02.

1.6K 208 78
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

Akwai Illah!

Alkalamin MaryamerhAbdul

02.

Hannunsa sanye da ankwa, doguwar kaca manne ta k'asa ya iso k'afarsa da ke zagaye da wata ankwar.

Da k'yar yake ajiye takunsa, idanunsa na lumshewa, leb'b'ansa ya bushe. Fatar jikinsa da ya kasance bak'i mai haske ya disashe, yayi fari.

Yawun bakinsa yake had'iya dan gusar da ishin da ke addabarsa.

A hankali yake takunsa cikin rashin kuzari. D'an sandan da ke biye masa na kallonsa ta wani siga, ba daman ya tunkud'esa yayi sauri.

Wurin da aka tanada dan tsayuwar wad'an da ake tuhuma d'an sandan ya sa shi, ya jawo k'ofar ya rufe.

Hannunsa Hamza ya d'aura a kan katakon da ke gabansa yana mayar da numfashi.

Kallonsa Alk'ali ya tsaya yi ta saman gilashinsa, yana lura da yanayinsa.

Bai furta komai ba na tsawon sakanni goma muryar Barrister Anthony ya doki kunnuwarsa.

"Sunana Barrister Anthony, lauya da ke kare wanda ake k'ara ya mai shari'a".
Ya russuna kad'an alamar girmamawa.

"Sunana Barrister Fatima, lauyar da ke kare wanda ya kawo k'ara. Nagode"
Ita ma ta russuna sannan ta koma mazauninta.

Gilashin idanunsa ya gyara, yana kallonsu d'ai-d'ai.

Sai da ya nisa sannan ya gyad'a kansa alamar bismillah.

Mik'ewa Barrister Fatima ta yi ta gyara rigarta, tana mai dai-daita tsayuwarta.

"Ya mai shari'a, ina neman a bani daman farawa da k'orafi akan yanayin da Hamza ya shigo."

Kad'a kai ya yi yana sauraranta.

"A yanayin da Hamza ya shigo wannan kotu, ba sai an tambayesa ko bincikesa ba, yana hali ne na yunwa, ya galabaita. Ana azabtar da shi da yunwa tun kafin a tabbatar da zargin da aka d'aura masa, wanda hakan ya sab'a shari'a.

Ina neman alfarma wurin kotu, da ta hana wannan cin kashi da ake masa, na hana sa samun wadattaciyar cima da kuma ruwan sha.

Dan har a lokaci irin wannan zargin da ake d'aura masa bai tabbata akansa ba, kuma ko da ya tabbata, alhak'in hukuntasa na ga kotu, sai ta bada hukuncin da ya dace dashi dai-dai da laifinsa".

Ta russuna kad'an
"Nagode ya mai shari'a, a duba bayanaina".

Zamanta ke da wuya Barrister Anthony ya mik'e, fuskarsa a had'e tamau.

"Ya mai shari'a, a yanayin yanda aka kama Hamza, an kama sa ne a yanayi na ta'addanci, an kama sa ne a tare da su 'yan ta'adda, wanda dukkaninsu sun bada kai sun amince da zargin da ake musu, Hamza wasa da kotu ya ke son yi, wanda 'yan sanda suke son sauk'ak'a wa kotu wahala, azabtar da shi shine kad'ai hanya mafi sauk'i da zai sa shi amsa laifinsa duk taurin kansa".

Bai zauna ba, idanunsa na yawo akan Alk'ali da alk'alaminsa. Gyarar muryarsa ya sa shi komawa mazauninsa.

"Barrister Anthony! Kotu na buk'atar ka karanto shafin da k'undin shari'a yace d'an sanda ya azabtar da mai laifin da ba'a tabbatar da laifinsa ba?".

AKWAI ILLAWhere stories live. Discover now