansa da shi.
Can dungun wani gini da yayi shekara da shekaru an k'i gama sa ya ga wani zungureren sanda. Taku biyu yayi ya isa wurin ya d'auko.
"Bismillah!"
Ya furta a fili sannan ya kwad'e kan macijin zuciyarsa na addu'ar samun nasara a kansa.
Macijin bai sake motsi ba, kansa ya tarwatse, jini duk ya b'ata jikin sandar.
Hamdala yayi sannan ya fara neman yanda za'a yi ya kawar da macijin daga hanya.
Yawon da idanunsa ke yi a farfajiyar wurin ya sa shi ganin surarta.
Hakan ya tsananta bugun zuciyarsa, tsoron ganin halittarta ya sa shi dakatawa na d'an lokaci.
'Me na ke gani haka?'
Yawu ya had'iye ya na kallonta, d'aya sashe na zuciyarsa na kwadaitar da shi isa gareta, d'aya sashen kuwa, illar hakan yake hasasho masa.
YOU ARE READING
AKWAI ILLA
Historical FictionTafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa. Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska. Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa...