LAIFIN WA? 33

522 24 1
                                    

A cikin mota Prince dai yak'en dole yake dan gaskiya yanason yaran sa kusa dashi amma ya ya iya baby ce..
A'a wana ke gani takwara tace haka ta girma? ...da gudu Iman ta tafi ta rungume Momy...tana dariya kamar ta Santa sosai.
A haka su Auwab suka shigo..shima Ayman ganin Kakus gunta yaje yana jan gashin ta..a'a Fauwan ne dama nasan zaku zo shiyasa namaka danwake zakaci?, eh zanci Kakus yace cikin gwarancin sa dariya sukai.
Momy ya kike kinsauka lafiya?, lafiya lou baby munsameku lafiya? Alhamdulillah Momy.
Masha Allah ina Maman ki ai munyi waya yanxu nace mata na sauka, ok nace kana na dan mike k'afata dan na huta..kallo Momy tabini dashi wanda nasan ganin cikin ne yasata...batai magana ba illa murmushi da tai.
Baby ki zauna daidai ga pillow can Auwab mik'omata zata fin jin dad'i ta fad'a.
Amal ce ta miko min wadda ta sake sai zubawa Momy hira take muma zama mukai saida aka bamu tsarabar mu dan Auwab cewa yake Momy banga jaka ta ba..itakam cewa tai yara naiwa banda kai.
Aa yau Autar Umma ce a gidan?, nice Ya Haleem kaganni ni kad'ai na taho shi sai nan da two weeks yanada meeting ne nikam nace nayi missing gida dole nazo.
Ayya Zainab da kin bari?, a'a gashi dai na taho...Ina yini Yaya ya yaran?, lafiya lou..Amal wato baby ta kwace mana ke koh?, Abba gidan ta yafi dad'i kuma yafi kusa da school d'in mu shiyasa.
To madallah...Zaman mu mukai inda Momy sai nan nan take dani komai tace baby me zakici ko kinason wani abin?, na kan ce a'a saboda ni komai ci nake.
Sai da mukai Isha'i kana muka fara haramar tafiya....Hannun Iman na kama naje gun Momy nace Momy ga takwarar ki sai ayi hak'uri zama da ita dan bataji....dariya tai tace inye anan zaki kwana Iman?, eh Momy nima murmushi nai nace ai Momy ta kice halak Malak mun baki ita muma mun kusa haifar namu..inagama gayamata nan ma naje gun Kakus na gayamata abinda nacewa Momy akan Aman.....shi albarka kamar sa tsuguna suma na godiya Momy harda kuka tace dama inada rabon riqe 'ya mace a rayuwa ta baby Auwab nagode Allah yabiyaku da alkhairin sa. ..Ameen muka ce kana muka fice.
Daga nan gidan MAMA mukai itama haka...su Sameer tsalle Dady murna yanda su Momy sukai murna Mama tayi ta mafi tata dan ita k'asa godiya ma tayi...
Dake dare ne bamu jima ba muka fita..a mota Auwab kansa murna yake baizata haka zaiga farinciki a fuskar iyayen ba godiya shima yai mun da fatan haihuwa lafiya.
********
Alhamdulillah duk abinda yai farko zaiyi k'arshe yau na wayi gari Allah ya sauke ni ya k'ara bani twinc namiji da mace wanda dani sukai kama sosai a gidan Mama na haihu saboda a jiya ne aka d'aura wa Yayu na aure tare da Adnan da Arfat wanda komai na bikin tare suke matan su gwanin sha'awa masu hankali da sanin yakamata.
Matar Adnan ne ce dai sai a slow dan tanada d'aukan kai saikace wadda tashiga familyn mitsiyata batasan gidan arziqi tazo ba.
Tun safe aka bugawa su Momy waya dan haihuwar ta tsakar dare ce da Asubah kuma ba'a sami layi kan su ba...
Baby masha Allah twinc kuma gajeriyar nak'uda namiki murna...Prince yace lokacin da yazo ganin mu.
