MATAN ALI

3.9K 95 6
                                    

[8/3, 5:19 PM] Bilkisu Bilyamin: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_

            ®
_Nagarta writter's Association._

       _Mentor's_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_

              ©
*BILKISU BILYAMIN*

*_Vote me on wattpad #Billybilya_*
*_#Anatari_*
*_#bilkisubilyamin_*
*_#love y'all_*

             225


    Gaba d'aya matan gidan sun hallara tsakiyar falon kuwa yana kwasar gaisuwa wajan Alhaji Ahmad surukinsu da Hajja,'yar nasiha Alhaji ya karayi masu da lallashin Munayya da Deji akan da yayi wata ukku zai dawo da Munnera da Azeema ya tafi dasu,kada su damu su kuma tada hankalinsu,ya kara da shi masu albarka.

    Babu kunya Munnay tace"Alhaji ai tafiyarshi ta feyi mana alkairi saboda tunda aka kawo mashi mu gidan nan bamu taba minti biyar cikin kwanciyar hankali ba,daga shikaran jiya zuwa yau huran yunwa yake mana"

    Karaf a kunnuwan Ali wanda fituwarshi kinan daga dakinshi yana daura agogon hannu,yaji maganarta ta karshi _da yunwa yake barinmu_ wani mugun kallo suka jefi juna dashi.

    Ran Alhaji idan yayi dubu a bace yake,a fadace yakai dubanshi akan fuskar Ali yace"maganar da ta fada gaskiya ne ku karya ne?"

    Shiru yayi saboda baida bakin magana amman yasan daga jiya ya fara yi masu haka kuma ai akwai kumai aje girka masu ne dai yace an daina.

    "Karya take Baffa ku yau ma abinci da yawa aka dafa har barinshi akayi, sai dai masu aiki suka dauka suka cinyi,bai barinmu da yunwa"

    Ranshi yaji yayi sanyi da yaji abinda Deji ta fada amman yana san ya gasgata abinda ita Dejan ta fada ya dubi Azeema yace"abinda ta fada gaskiya ne ku ya abin yake"

     "Ina azumine shiyasa ban sauku kasa ba kwata kwata yau sai da zamu tafi din nan"

      "Maganar kwana biyu da ya wuce fa?"

     "Yana bamu,kuma akwai wadatacci a cikin store duk mai so sai ya girka"

     "Ku kuke girka abinku tunda kuka zo kinan"

   Da sauri Deji tace"wannan christan ne yake dafawa kullum daga safi zuwa rana hadda ma na dari"

     Masha Allahu bana fatan a kafa rashin adalci a gidan nan duk mai wata matsala kada yake fada,kumai yayi maku a sanar dani"

     Ido Hajja ta kura ma Deji saboda ta gama fahimtar duk abinda Munnayya ta fada haka yake,amman Deji tayi saurin kari laifinshi irin wannan matan sune ake alfahari dasu,kuma kuwace uwa take san danta ya aura.

    Waje Ali ya samu ya zauna ranshi na kuna yace"Alhaji barka da yamma"

     "Barka dai,da fatan kun gama shiri?"

      Kamar baya so yace"Eh,mungama"

    "To muna iya tafiya ai ko?"

    Gaba daya suka tashi,domin tafiya har sun kai bakin kofa Alhaji yace"ku bazaju ji rakiyan mijinku ba?"

    Ba kunya Munayya tace"Allah ya raka taki gona,zan huta da jaraba"bata taba tunanin cewa gaban sirikinta take ba,saboda kunya Deji kasa tayi da idonta saboda bata saba ganin wannan rashin kunyar ba.

    Ran Aminatu bace tace"ke wai uban waye ubanki da kike san kiyima mutane rashin kunya"

     Tsawa Alhaji ya daka mata yana yi mata gargadi da cewa matar yayanta ce.

MATAN ALIWhere stories live. Discover now