🌳🌳🌳
*TUSHIYA...*
Story life.
🌳🌳🌳By *Sanaah Shahada*
my wattpad user name @SanahShahada.
✏📖 *FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*
To you all *BIEBIE ISA GROUP*
*Zulaihat Rano, Khadija S Mohd (cittah), Marnaf, Allah ya bar zumunci*
*All MMM Group Allah ya bar mu tare ya kore mana duk wata fitina**Ban da bakin da zan ce komai, na gode matuka da gaske Momy Allah ya yi jagora ya shirya zuri'a (Aishatu S Gadanya) NA GODE!*
PAGE 9⃣~1⃣0⃣
"Ya Ahmad dan Allah ka saurare ni, ina cikin damuwa fa" in ji Bushira.
Ahmad ya kalleta kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya ce"Wai ke yanzu baki ji kunya ba? Duk duniyar nan ki rasa wanda zuciyarki zata mannewa da sunan soyayya sai Ramadan? Kada fa ki manta duk duniya idan da abinda Ramadan ya tsana bayanki zai bi"
Ta tsugunna bisa guiwoyinta ta daga hannu sama alamar roko ta ce"Na sani bros, amma ba yadda zan yi a kai ne. Zuciyata ce"
Ya jinjina kai "To wai ma taimakon me zan miki?"
Ta yi murmushi ta mike tsaye "So nake duk yadda za ka yi ka yi in shiga dakinsa"
"Me kuma za ki yi a dakinsa?" Ya tambayeta.
Ta cuno baki "Babu ruwanka da me zan yi, idan har kai dan uwa na ne ka taimaka min"
Ya rausayar da kai "Ba komai zan yi"
Ta daka tsalle ta mai kiss a gefen kumatu "Thank you so much my lovely brother" ta fita da guda.
Bin bayanta yayi da kallo sannan ya tashi ya fita yai sa a kuwa yana futowa suka hadu da Ramadan sai ya sakar masa murmushi.
Ya mika masa hannu "Barka da safiya bokan turai" Ahmad ya ce masa.
Cikin salon yanayin rayuwarsa, mutum ne mai shariya da rashin sakin fuska a koda yause, ya dube shi ya ce"Ahmad yau lecture ne?"
Ahmad ya girgiza kai ya ce"Yau ban da shiga school, am gwara ma da na hadu da kai dama bangarenku zan shiga"
"Akwai wata matsala ne?" Ramadan ya tambaye shi.
"A'a dama ba komai bane Yaya Ramadan, wannan littafin naka na chemistry nake son in duba tunda yau ba inda za ni."
Ba tare da tunanin komai ba ya laluba aljihunsa ya dauko dan mabudi ya mika masa. "Ga key din nan, ka rufe min daki idan ka gama bana son shirme ka ji ko?"
Ahmad ya jinjina kai ya ce "Ina gamawa zan rufe maka"
"Ok na tafi asibiti" Ya wuce ya bar shi a tsaye.
Da sauri Ahmad ya koma cikin gidan su ya sai suka yi kicibis da Bushira tana tsaye a soro . Ya yi dariya "Ke kam kamar mayya ki ke idan kika sa naci a abu"
Ita ma dariyar ta yi tana cewa "Na dai ji, ba ni keys kai dai"
"Ai bai bani ba cewa ya yi wai wasa zan masa a daki"
Ta bata rai "Dan Allah ka bani kada ka bata min lokaci, na ga fa lokacin da ya baka"
Ya mika mata "Kin san fa 'bangaren su daya da su Hamza, idan suka gan ki fa?"
Ta yi tsaki "Kai dai tunda ka bani shikkenan,yadda zan yi duk wannan ni na sani"
"Allah ya fidda Ai daga rogo to, mara kunya" ya shige ya barta.
Ta tsaya tana jujjuya dan mukullin tana tunanin yadda za ta dauki wannan kasadar, wajen mintuna goma sannan ta yi shahada ta fito ta nufi cikin gidan Gaadon.
