TUSHIYA...

191 17 3
                                    

🌳🌳🌳
*TUSHIYA...*
*(Life story*)
🌳🌳🌳
*BY*
Hasaanah Zakariyya Maidaru *(Sanaah Shahada)*

✏📖
*FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*

*Ku yi hakuri da yanayin da labarin yake tafiya a kai, mun kusa zuwa inda ku ke jira din, amma ban da gaggawa fa lol*

Ina muku fatan alkhairi a duk inda ku ke.🙏🏼

Join me at my whttppad @SanahShahada.(Domi samun labarin daga farko)

Page 1⃣3⃣~1⃣4⃣

Alhaji ya kalli abban Bushira ya ce "Ina so ka ji kuma ka san babu abinda zai sa a fasa wannan auren sai ikon Allah"

Abba ya sunkuyar da kan shi kasa "A yi hakuri Alhaji yarinyar nan fa bata isa aure ba, amma idan ban da haka ni da ita ai duk mallakinka ne"

"Ya rage ruwanka dai, ni dai na fada nan da sati hudu za a daura mata aure"

Ita dai safiyya tana kan cinyar Yabi sai raba idanu take a tsakaninsu fata take a ranta ina ma bata ga wannan ranar ba.

An tashi daga taron Alhaji ransa a bace haka iyaye matan da tun farko Alhaji ya ce kada kowacce ta sanya masa baki a maganarsa, amma fa Allah ne ya taimaka maman Bushira bata nan ta tafi unguwarsu ta ce a kan wani taronsu ba za ta fasa zuwa gidansu ba.

Tana dawowa ko gidanta bata shiga ba (samu labarin halin da ake ciki tunda Bushira ta suma Ahmad ya kirata yana kuka ya ce ta zo za ta mutu) ta shige cikin gida ta dinga tata rashin arziki maman Ramadan din ta biye mata suka dinga yi da kyar aka raba su kowacce ta sha alwashin ba za su hada jini ba.

Bushira kwance akan cinyar mama tana kuka jiiiyar kanta har sun fito "Ko sama da 'kasa za ta hade ba zan auri wanda bana so ba mama"

Mama ta shafa kanta tana rarrashinta "Kwantar da hankalinki Bushira, daina kuka, middin ina raye babu wanda ya isa ya miki abinda ba kya so."

Ahmad ma da ya shigo fada ya dinga yi kamar wanda zai ari baki, ya ta'ba gefen wuyanta ya ji zafi rau *(Mu kula ko yaranmu ciki daya su ke bai kamata suna taba jikin juna ba matukar sun balaga dan kaucewa fadawa tarkon shaidan)* "Mama ji zazzabi ne a jikinta ko asibiti za mu tafi?" Ya ce.

Mama ta kalleta sannan ta kalle shi "Tun dazu nake fama da ita ta ki, ka san tsoron allura take, amma ta sha magani. Kamata ka kai ta d'akinta ta kwanta"