Hmm prince muna gama waya fa dakai naji ciwo nazata na wasa ne saida naga kan baby shine fa nakira wayar Mama kafin ma tazo baby ta fito....d'ayan ne dai saida tazo....tun a daren ta dubani taga ba komai. Wait kina nufin kice Mama Doctor ce? Of course Dady ne yace baison aiki shiyasa...ayya.
Da tuni a gida zaki haihu, abinda nagama cewa kenan ansha biki kullum ina gida na Sai a jiya ne nai sha'awar kwanan gida ashe baby ne zasu zo duniya.
Wannan karan ma naga gata gun kowa dan a gun Mama na zauna. Su Momy murna sun sami twinc Ya Sameer dai ko wanka baiba yazo....ranar dai sai dare kowa yabar gidan Mama.
Dadyn Prince dashi da 'yan uwan sa wad'an da sukazo bikin suma haka sukazo Abokan Dady kam sai da 12 tayi kana suka dena zuwa.
Kullum Momy na hanya da Iman 'yar ta wadda Hausa take son b'acewa Aman ma suna zuwa da Kakus, Ayman ne dai gani a gidan su kullum yana mak'ale da yaran yakance Amma muma aka mana Baby kada Aunty baby ta tafi dasu..Ayman rufamin asiri kaima da aka ban nagode ai sai muyi hauka nikam dariya nake a raina na k'ara d'aukan alkawarin tunda tanaso nikam zan bata macen.
*********
Kwanan mu biyar kenan da haihuwa kuma a kullum baka rasa masu shigowa...Auwab kam dama anan ya tare d'akin Ya Sameer nan ya ajiye kayan sa tun kwana biyu da haihuwa wai bazai iya zama ba ni ba ku kifa babu kunya gidan surukai.
Yau manyan bak'i mukai dan amaren ne kaf sukazo Auwab kam yana mak'ale da mu anata hira.
Matar Adnan ce dai bata saka baki saboda gayu irin nata...yanzu haka Momy ce tazo duk sun gaishe ta amsawa tai da sakin fuska da matan su Ya Hadeeyatullah suma zama sukai duk hiran su sace Baby kaza...Hakan ba k'aramin bakan ta ranta yake ba....narasa wace ita daga auro ki har zata d'orawa kanta masifa.
Baby babu fa suna Auwab yafada, to prince yadda kace haka za'ayi Abban babu. Dukan wasa yakaimun yace ai wallahi kina Arba'in zaki samu ciki ki bamu namu haba yarinya duk tabi ta rabe mun yara tun kafin ma su girma...dungure mun kai yai.
Sameer ne yace wait....me nakeji?, abunda kaji ne..wai kasan me?, Iman ce tace suma asamomusu baby...ke baby daga jin haka sai kikace Iman kinaso? , yarinya tace eh kema Momy eh muna so wallahi.
Anbaku shine furucin baby... Momy saiki zab'a macen ko namijin...nagayamuku ba saiga Momy na godiya ba harda cewa batada kamar baby a duniya a gabana Momy ta dauki Adnan tabawa Mama Little Zahra kai naga takaici gashi ba halin magana nidai baby na yanda taga dama dani ya fad'a yana hararen ta...dariya suka kwashe da ita kafin Fauzan yace tab wallahi nidai ba'ayi matar da zata mun haka ba...kazama mijin tace daga bayan su sukaji ance indai Auwab ne kafin ma baby tace yayi.
Juyawa sukai Momy ce tana dariya da babyn a hannun ta tace ai baby macen arzik'i ce kafin a sami yarinya kamar ta a yanxu sai an tona. Shiyasa ita d'aya ce..Auwab Mijin mace d'aya ne..itace gudalliya tasa....babu yaji ba saki ba kishiya.
Ihu suka sanya..aikam Auwab fuska ya b'ata yace Momy..aikam karin aure dole tunda har yanxu bata haifamun yaro ba. Prince baby tace juyawa yai tace kasan me?, ai kaidai aure ko a Lahira haitata haitata haraaam....murmushi Momy tace kwarai kuwa akan baby zan iya b'atawa da kowa...nima haka Kakus tace amma ni wannan Karon ba'a ban d'a ba sai ki kabawa iyayen ku....Kakus bari a samu wani zamu baki. Ke wa zaki bawa wallahi baki isa ba..murmushi akai.
