MATAN ALI

8.4K 308 117
                                    

[8/9, 6:58 PM] Bilkisu Bilyamin: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_

            ®
_Nagarta writter's Association._

       _Mentor's_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_

              ©
*BILKISU BILYAMIN*

*_Vote me on wattpad @Billybilya_*

    *_This page is for you, munayshat and Ashnur love y'all_*


             240

Duk yanda Munayya tasu tijara a wajan taga babu damar hakan,kwafa tayi tace ma peter zasu hadu, _next meet_,zai raina kanshi.

   "Sai dai idan Ya Ali ya dawo,amman indai ina gidan nan babu wannan maganar"

   Tsaki tayi tace"sa'idawa masu zuwa lahira da kukun dambu,banza kalarki kalar azzalumin wanki gadan jaraba"

    Dariya Aminatu tayi tace"oho dai kwadayi yasa aka aure yayana, munga yanda za'ayi handama ai,marasa wadatar zuciya,diyar tsohun barawo"

    Tsaki tayi ta kuma cikin gida saboda ga alama wannan ta fita rashin mutunci, _saukinta ma Allah yasuta Munnera bata nan da taga lagwanta yanda ta matsa mata,Allah yasa dai ba zama zatayi dasu ba aikuwa da,da akwai matsala._

    Bayan ta Aminatu ta ruf, itama ta shigo cikin gidan,duguwar kujera ta samu ta zauna,sannan ta kira Ali take fad'a mashi yanda sukayi da Munayya,dariya yayi yace"kada ki sake ki raga masu,sannan kada peter ya kara shigowa da sunan dafa abinci,kuwacce ta dafa da kanta,ki dai nasan baki da matsala saboda huran Hajja ce"

     "Eh gaskiya,amman Ya Ali wannan matar taka batada mutunci kaga yanda take zagin ma'aikatan gidan nan kuwa"

    "Shiyasa nace kizo dan nasan zaku dama rashin mutunci da ita, _i know very well_ zaki iya da ita"

     "Kasan bana san hayaniya fa ya Ali"

   _"Just do it only for me"_

   "Ya Ali masifar?"

   "Eh mana,ai kinga ga ranarta tazo kuh"

    Dariya sukayi gaba dayansu bayan sunyi sallama yake fada mata _yana cikin skul amman idan ya samu natsuwa zai kirata_
   

   ABROAD....
   LONDON

    Gidan da suka sauka maikyau ne dai dai misalin zaman mace hudu,kuma feye da haka,amman kuma falone babba sai 5bedroom a cikinsa, sai kichen guda biyu, sai wajan daining table shima babba wanda zai iya cin mutum goma,manyan kujeru ne seatbiyu aka kawata falon dasu,gefe daya kalar black and orage ne,gefi dayan kuma Ash and black,sai dankaririyar plasma wadda ta kusa cinye bango daya manne jikin bango,kumai na falon gwanin ban sha'awa,Azeema ta dauki daki daya,itama Munayya ta dauki daki daya,sai kuma daman Ali akwai dakinshi a gidan saboda nan ne gidanshi.

   Yau kwana biyu da saukarsu amman har yau basu saka Ali a ido ba,tunda ya shigo ya ajiye kayan shi,wani abokinshi yazo ya dauke shi basu kara saka shi a ido ba,ba kuma wai dan ba gidan yake kwana ba,sai dan sanda zai shigo gida sun dade da bacci sanda zai fita basu riga sun tashi ba,duk da yana bala'in takura da hakan,ji yake kamar ya bar masu gidan ya sake gida,saboda yayi imani idan har zasu cigaba da zama inuwa guda babu abinda zai hana basu ga tasku ba.

    Yauma kamar kullum Munnera ta fito daga ita sai wata shigeyar riga jikinta wadda bata da maraba da zindir,wata mahaukaciyar mika tayi sannan ta wurga kanta saman kujera tana fadin "wash Allah na"

MATAN ALIWhere stories live. Discover now