MATAN ALI

3.6K 80 2
                                    

[7/2, 1:54 PM] Bilkisu Bilyamin: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_

            ®
_Nagarta writter's Association._

       _Mentor's_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_

                ®
*BILKISU BILYAMIN*

             120-125

        Shiru-shiru yaga Saude ta kawu ruwa bai ga ku 'kiyarta ba,ga kishin ruwa yana ji,ana cikin wannan hali ne sai ga Yayan *_DEJI_* ya shigo gidan,sa'bi da fatanya a kad'ar shi, yayi sallama daga can d'akin Malam Audu ya amsa yayi kiran shi.

      Yace"bani ruwa mai sanyi a tulu insha"

     "Inna bata nan ne?"

       Yake tambaya yayi hanyar d'akin Saude ya d'auku kofi ya kaima Malam Audu ruwa,turus yayi da ya iske Saude zaune saman tabarma tana daman fura.

     Yace "nama d'auka bakya nan ne Baffa yace in kawo mashi ruwa"

     Banza tayi dashi ta cigaba da dama furarta,amman cikin zuciyarta tana jin ba dadi yanda take ma Malam Audu haka,duk da a ciwarta shiya d'aukar ma kanshi, kuma ta kudurta cewa bata ga ranar barin wannan rigima ba har sai sanda ya maidu mata d'iyarta gida.

     Tsawa ta daka mashi tace"zaka tashi ka kaima Malam ruwa ku kuwa,ka nime waji ka zauna"

     Tashi yayi yana kara mamakin canjin da yake gani a gidan tun bayan auran 'Kanwarshi *_DEJI_* abubuwa da yawa sun sauya ciki hadda kuda yaushi Innarshi tana cikin bacin rai da kuka, kuma ta daina fira da Baffan shi hatta abinci sai dai ya d'auka ku kuma ta aika shi ya kai mashi.

     Mud'a ya d'auka ta silba inda ya ga tana dibar mashi ruwa ya cika ya saka marfi ya d'auka ya kai mashi turakar shi,amsa yayi yasha yace"da fatan yau ka gama idashin nomar nan?"

     "Eh na gama Baffa,yaushi za'a zuba takin?"

      "Muna iya bari kamar nan da kwana ukku haka ku hud'u ko?"

      "Eh to Allah ya kaimu"

    "Ameen,idan ka gama hutawa zan aiki ka gidan Alhaji Iro(mahaifin Saude kinan)"

     "To Baffa,ya zanci mashi saboda daga masallaci in nayi sallah sai in wuce"

     "Kaci zanzo in same shi bayan sallar isha'e"

     "To Baffa,bari in kawo maka furar"

     "Babu damuwa,ngd Allah yayi maku albarka,yasa alkairi a rayuwarku"

     Har cikin ranshi yaki jindad'i addu'ar mahaifinshi gari su shida 'yar uwarshi,ya Inna take tunanin Baffa zai iya saida *_DEJI_* zai samu lokaci su zauna yayi mata bayanin yanda abin yaki, kuma mutumin da Baffa ya ba d'an shi Auran *_DEJI_* mutumin kirki ne yana da alheri sosai da karrama mutane.

     Tashi yayi ya kuma dakin Saude ya tsaya yace"ina furar Baffan in kai mashi"

     Kwarya ta mika mashi sannan ta tashi ta haye gado tana jin ranta babu dadi.

     Bayan ya kaima Malam Audu furan ya kuma d'akin saude ya zuba tashi yasha ya kushi sannan ya shiga dakin shi ya cire kayan da yaje gona dasu ya watsa ruwa, sannan yasan ya masu haske sosai, yana da tasafta matuka,kuda yau shi zaka ganshi cikin tsafta gwanin ban sha'awa,alwala yayi sannan ya ji bakin 'kufar Malam Audu yace"Baffa sai ka tahu nayi gaba"

     "Nima ganinan bayanka ruwa kawai zan watsa in tahu,insha Allahu"

     Masallaci Jauro ya nufa shikuma Malam Audu ya dibe ruwa yayi hanyar bayan daki  da zummar yayi wanka,shima yayi shirin masallaci.

MATAN ALIWhere stories live. Discover now