Allah ya taimake ta bata hadu da kowa a hanya ba har ta shiga 'bangaren su Ramadan. Dafe kirjinta ta yi ji take kamar zuciyarta zata fito.
Da ta shiga d'akin sai ta sanya sakata ta bi kofar ta zauna.
Ta bi dakin da kallo, ba yadda za ta yi dole ta yabi tsarin sa da yadda yake kamshi, lallai mamallakinsa mai tsafta ne.
Zabura ta yi da ta tuna abinda ya kawo ta, a nitse ta bi dakin da kallo ta yarda idan ta tashi maidawa ba za a samu mishkila ba.
Bayan ta yi abinda za ta yi har ta juya za ta fita fitinanniyar zuciyarta ta zuga ta sai ta dawo ta fara bude takardun da suke kan tebur. Wata farar takarda ta fad'o zanen heart da aka mata ya ja hankalinta ta dauke ta ta bude.
"A kullum ganinka kamar ruwa ne ga shuka!" Wannan kad'ai aka rubuta a ciki ko suna babu.
Can ta sake hango wata guntuwar takarda an dora mata kwalbar turare, ta mika hannu ta dauko ta.
"Kada ki damu za ki ji daga gareni, kwanakin auren mu basu wuce ki kirga su da hannunki ba. Matata!!!"
Ita kanta bata san lokacin da tsakin ya fito ba, ba dan kada ta yaudari kanta ba da juyawa ta yi ko zata ga mamallakin tsakin, amma ta san ita ce ta fitar da shi.
"Aikin banza da wofi!" Ta ce cikin sauri kuma ta fito daga dakin.
Tana fitowa daga lungun 'bangarensu suka had'u da Ramadan saura kadan ya tureta da alama sauri ya ke ma dan sam bai ganta ba.
"Ke xo nan!"
Cak ta tsaya amma ta kasa juyowa.
"Ki ce Ahmad ya kawo min mabudin daki na"
Da gudu ta karasa cikin gidan ta shiga dakin Ahmad ta cefa masa mabudin tana cewa "Mai d'akin ya dawo ya ce ka kai masa"
Ta fita.
Shi ma a tsorace ya mike ya dauki keys din ya fita.*** *** ***
"Asma'u ni dai fa sai dai duk abinda ma zai faru ya faru, amma ni dai ina son mutumin nan"Wacce aka kira da Asma'un ta tabe baki sannan ta ce"Dama fa da ke ya dace, ai kwarya bin kwarya ta ke, mai kyau sai kyakkyawa. Kwantar da hankalinki Khady kamar kin same shi"
Suka tafa.
Bushira ce ta zo ta zauna a tsakiyarsu "A nan ku ke nake ta neman ku? Break time fa ya kusa wucewa"
Khadija ta duba agogon hannunta "Share wani time ban wayarki zan ga wani abu"
"Tun da aka turo min waqar Ra'ees din nan kin hana wayata sakat, kawai ki tura a taki ko nima na huta" Ta mika mata wayar.
"Ai ina ga abinda zan yi yanzu kenan" ta karbi wayar ta mike tsaye "Bari na koma gefe dan kada ku dame ni ma"
Gaba d'ayansu suka yi dariya.
Bayan tafiyarta Asma'u ta kalli Bushira ta ce"Ya mutumin na ki kuwa Sister?"
Bushira ta yi dariya "Ki na nufin wai yaya na Boby?"
"mtss! Ke dai kenan kullum ba ki da magana sai ta shi, to ina nufin Ramadan"
Bushira ta yi murmushi "To ai dole ina magana a kan shi, shima fa yana kula da ni. Oh ni kin tuna min ma wai yau muna da meeting a gida"
Asma'u ta girgiza kai tana tabe baki.
Ina zuwa!
YOU ARE READING
TUSHIYA...
General FictionBushira yarinyar da ta taso cikin wata bahaguwar rayuwar da ta kasa gane ganta.