Amal ce ta taho tace Ya Adnan dan Allah nima ku haifamana mata ace duk yawan mu maza ne mata kad'an ne gaskiya muna son mace...hannun ta yakama yace My Amal wallahi nikaina inason mace muna school saidai muyi ta nuna pics naki kece qanwar mu..nima haka saidai naita cewa Maza ne...tafad'a a shagwabe murmushi yai yace karki damu ke zaki haifamana mace.
Auwab ne yace Amal tunda kinaso to sai kiyi aure ki haifama na....tab nikam aure ba yanzu ba sainayi 20 years sannan zanyi...Arfat ne yace dake kece da kanki koh?, stupid kawai tashi kinzo kinsa mu a gaba.
Aa Arfat ina ruwan ka taho nan sis Adnan ya fad'a a tausa she. ..aikam matar sa cika tayi fam itafa bazata juri wannan abin ba.
Yauwa wai d'azu naji kace Adnan da zahra sunan yaran? , eh takwara namaka dan naga matar ka ba kalar haihuwa bace...bangane ba ni nace bazan haihu ba?, nace dai yara biyu sun isheni dan bazan zauna kamar akuya ba ina haifar yara...Kuma yara na guna zasu tashi tafad'a a hasale dan taga Auwab sai wani ji dakai yakai.
Muku ma family namu mace bata zab'an abinda zata haifa...saboda haka kima cire wanann ak'idar yara goma zaki haifa, kuma ai Akuya da miji take haihuwa ke baku goma sha biyu ne a gidan ku ba....ya akai Maman ku ta haife su?.
Ido ta ware tace bangane maganar kaba?, eh bazaki gane ba yammatan Adnan a dai kula da irin maganar da za'ayi kinji yarinya haihuwa kuma goma sha biyu zakiyi kamar kumbo kamar K'oren sa kinga kunyi matching da Umman ki.
Kasa magana tayi saboda bata zata zai fuskanci abinda take nufi ba...shi kam Arfat dama matar batai masa ba dasu Fauzan dariya suka kwashe da ita..gaskiya ne Prince kaji hausa to ke kinji mu dai ...Adnan nagaji inason komawa gida hayaniya tayi yawa.
Only yini zamiyi fa wani irin kin gaji ga k'awayen ki nan..anata hira zakice zaki tafi?, a'a Sakina yada tafiya ana hira keda amarya ce gaskiya ki zauna ba inda zaki...baki ta tabe kawai kafin tace wai ke baby suruka ce ko kuwa kema yar uwa ce?
Kafin tayi magana Adnan yace only me yakawo wannan maganar?, ai baby ita ba suruka bace 'yar Momy ce nan gidan su ne Sameer..Fauzan yayun tane Adnan da Arfat kuma yayun tane suma.
Halan Ya Adnan baka gayawa Sakina wace baby ba?, hmm ko ban fad'a mata ba yanxu tasani baby itace farincikin mu...matar wani tafad'a tana zare ido. Kwarai kuwa dan zuwan ta alkhairi ne a gun mu bata shawara koda da mijin tane sai mun had'u haka muma we can't do anything batare da ita ba...matar broth.. Ina godiyan takwara Auwab Allah ya raya baby..Ameen kowa yafada banda ita.
Anyi suna sosai, wannan karan su k'aru dan da matan su akai komai yar mulki kuwa tana gefe Kakus kam tunda taga take taken ta shikenan ta fita sabgar ta..Maman Adnan kam tayi bakin cikin samun suruka kamar ta dan matan sauran masu kirki komai tare suke.
Bayan Arba'in ba gida suka koma ba, da Momy suka wuce China dan kai musu ziyara Amal kam tazama yar gidan Baby dan tare suka tafi da ita...baby kam tun can ma batai wasa ba wajen koyawa Amal girki da kwalliya dan tanada wani kudiri a ranta na son had'a zumunci.
A China sukai zaman su dan sunyi hutun school kuma ga strike da aka tafi shiyasa sukai zaman su a can tare da Momy da 'yan uwan Auwab masu kirki.

Auta ce

LAIFIN WA..?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora