MATAN ALI

5.5K 114 8
                                    

[7/20, 8:23 PM] Bilkisu Bilyamin: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_

            ®
_Nagarta writter's Association._

       _Mentor's_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_

              ©
*BILKISU BILYAMIN*

        _Ina mika sakon  gaisuwa ta,ga 'kannai na,kuma masoyana,abin a'lfaharina,a kullum ina maku fatan a'lkairi da rayuwa d'urariya,Allah ya dauwamar da rayuwarku cikin sunnar Annabi mohammadu sallallahu alaihi wasallam, *Faty BB,Autar Hajiya,Beibei Isa,Feedoom,fiddausi sodangi*_

*_Vote me on wattpad @Billybilya_*

             175

*RIGAR MALAM AUDU*

     "Baffa wai mai ka keyi a gona tun asuba da ka fita?"Jauro yake tambayar Malam Audu da yake ta faman noma babu ji babu gani.

      Dan tsayawa yayi yace"idan ma naje gidan mai zan iski inba bacin rai ba"

    "To yanzo dai Baffa ka barshi haka muje gida kaga wani abin mamaki"

       "Ai ni na gama shan mamaki wajan Saude,abinda ya rage kawai ta fara zagina,shi kadai yayi saura"

       "Allah ya kyauta ma Baffa haka bazata faru ba"

     "Kayya dai Jauro, ana kan hanya"

     "Ni dai Baffa mutafi kaga abinda nake san ka gani a gidan"

       *_"DEJI_* ce tazo koh?"

          "A'a Baffa,kadai bar noman haka mu tafi gida nasan sai ka bani goron albishir"

     "Saura kuyya biyu in idasa, bari in 'karasa sai mu tafi inga wannan abin da kake ta faman fad'a mani,kana farin ciki"

      Amsar fatanyar yayi yace"Baffa kawo in 'karasa da sauri mu tafi,ka isa can rafin ka gyara jikin ka kafin nan na idasa sai mu tafi"

      "To,bari inyi sauri "

A bayan keken shi ya goya Jauro suna tafiya suna fira ta rayuwar duniya da al'amuran noma,

     Saude ta riga ta sare da batun Malam Audu,hankalin ta ya gama tashi ta fidda ran,dawowar shi kusa kusa,d'aki ta shige ta saka kuka tana dana sanin abinda ta aikata.

      Sallamar Jauro taji cikin kunnanta, amman ba taji ta Malam ba,sai da Jauro ya shigo yake fad'a mata Baffa fa ya dawo,da hanzarinta ta fito ta iske shi garkin shanu yana kukarin kwanci masu ciyawar da yayo a gona.

      "Sannu da zuwa Malam"

     Bai amsa ba saboda bai tsammaci itan bace,daman baisa aka za'ai mashi tarbar arziki ba.

    "Malam naci sannu da zuwa kayi shiru"

   Juyuwa yayi,yana mamakin abinda yake ji daga bakin Saudanshi.

     "Yauwa Saude,ya gida?"

    "Gamu cikinshi"

Keken ta amsa ta gungurashi can inda ake adanashi sannan ta fito tana tambayar ya aikin gonar.

     Kanshi d'auri yake tambayar zuciyarshi shin Saude ta sauku ne ku kuwa dai gizo take mashi,Saudan da yasani dai har ya fita yau baima ga kiyarta ba,daki ya nufa zai wuce yana kukarin dage igiyar ya wuce sai yaga kayanshi saman igiya an wanki so fes,ga kuma gida yasha shara,bai idasa tsuriwa da mamaki ba sai da ya 'kara shiga dakin shi yaga kulolin da ta saya tana saka mashi abinci,a duk lokacin da take cikin nishad'i ku kuma soyayyarshi ta mutsa to kuwa anan zata saka mashi,ya gani hakan ne ta yanayin zaman takewarsu.

MATAN ALIWhere stories live. Discover now