🥦🥦🥦
*TUSHIYA...(LIFE STORY)*
🥦🥦🥦*Shafi na 21-22* by *Sanaah Shahada*
✏📖 *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
🥦
Getsetse ta tsaya a gabansa sanye da riga da wando, ba ko sallama ta ce "Ga ni. Ina fata dai lafiya?"
Ya kalleta ya girgiza kai kana ya ce"An dai yi asarar hali wallahi! Yanzu ke duk girmanki ba ki iya sallama ba? Any way ba abinda ya kawo ni kenan ba, na zo ne akan maganar bikinmu dan haka ki nutsu ki ji ni bana son shashanci"
Ta tabe baki "Ka fada min abinda ya kawo ka malam kada ka takurawa rayuwata"
Ya dan sassauto da murya "Abinda nake so da ke Bushira ki yi hakuri mu rungumi wannan abin tunda manyanmu ne suka hada, mu yi biyayya insha Allahu za mu ga alfanun hakan ko nan gaba kin ji"'Kokarin korar abu mai kama da yarda da kalamanshi ta yi a zuciyarta, ta kalle shi sama da 'kasa kana ta ce " Ba da ni ba guda a hurumi! Na fada yanzu ma zan sake fada, baka isa na aureka ba dan ni ba matar talaka ba ce, ko mai mota ma ba kowanne zan kula ba balle kai da ka ke da mashin matsayin kafi babu. Ba zan aureka ba Ramadan koda kuwa duniya zata taru a kai na!"
"Kin manta kema a gidan talaucin kika fito Bushira? Baki san me Allah zai min nan gaba ba kila nima ya azurtani yadda ki ke tunani, zan kula da ke a hakan ba zaki muzanta ba."
Ta gyara tsayuwarta tare da jingina a jikin bango "Ni dai abinda nake so kuma nake neman alfarma a wajenka dan Allah ka ce baka So na ba zaka aure ni ba, dan Allah!"
Ya girgiza kai tare da lumshe idanu ya sosa gemunsa kana ya ce "Ba zaki fahimta ba Bushira."
"Tunda ba zan fahimta ba ka bar wahalar da kanka. Wai ma ina wadda ka ke SO? Zuciyar ka ba ni take kallo ba kada ka cuci kanka"
Ware idanunsa ya yi ya sauke su a kan fuskarta cike da mamaki a fuskarsa ya ce"Wa ya fada miki?"
Ta tabe baki "Ni dai kawai ka rabu da ni ba sai ka ji a ina na ji ba"
tana gama fadin haka ta juya ta tafi yana ta kiranta ta tsaya amma ko waigensa bata yi ba.Ya dafe kansa yana jin kamar ya fitar da hawaye dan takaicin tare da mamakin da Bushira ta masa . Ya fita daga soron gidan ya nufi cikin gida kanshi yana sarawa.
Tana shiga gida mama ta tare ta tana tambayarta ya suka yi. Ta ce "Ba komai wai ya zo maganar bikinmu waye-waye ni kuma na fada masa ba zan aure shi ba""Kin yi min daidai Bushira! Bari Abbanki ya dawo ma a yita ta 'kare" inji mama.
Bushira bata ce komai ba ta fada daki tana shiga ta kunna wayarta ta tafi kira "Bari na kira yaayana ya sauke min takaicin wannan mutumin, gashi aji garau din da Aunty ta bani ya 'kare da na afa shi, dan ni babu abinda zan bari ya dagula min tunani tunda na san ba aurensa zan yi ba"
Ya katse wayar kamar yadda ya saba ya biyo kiran.Da daga kiran da cewa "Hello"
"Ran Amarya ya dad'e" ya ce mata cikin sigar tsokana.Ta shagwaggwabe murya tana dirza 'kafafu kamar yana gabanta ta ce "Au haka ma zaka ce min ko? Shikkenan mun yi fada"
Cikin sauri ya ce "A'a dakata! Idan na yi fada da 'kanwata ina na kama na rike? Yi hakuri ba zan sake ba"
Ta yi murmushi ta kwanta kan gado "Ai kai din ne wallahi"
"Ai dai na bada hakuri."
