05.

1.2K 173 10
                                    

11 JUNAIRU 2017
MAIDUGURI/LAGOS 10:05am

Sabuwar wayar Nokia da aka kawo mata sati biyu da suka wuce ta d'auko jin rurinsa.

Hoton matar da aka sa mata dan gane me lambar ya sa ta fad'ad'a murmushinta.

"Fatima!" Ta furta a fili sannan ta danna wayar ta d'auka tana mai d'aurawa a kunnenta.

"Assalamu alaikum!"

Ta furta cike da fara'a. Muryar Fatima ta ji daga d'aya b'angaren tana mik'a mata gaisuwa.

"Maa yanzu zan taso, a yi min addu'a".

"Alhamdulillah, to Allah ya kiyaye hanya ya tsare, kin samu mai d'auko ki daga Airport d'in ko in nemo miki Na'e...?"

"Shi zai zo ya d'aukoni ma, ya ce kafin mu tashi in tura masa sak'o dan ya zo da wuri kar in zauna zaman jiransa".

Wani abu Maa ta ji ya mak'ale mak'ogoronta, hawaye ya silalo saman kuncinta, halaccin mutanen nan biyu a rayuwarta bata san ta ina zata fara saka musu ba.

"Nagode muku, Allah ya biya ku da mafificin alhairi".

Jin sautin muryarta cikin kuka ya sa Fatima katse wayar tana mai jin tausayinta cikin ranta.

"Kaltum where are you? (Ina kike Kaltum?)"

Ta fad'a a fili had'e da lumshe idanunta ta fad'a duniyar tunanin rayuwarsu.

Tabbas ko wani d'an Adam da nashi jarabawar, Allah ya basu ikon cinye dukkan jarabawarsu.

Hawaye ta ji ya sauk'o mata, tana jin zuciyarta na cunkushewa. Duk da abunda zata je ta samu a garinta na Maiduguri bai hanata komawa tushenta ba, bai hanata k'in bin duk wata hanyar da zai sada ta da 'yan uwanta cikin farin ciki ba.

Alhamdulillah take yawan furtawa a duk lokacin da tunanin rayuwarta ya bijiro mata.

Muryar matar da take sanarwa cikin speaker (abun magana) ya sa ta mik'ewa cikin takunta, ta d'auki jakar hannunta ta gyara mayafinta ta wuce dan shiga harabar da zata shiga jirgin da zai kai ta Maiduguri.

***
DAMATURU 10:10am

"Abor anya ba maganin bacci zamu d'ura mata ba?"

D'akin Falmata ya lek'a ta taga ya ke fad'an hakan, murmushin da take yi yasa shi shagala a kallonta, bai iya jin furucin Abor ba sai bud'e k'ofar da ya ji.

Kyawunta ya fito sosai, kayan da Falmata ta sa mata ya matuk'ar karb'anta. Anyi mata wanka duk daud'anta ya gushe, banda duhun da tayi bai ga nakasu cikin shiganta ba.

Ruwa Abor ya samu ya jik'a maganin baccin ya mik'a mata.

Ba gardama ta kwankwad'e tana mai kad'a kai tana murmushi. Ita kanta tana jin dad'in jikinta, Falmata na lura da duk lafiyar jikinta.

"Jamilu ka tafi ka d'auko 'yan kud'ad'en da kace kana da su. Sabi'u ya k'irani ya fito daga gida, gwanda mu gama shiri kafin motar ta iso".

Bai iya magana ba sai kad'a kai da ya yi. Sosai ta masa kyau a yau, bai san dalili ba yake jin tausayinta tun ranar da ya fara d'aura idanunsa a kanta, bare yau da ta canja daga mahaukaciya zuwa mai hankali a shigarta.

"Menene tarihin rayuwarta?"
Wani sashe na zuciyarsa ya tambaya.

"Allah ya baki lafiya".

Ya furta a fili sanin ba yi da amsar tambayarsa.

Juyawa ya yi ya bar Falmata da Abor suna tsaye gefenta.

Mintuna biyar bai kai ba ya dawo yana cewa su fito, Sabi'u ya iso.

AKWAI ILLAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن