TUSHIYA

248 29 2
                                    

🌳🌳🌳

    *TUSHIYA...*
       
       🌳🌳🌳
Hassanah Zakariyya Maidaru
   *Sanaah Shahada*

✏📖
          *FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*

     Page 3...

Tun daga nesa ta hango shi tsaye a kofar gida rungume da hannu, shigarshi dai data tsana ta yau da kullum yau ma ita yayi,doguwar jallabiya mai gajeran hannu kalar furanto,fuskarshi dauke da glas din da zame masa kamar gado.

   Ta yi tsaki yafi goma kafin ta karasa kofar gidan. Tana zuwa dab da shi ya daka mata tsawa cikin muryar rashin son wargi yace"Daga gidan uban wa kike yanzu?"

  Ta hado gizagon duniyar nan ta makawa fuskarta dan ya fahimci ita dinma bata son wasa kuma daidai take da duk abinda yake ji. Bata ce komai ba take kokarin gota shi ta shiga gida

"Ba tambayarki nake ba Bushira?" Yace a wannan lokacin ya dan sassauta muryarsa.

  "Daga makaranta mana!"

  Ya kalli agogon hannunshi ya dago ya kalleta yace"Kada ki raina wayona mana Bushira! Yanzun karfe biyar da rabi har da mintuna aka taso ku daga makaranta? Ko dai gantalinki kika wuce?"

  Ta yatsina fuska kana tace"To malam Ramadan tunda ka san inda na tafi ma miye na bin ba'asi? Ai yanzu hukunci ya rage maka ka yanke kawai Baba!"

  Ya daga hannu zai wanketa da mari yaji muryar Hamza yana cewa "Dan uwa kada ka soma!"

Ya sauke hannunshi ya juya ya kalleshi cikin fushi yace "Mai yasa zaka hana ni Dan uwa! Kaji rashin kunyar da yarinyar nan take min kuwa?"

   Bushira ta kallesu gaba daya tace"Kwa ji da shi wai ciwon ajali a dan yatsa" ta shige gidansu tana cewa "Wallahi tunda uwa da ubana basu dake ni ba babu katon da zai ware kwanji ya kile ni na zuba masa ido dan ni ba jaka bace,dan kuna dukan kannenku to ni ban da ni..."  suka ci karo da babanta zai fito yayi turus ya dubeta da mamaki yace "Bushira daga ina kike haka? Gaba daya kin tada hankukanmu,yanzu haka da kika ganni police station zan kai rahoto daga nan na wuce gidan redio,na je makarantar taku ance kun dade da tashi,so Ramadan ne ma suka raka ni"

  Ta yi rar-rau da idanu tace "Abba bafa bata zan yi ba a garin nan,sis Khady ce bata da lafiya shi ne na je na dubota fa"

  Ya dafa kanta cikin sigar rarrashi yace"Sorry uwata,ba wai ina nufin zaki bata bane ina tsoron yadda duniya ta lalace na,amma mai yasa ba zaki sanar a gida cewa ga wajen da zaki ba? me amfanin wayarki?"

   "Ka manta ai bama zuwa da waya school Abba"

   "Ah to...to! Haka ne fa na manta ne,yanzu shiga ciki bari na fadawa yaran dan suma hankalinsu ya kwanata"

  Ya fita ita kuma ta shiga ciki.

Zaune ta samu Mamanta dafe da tagumi hannu bib-biyu tana ganinta ta mike zunbur ta daga hannunta sama tana cewa"Allah na gode maka!"

Ta jefa jakarta kan kujera jagwab! Itama ta bita ta zauna tana cewa "Wash Allah nah!" ta fara yunkurin cire sandal da safarta.

  Maman ta zauna tana raba ido a kanta ita haushi ma ya shake mata kalmomin da zata jefeta da su dan haushi.

  "Mama Khady ce bata da lafiya shi ne na wuce gidansu na dubota,baki ga yadda jikinta yayi tsanani ba,likitoci biyu ne a kanta ma,kamar ma kada na taho na barta wallahi!"

  "Ai da kin tsaya kin kwana tunda kanwar uwarki ce!" ta fita ta bar mata falon.

   Bushira ta kishingida akan kujerar tana tunanin Boby da suka hadu yau din nan 'Yayana ko yana ina yanzu?' ta ce a zuciyarta.

  "Ga abincinki to,idan kuma kin ci a can din to"

  Ta yi murmushi tana bude flat din shinkafa ce da miya da kifi "Ina sonki mamana!" tace tana sa cokalin abincin a bakinta.

  Itama murmushi tayi tace"Nima ina sonki 'yata! Sai dai bakya la'akari da damuwarmu a kanki why?"

  Ta tashi ta dafa jinyoyinta "Nafi kowa shiga tashin hankali idan naga damuwa a fuskarku komai kankantarta,zanyi duk kokarina na hanata shiga zuciyarku."

   Ta shafa kanta tace"Na san haka Bushira!"

   4...Loading

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now