"Na hakura, ai bana bushi da yaayana wasa nake maka"
Ya yi dariya ya ce"Yauwa har na ji dadi. Ya ake ciki ne miye labari?"
"Ba dai ka 'ki zuwa waje na ba, dan baka san yadda na matsu na ganka ba wallahi. Yanzu Ramadan ya zo wai muyi maganar aurenmu"
"To ke me kika ce masa?" Ya tambayeta.
Ta maida wayar daya barin ta ce "Na fada masa har yanzu ban ji zan iya auren shi ba"Ya yi ajiyar zuciya "Ki bi komai a hankali mana 'kanwata, yanzu dai ki bari za mu hadu sai mu tattauna, amma ki sassauta kada ki biyewa son zuciyarki ta hana ki yiwa magabatanki biyayya"
Ta yi karamin tsaki yadda ba zai ji ba kana ta ce "Haba yaayana ga mari ka tsinka jaka? Da wanne zan ji? Da auren wani" zan ji ko da rasa wanda nake so?" Ta fashe da kuka.
"Ki bari za mu yi maganar daina kukan please!"
Ya kashe wayar dan gaba daya ta rikita shi tana neman rushe masa dagiyarsa.
Ta zame wayar daga kunnenta ta ci gaba da kukanta tana rasa wasu abubuwa sabi da suka zo mata a zuciyarta yanzu 'Ko duniya zata zage ni zan aikata haka dan tsira da soyayyata' ta ce a zuciyarta kana ta tashi ta dauko jakar makarantarta ta duba tsohuwar ajiyarta tana nan.
Murmushi mai kama da na mugunta ta saki 'Dabi'ar soyayya ce ba haka na so ba!'***
"Dan Allah Boby ka tausayawa zuciyata wallahi tana bugawa da 'kaunarka wadda babu gauraye a ciki""Sai na cin amana ko? Haba Khady mai yasa za ki yiwa Bushira haka?" Boby ya ce yana kallon kwayar idanunta da ta rine saboda kukan da take yi.
Ta durkusa guiwa a kasa ta daga hannayenta alamun roko ta ce"Ba amanarta ba ce wannan, a yadda zuciyata take fada min saboda ni aka yika kuma Bushira bata maka kwata na son da nake maka, ka yarda da ni"
Ya bude motarsa kana ya kalleta yana nuna ta da mukulli "Dama na zo in miki gargadi kada ki 'kara kiran waya ta ki dameni da banzayen kalamanki na yaudara, ki sani zuciyata Bushira kadai take SO, balle ko zan SO wata ba zan yiwa Bushira irin wannan sakayyarba, da zuciya daya nake SOnta." Ya shige mota ya barta nan a tsugunne.
Ganin mai gadi da masu aikin suna kallonta yasa ta tashi ta shiga cikin gida, a falo ta samu Momy tana kallo.
"Khadija lafiya kuwa mai ya samu idanunki haka?" Ta tambayeta tana kokarin janyo hanunta kusa da ita.
Tsaki Khadija ta ja tare da kwace hannunta ta ce "Babu ruwanki da abinda ya same ni, ki rabu da ni" ta wuce daki.
Momy ta girgiza kai "Allah yasa ki gane ni uwa ce a wajenki ba matar uba ba Khadija"
Tanan nan zaune ta ga fitowarta da key din mota a hannunta , bata mata magana ba dan ta san ko ta tambayeta ba zata fada mata inda zata ba.
#Please vote and comment!
YOU ARE READING
TUSHIYA...
General FictionBushira yarinyar da ta taso cikin wata bahaguwar rayuwar da ta kasa gane ganta.