1 LAIFIN WA. . ?

1.9K 81 0
                                    

#ANATARE.

LAIFIN WA?.
  By Real Autaras. Autar Hajiya❤️

    I can't clarify how u are to me, I just expectation good life for u and our Up coming baby HAUWA MOHD JABO {Mrs ENG ALIYU} u means all to Autaras #ILYSM My Mentor.

1

Fitowar ta kenan daga Diamond Bank wanda ke kan titin Bank road kusa da first office cikin garin kano.
Da alamar kud'i taje cire dan ga ATM card d'in ta nan a hannun ta sai kuma kud'i wanda zai kai kimanin Dubu d'ari duk a hannun ta sauri take dan tana tafiya tana saka kud'in cikin jakar ta k'irar MK.
Wayar tace tai k'ara alamar shigowar kira. Tsayawa tai ta d'auka. ..
"Hello Dady"
"Hello Zahra..kina ina? nadawo naga ba kya nan kuma Maman ki tace ke d'aya kika fito batare da driver ba...me yasa baki jira Yayan ku yazo ya kaiki ba,banson kina driving ke kad'ai?.
"Oh Dady on my way fa.....danma Allah yasa naga Autar hajiya ta taimakan na cira amma wallahi da still now ina kan line..
Da nazo kan Machine nasu duk akwai layi...daga na wajen har na ciki,so saina shiga nai withdrawal nan ma layi maybe anyi salary ko kuma y'an kasuwa ne...Ina fitowa kuma sainaga Auta itada wata staff nasu shine fa nabata aka ciren.
Ok to maza ki tawo gida....ok Dady saina qaraso. Tafiya tafara zatai k'ok'arin tsallakawa inda tai parking motar ta baya da State CID.....daidai tsakiyar titin wata mota k'irar Accord VC ta tawo da gudu baikula da tafiyar matashiyar budurwa saidaya zo daf da ita kana yai k'ok'arin kaucewa itama k'ok'arin komawa da baya take shi kuma yana k'ok'arin yin bayan dan yabata damar wucewa ta gaba amma inaa......k'addara ta riga fata dan duk kaucewar su saida akai abinda ba'a so wato accident.
Gaba d'aya motar tai kanta sama tai sannan tayo k'asa kanta ne ya bugu sosai....da gudu gayen dake tuk'a motar ya fito yai wajen ta.
Baijira komai ba sunkutar ta yai kawai sai jakar ta dake rataye a kafad'ar ta yai cikin motar sa.
Gudu sosai yake da ita k'ok'arin sa ya kaita asibitin sa dake Sultan Road....HUAZHONG HOSPITAL .
Wayar sa ce tai k'ara....da kamar bazai d'auka ba...amma jin sautin wak'ar yasashi d'auka.
"My Auwab kana ina ne?, najika shiru kasan fa nan da 3 hours flight d'ina zai tashi ina sauri nagama komai a Asibiti kafin natafi...
Mom....MOM accident nai na kashe wata yarinya ina hanyar clinic d'ina...Mom koina jikin ta jini yake na kasheta sai yasawa Maman nasa kuka dama daurewa yake amma ganin yadda kayan sa ya b'aci da jini kuma yarinyar bata motsi yasaka shi tsinkewa da al'amarin.
Noo Son kada kuje Clinic naka tawo nawa maza yi sauri ku k'araso....Mom nawa yafi kusa da inda muke muna wajen Asibitin Nasarawa. ...oooo I said don't go....ka kawo ta nawa ina nan maza ku tawo 'YanKaba ba nisa da inda kake....Tom am coming now.
Da sauri ya karya kwana yabi ta State Road yafita titin da zai kaishi 'Yankaba.
Ita kuwa Maman duk yadda take sauri haka ta ajiye komai tafara jiran Tilon d'an nata da peteint d'in tasa.
Kayan ta ta canja zuwa na Doctor sai medical glass nata data sanya....bakin reception d'in ta koma tana jiran zuwan sa.
Kai komo tafara har wasu na tambayar..Madam is there any problem?, amsa take basu da Noo....
Can tana shirin juyawa tajiyo k'aran bud'e gate. Da sauri ta fito....ilai kuwa shine da gudun ta ta nufesa kafin ma taje harya fito da budurwar a hannun sa a gigice fuskar sa jawur alamar yaci kuka ga jikin sa jini kamar an yanka saniya.
Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un bakin Hajja Zainab ke furtawa, a yanda taga budurwar ita kanta ta sare da ita.
Da hanzari aka d'akko gado aka d'ora ta sai Theater room.
Dashi aka shiga nan fa likitoci suka taru akan ta dan ceto ranta. Agajin farko surgery sukai mata akanta sai gefen kunnen ta k'afar ta d'aya tai tsagewar k'ashi hannun ta kuma karyewa yai na hagu.
Almost 3 to 4 hours suna aiki akan ta kafin a sakamata oxygen dan jawo numfashin ta.
Auwab yana gefe a theater amma baida k'arfin bata taimakon sa...yanadai kallon komai...ya kuma k'ara godewa Mom data kasance UWA tagari gareshi.
Saida suka tabbatar angama komai kana Hajja Zainab tasamu kanta.
Rarrashin sa take akan komai fa yanada sanadi kuma Allah ya rigada ya rubuta sai hakan tafaru so kadaina damuwa fatan mu yanda akai aiki a sa'a ta farka in time.
Last issue kuma ya maganar samun iyayen ta?, kuma kaga yanzu fitowa ta akamun waya jirgin yai landing so ya zamuyi?.

@ut@r H@jiy@

LAIFIN WA..?Where stories live. Discover now