06.

1.6K 180 30
                                    

Tsakanin Damaturu da Maiduguri awa d'aya ne da 'yan mintuna.

Basu wahala ba suka shigo garin Maiduguri da misalin k'arfe goma sha biyu na rana.

Kai tsaye Federal Neuro Psychiatric Hospital da ke hanyar Baga (Baga Road) suka nufa.

Basu sha wahala ba wurin sanin inda zasu nufa, kasancewar akwai d'aya daga cikin malaman Abor da ke aiki a can. Kuma tun kafin isowarsu ya sanar da shi komai.

Kud'ad'en da ke hannun Jamilu kaf sai da ya k'are, Abor ya ci gaba da biyan sauran gwaje-gwajen da za a yi mata.

Kasancewar babu danginta da ke kusa, hasalima ba a san inda ta taso ba, Abor ne ya cike komai yanda ya kamata.

Daga nan aka mik'a ta ga likita na farko a cikin uku da suka kamata su dubata. Basu gama duba ta ba sai k'arfe biyar na yamma.

"Toh Alhamdulillah, mun yi duk gwaje-gwajen da suka dace, sai dai ba a nan gizo ke sak'ar ba, dan duk wanda aka kawo mai lalurar kwakwalwa kafin a fara masa komai sai ya ga wad'an nan likitocin guda biyu, in an samu sab'anin fahimta tsakanin biyun nan sai a tura ga na uku kamar yanda muka yi mata yanzu".

Dr. Shamsuddeen da ke zaune cikin ofishinsa yake musu wannan bayanin.

Babban mutum ne, wanda a k'alla yana da shekaru hamsin da 'yan kai. D'aya bayan d'aya yake kallon Abor da Jamilu dan tabbatar da cewa suna fahimtan kalamansa.

"Mun yi bincikenmu, mun auna duk wani abunda za mu auna, mun rubuta saura mu tura bayananmu zuwa b'angaren da ya dace da ita. Babu laifi in kuka barta a k'ark'ashin kulawarmu kafin mu samu amsar gwajinmu daga wurinsu, haka zalika babu laifi in kuka tafi da ita har zuwa lokacin da sakamako zai fito a d'aura ta akan magungunan da suka dace".

Zama Jamilu ya gyara, ya d'aura hannunsa bisa teburin da ke gabansa.

"Idan na fahimceka, kana nufin babu wani maganin da za a iya d'aura ta a kai yanzu har sai lokacin da sakamako ya fito?"

Murmushi Dr. yayi, ya ajiye bironsa a kan takaddar da ke gabansa.

"Idan kuka ajiyeta a tare damu zamu ci gaba da lura da yanayinta, zai bamu damar karantar irin cutar da ke damunta, kuma a duk lokacin da buk'atar bata wani magani ya taso zamu iya bata, amma haka kawai ba tare da mun samu cikakken bayani game da matsalarta ba baza mu iya bata komai ba, dole sai mun jira".

Lashe busashshen leb'b'ansa ya yi ya jefa masa wata tambayar.

"Har zuwa yaushe sakamakon zai fito kenan?"

"Baya wuce kwana talatin, wani lokaci sati d'aya, wani lokaci biyu, wani lokacin sai a kwana na talatin d'in, ya danganta da irin wahalar da larurar yazo".

Kallon Abor Jamilu yayi, yana jiran shawarar da ya yanke game da barinta a nan ko tafiya da ita.

"A ajiyeta a nan d'in, in mun tafi da ita ma bamu san ina zamu ajiyeta ba".

Likitan bai samu damar amsawa ba k'arar buga k'ofarsa had'e da bud'ewa lokaci guda ya dakatar dashi.

"Sorry (kuyi hak'uri), ana nemana a T.H da gaggawa shine na shigo sanar da kai Daddy".

Yana tsaye bakin k'ofar yayi maganar, da alamu bai san da akwai mutane a ofishin ba ya shigo, yanayin maganarsa ya nuna hakan.

Saurayi ne sanye da farin kayan da likita ke sawa. Fari ne mai tsawo, bayi da jiki sannan bai kasance siriri sosai ba.

"Ok, zaka iya tafiya Mufeed".
Cewar Dr. yana d'auke idanunsa daga garesa.

Bai sake furta komai ba wannan saurayin ya fice, Dr. Shamsuddeen ya ci gaba da yi musu bayanin abunda ya dace suyi kafin barinta a hannunsu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 05, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AKWAI ILLAWhere stories live. Discover now