LAIFIN WA? 29

414 23 2
                                    

LAIFIN WA?

Na
Re@l Autar hajiya

  29.

Zama tayi a hankali Momy ta d'akko macen ta bata wadda take ta tsotsan hannu fara sol da ita kamar tsada.
Baby bata tasha kunga sun jima da tashi lokacin baki tashi bane. Da kai ta amsa abinda kullum take fatan gani kenan ace yau gata tana feeding babyn ta to gashi Allah ya kawo lokacin.
A hankali ta ciro na barin hagu..har zata bata Momy tace baby na dama shiyafi koh?, Tom ta amsa a kunya ce dan gaskiya tanajin kunyar Momy..bud'e k'ofa akai  ba kowa bane face Auwab kallon baby yayi itama kallon sa tayi a kunyace sabida taga idon sa kyam a Boobs d'in ta da suka ciko tana feeding baby girl.
  Gefen ta ya zauna bayan ya amshi babyn duka biyun a hannun Momy...zuba musu ido yai tana tasbihi da kirari ga shugaban Hallita baki d'aya,  baby I'm sorry banson nasaki jin ba dad'i kinji?, murmushi tayi masa bayan ta shafo gefen fuskar sa tace my prince charming wayace baby tayi fushi....ita bata fushi da sanyin ranta ya kaga babyn mu?.
Matsowa yai kusa da ita sosai yace baby they are all fine and amazing babies....kawo little Zainab ta k'oshi abawa little Abdallah da little FAUWAN.
Momy dake bayan su jin sunan daya ambata ne yasata cewa Auwab...me kace?, yes Mom sunan su kenan yanzu nayi musu hud'uba dashi sunan Dady da sunan Dadyn Baby sai ke...wow son kamin komai Allah ya biyaka common my little..d'aukan ta tayi tana murna..da tagama ficewa tayi dan zuwa ganin komai ya daidaita tanason ayi discharge nasu yanzu.
Tnq prince kaiwa Dady takwara zaiyi murna...I know zaiyi yammata...uhm na tab'a please?, me zaka tab'a kaifa prince bakada kunya wallahi...eh naji kafin tace komai yafara latsa Boobs d'in ta..osh zafi bari ko namaka ihu....tare suka sanya dariya a haka Momy ta shigo ta samesu. Kayan da aka kawo ta d'iba kafin ta tabawa wani yakai motor baby guda ta d'auka suma suka d'auki guda suka tafi gida.
Gaskiya yara sunzo da goshi dan matan governors ministers prime minister...kaf sune sukazo ganin baby da matan sarki gidan su ya cika sosai da mutane dan Kota ina zuwa ake ganin baby basu suka sami sarari ba sai bayan sallah Isha'i.
Nurse biyu Momy ta samo dan kula da ita da babyn. Baby inason magana dake pleas, prince ehem inaji ta fad'a bayan ta ajiye little Zainab akusa da ita.
Baby dan Allah inason ko namiki laifi ki ringa mun afuwa fushin ki na tadan hankali banson abinda ranki zai b'aci nakan ji kamar na kashe kaina ne a duk lokacin da kikai fushi kuma waini na b'ata miki kinji?, kanta ta kwantar a kafad'ar sa tace prince insha Allah nadena d'azu ma bawani haushi naji ba....kaji baby na danma yanzu katashi a baby masu abu sunzo. Su wa ya  fad'a  a shagwabe? yara mana...wallahi ban yarda ba ai nawane aro na basu kawai.....haka Momy da Dad suka zo anata hira.
Saida tayi waya da Maman ta da Dady kafin ma tayi bacci...Happy family.

Nigeria.