Ya sa hannu ya d'agota ya jingina a kafadarsa, wata karamar riga ce pink da dagon wando a jikinta kanta babu dankwali. Ya kai ta daki ya kwantar da ita ya ja mata bargo, ya sumbaceta a koshi yana cewa "Ke kadai ce 'yar uwata kada ki bari damuwa ta kama min ke nima zan shiga wani hali"
Ta jinjina kai idanunta a rufe ya jawo mata kofa ya fita.
Ba jimawa mama ta ji karar wayar Bushira a falo ta zo ta dauka ta shiga dakinta tana cewa "Kin bar wayarki a nan ga shi sai kira ake" ta ajiye mata wayar a gefen filonta, ai kuwa tana bada baya mai kiran ya sake dawowa.
Bushira ta laluba hannunta ta cikin bargo ta dauko wayar, ta bude idanunnta da kyar da sauri ta amsa wayar ganin wanda ya ke kiran.
"Yaya na" ta ce a hankali
Ya gyara kwanciyarsa a kan kujera "'kanwata ya ki ke?"
Ta rintse ido hawaye ya fito "Ina da damuwa yayana"
Da sauri ya tashi daga kan kujera "Damuwa? Oya fada min ko menene"
Yadda ya nuna dinnan ba karanim tasiri ya mata a zuciya ba hakan ya sa ma zuciyarta ta karye bata san lokacin da ta bare baki tana kuka ba.
"Please my sister stop crying ok? Fada min ko dan ba na taho gidanku yanzu"
Ta daga hannu tana girgiza kai kamar yana gabanta ta ce"Ba zai iyu ka zo gidanmu ba fa ka yi hakuri mu hadu gobe a hanyar school"
"Sam ba zai iyu ba! Ko dai in zo gidanku yanzu ko kuma ki zo mu hadu a gidansu Khady"
Ta yi ajiyar zuciya "Ba komai mu hadu a can din ba na fito yanzu"
"Ok take care" Ya ajiye wayar.
Ya mike ya zari mukullin motarsa dake hannun kujera ya fita.
*
Wanka ta samu ta yi har yanzu jikin nata akwai zafi ta sanya wani siket din jeans da riga 'karama, ta d'aure kanta da ribon ta dauko wani karamin mayafi ta yafa.
Tunani ta yi bata da kudi dole ta san yadda za ta yi ta karba a wajen mama.
Har daki ta samu mama tana shiga ta dago ta dubeta "Ke kuma ina za ki, ke da ba kya jin dadi? Ga kuma yamma ta yi?"
Ta xauna a gefenta da shagwaba ta ce"Gidan su Khady zan je akwai abinda zan karbo kuma zan fada mata halin da nake ciki, kin san dai duk friends dina ba ni da kamarta ko?"
"Oh ni 'yasu yau ina ganin abu! Daga tambaya kuma sai ki nemi yi min kuka? Na dazu da ki ka yi bai ishe ki ba ko dan wannan na shagwaba ne? Kin ga ki bari sai gobe idan kuka hadu a makaranta ba sai ki fada mata ba saurin me ki ke?"
Bushira ta fara dira kafafu "Ni dai yanzu zan je in fada mata wallahi! Ji nake kafin goben kamar zan mutu"
Mama ta rufe mata baki da hannayenta ranta a bace ta ce"Dena cewa za ki mutu kafin gobe in sha Allahu ba yanzu za ki mutu ba sai na ga ranar da za ki zama cikakkiyar likita sannan na aurar da ke, yanzu dai tashi ki tafi, amma dai kada ki kwana" Ta janyo jakar da ta je unguwa da ita ta dauko naira 500 ta bata "Wannan zai kai ki na sani, dawowa kam na san direbansu ne zai kawo ki"
Bushira ta karbi kudin ta sa a aljihun siket dinta sannan ta ce"Na gode mama" ta sumbace ta "luv you" ta fice tana dariya.
Ita ma mama dariyar ta ke yi "Wannan kawance na yaran nan yana bani mamaki, kamar hanta da jini ba 'a son rabuwa? Hmmm na san dole za ta kwana balle yau an samu abin tattaunawa"

*** ****
Tunda suka shigo dakin yake dafe da kai, a jima kadan ya yi tsaki idanunsa sun yi jajur saboda tsabar damuwa, sam kwakwalwarsa ta gagara bashi hadin kan lalubo wani abin mora cikin tunanin da ya ke yi. Ramadan kenan!

"Dan uwa dan Allah ka sassautawa kan ka haka mana! Kada ka ja wani ciwon ya kama ka fa" Hamza ne wanda tun dazu ya ke rarrashinsa.

Hannu Ramadan din ya daga masa alamun baya son a dame shi.

Hamza bai sake ce masa komai ba ya fita hade da jawo masa dakin ya san a irin wannan yanayin Ramadan yana da wuyar sha'ani.

Bayan fitar Hamza da mintuna ya tashi ya fito kofar gidan yana dafe bango.
Juyuwar nan da zai yi ya ga Bushira ta fito daga gidansu sanye da shigar da ya ki jinin ganin diyar musulmai da su.
Ya ja tsaki ya kau da kai.

Ita ma tana fitowa ta gan shi gabanta ya yi wata mummunar bugawa ta dan tsaya kamar ba za ta tafi ba, ta sake kallon inda ya ke sai ta ga ma ba ita ya ke kallo ba ta juya tana tsakin karfin hali dan kuwa zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito.

Bayanta ya bi da kallo "Ban san me ya rufe idanun Alhaji ba da har ya rasa wadda zai hada ni aure da ita sai wannan 'kazamar" Ya ja tsaki ya koma cikin gidan.

*To fa fans ga Ramadan da Bushira ana buga game, anya ba wata a 'kasa kuwa? Ba dai mu je gaba mu gani.*

Thanks for your prayers🙏🏼🙏🏼🙏🏼 Ina tare da ku.

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now