Wai kai Arfat kana nufin zama zakayi har sai sunzo gaskiya nidai Visa zan nema......nima tunani na kenan fa wallahi Sameer ya za'ayi to?.
Adnan ne yace Fauzan kayi shiru? dariya ya saki yace wai ku angayamuku ni ku ne?, tuni naiwa dan gidan Ambassador waya inason visa ta mutum 4 tum jiya d'azu ya kirani ma yake cewa ansamu tickets kawai zamu siya daga yanxu xuwa ko yaushe zamu iya tafiya.
Ihu suka saka jin bayanin Fauzan, amma guy d'in nan ka iya suprise gaskiya we ar happy.
  Kakus ce tace yo nima sai anje dani dan ba...haba Kakus keda zatazo wanka nan ba dad'i na kije tunda uwa ce ke ga Momy nan sukai convincing nata ta hak'ura amma da kyar......daga nan shiri suka fara bayan kowa yaiwa iyayen sa bayani...Mama murna tayi ganin kina komai yar ta ake so haka.
******
Prince wai kai mene ka kori nurses d'in kazo kana damuna?,  haba baby nakasa zama gurin da babu ke shiyasa. Ehem idan Momy tazo fa?, she can't send me out Momy is wise fa kuma kinsan I can't do anything for u apart from kiss..and hug.
  Ok...ga Little Abdallah yanata mutsu mutsu yak'i bacci, Abbun sa yake son gani common Boy cak ya d'aga shi yana masa wasa...oho jinjiri ne saidai yaita kallon sa amma ba damar dariya ko wani abu saida yagama wasan sa dashi kana ya ajiye shi lokacin har yayi  bacci.
Kusa da ita ya matsa yace baby me kike so game da suna kuma kinduba kayan komai yayi ko akwai abinda za'a k'ara?.
Haba prince kaya sunyi saidai muce Allah ya saka da alkhairi dan kayan ma sunyi yawa...Momy fa trolley set ta had'omin ga kuma na baby gaskiya banda abin cewa saidai Allah ya k'ara maka sona.
Baby amma ke muguwa ce idan sonki yafi haka ai haukace wa zanyi....ai kece zakice Allah ya k'ara miki son prince dandai kad'an ake sona.
Murmushi tayi tace yauwa prince alfarma nake so....please kada kace a'a saboda abinda nakeson fad'a har raina.
Prince inason mu bawa Momy takwaran ta kodan kirkin ta da son d'a take mana..kaga batada kowa a kusa da ita kaine ka rage mata kuma gashi ka rabu da ita dan ba zaman China zakai ba bare ace zata ganta at anytime she need.
Abdallah kuma Mama zata so yaro a gunta kodan ganin itama ita kad'ai ce....yaran mu ba zasuyi danasanin zama gun kakkanin su ba...Bayan haka kodan karatun yaran nan ma so su zauna waje guda.
Kakus ta girma amma ganin jinin ka kusa da ita zataji dad'i sosai tana son ka tana k'aunar ka...amma a haka duk son d'a Momy take maka ta yakice tabarka gun Kakus itama a bata FAUWAN..
Momy tanason mace Allah baiba ta ba saida taji an haifa amma idan muka bata mafarkin ta ya cika ne koda ba itace ta haife ta ba d'an ta da tafi so shine ya haifa.
Prince ta kira sunan sa a ladabce kana ta tsuguna kusa da shi tace wallahi ko duk one year kake son na haihu kuma koda zan sha azaban da tafi wannan ne zan haifamaka yara indai Allah yabani.
  Dama tunda na aure ka nake tunanin bawa Momy d'ana kodan k'aunar da take mana....gashi kuma ikon Allah yabamu uku a lokacin da bamu zata ba.
Ina budurwa  ban tab'a sha'awar yara fiye da biyu ba....amma gashi tun banje ko'ina ba Allah yaban uku ka yarda karka ce a'a Allah zaibamu wani ina yaye su sai mu basu kaga sai mu haifo namu....indai kana sona kamun wannan.
Tana gama maganar ta mik'e ta hau kan gadon.

Auta ce

LAIFIN WA..?Where stories live. Discover now