TUSHIYA...Shafi na 25-26

152 15 3
                                    

🌳🌳🌳
   *TUSHIYA...(Life story)*
      🌳🌳🌳

  By *Sanaah Shahada*

✏📖 *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

  Shafi na *25-26*

  Sukutum da guda wannan shafin naka ne Ustazu *Bamai* Allah ya biya bukatu!

  🌳
"Baba ka yi hakuri" Ramadan ya furta da 'kyar.

  Kawu Mamman ya sake wanke shi da mari "Rufe min baki a nan marar mutunci ko na yi maka baki kafi haka lalacewa, sakarai marar tunani kawai! Ka yi kyan d'an miciji wallahi!"

   Alhaji Baba ne ya daga masa hannu ya yi shiru "Ya isa haka Mamman! Ya isa"

   Su Zainab da Hasanaah su ma  kuka suke.

  Bushira kam babu wanda zai fahimci yanayin da take ciki dan saka kanta ta yi cikin guiwowinta.

   Kawu Hassan ne ya tsawatarwa su Zainab kan su yiwa mutane shiru, sannan matan da suka kama kace-na ce.
  Bayan shiru na wasu mintuna Alhaji Baba ya fara jawabi.

  "Ba ka kyauta ba Usmanu! Ka zubar mana da mutuncin ahali. Ka zubar da girmanka.

  Ba dan wadannan hotunan da kuka d'auka tare da yarinyar kafin da bayan ta samu cikin ba wallahi ba zan yarda kai zaka iya aikata haka ba. Ina ilimi da tarbiyarka Usman? Yanzu ita wannan yarinyar da ka yiwa cikin ka kyauta musu kenan? Ba ka yi tunanin y'an uwanka mata idan aka musu haka ba ko 'ya'yanka? Ba komai ka je duniya ce za..."

  Cikin sauri Ramadan ya rarrafa ya kama 'kafafun Alhaji yana kuka ya ce "Dan Allah Alhaji kada ka min baki! Kada ka barwa duniya ni ta hora ni, na tuba Alhaji ba zan 'kara ba"

   Hamza, Umar da Ahmad suma kukan suke ganin halin da Ramadan yake ciki, mutumin da basu taba ganin kwalla a idanunsa ba amma yau shi ne da kuka shabe-shabe.

  Su ma suka je wajen Alhaji. Hamza ya dafa guiwarsa ya ce"Alhaji dan Allah ka yafe masa *'kaddararsa ce* haka"

Alhaji ya jinjina kai ya ce "Wannan ba kadara ba ce son zuciya ne. Shi yasa Bahaushe ma ke cewa "Son zuciya 'bacinta" yanzu zuciyar waye bata 'baci ba a wajen nan duk a dalilin nasa son zuciyar? Ko ban waje"

  Suka juya wajen Kawu Mamman ya yi saurin kau da kai amma duk da haka sai da umar ya je ya tsugunna gabansa ya ce "Baba ka yafewa d'an Uwa! Na tabbatar maka tsautsayi ne ba halinsa bane wannan" Kawu ya dafa kansa bai ce komai ba.

   Innar Ramadan tun lokacin da taga hoton take kuka balle yanzu da ta ga halin da danta yake ciki dan ba damar ta yi magana da ta shaidi d'anta itama ta ce ba halinsa bane.

  "Mahaifin yarinyar ya ce ya dauke ta za su koma wani gari, idan ta haihu za a kawo abinda ta haifa" Inji Alhaji.

  Ramadan ya d'aga ido ya kalle shi, yana son cewa wani abu amma bakinsa ya ki buduwa sai ya sunkuyar da kansa yana share hawaye da bayan hannunsa. A zuciyarsa bai bar maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ba.

  Maman Bushira ta ta'be baki ta ce "Ai dole su kawo abinda aka haifa ai dama ance wanda ya ci ladan kuturu ai dole yai masa aski. Da an saka min 'ya a baki ana ganin kamar itace lalatacciya ashe zaton wuta ake a makera, yo dama duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba ai tasa ko d'umi ba zata yi ba."

  Abban Bushira ne ya daka mata tsawa ya ce"Ki rufe min bakinki a nan ko na saba miki"

   Kamar za ta yi shirun kuma sai ta ce "Zan yi shiru amma bayan na ji makomar 'kaddararren auren da ake neman likawa 'yata. Ina fata an warware shi?"

   "Aure yana nan ba fashi!" Alhaji ya ce.

  Gaba daya suka kalli Alhaji Safiyya ta juya ta kalli Bushira ta ga razana a fuskarta. Da hannu ta mata alama ta yi hakuri kawai ta barwa Allah komai.

   Maman Bushira ta mike tsaye tana cewa "To kuwa ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa! Aure da mazinaci? Wallahi ba 'yata ba" Ta kamo Bushira ta mi'kar da ita tana share mata hawaye.

   Innar Ramadan ce ta sha gabanta tana cewa "Wa ye mazinacin? Ramadan ba mazinaci bane, kuma nima ba zan yarda ya auri 'yar mace ba marar tarbiyya"

  "Ai kwa dai ga 'karshen rashin tarbiyya nan a wajen d'an namiji." Ta ja hannun 'yarta tana cewa "Zo mu tafi na ga wanda zai daura wannan auren muddin ina raye"

   Alhaji ya dafe 'kirjinsa ya fara tari har da jini sai ya koma luww ya kwanta idanunsa suka rufe.

   Safiyya ta yi kansa da gudu tana jijjiga shi tana kuka gaba daya jama'ar falon suka yi kansa.

   Ta cakumo wuyan rigar Ramadan tana cewa "Yaaya ka tashe shi dan Allah kada ya mutu. Alhaji shi ne uwa da uba na idan ya mutu wa zai kula da ni irin sa? Yaaya ka duba shi"

   Gaba d'aya ta rikice ta rikita shi ya rasa ma abinda ya kamata ya fara yi.

  "Umar tashi ka yi gudu ka nemo taxi a kai shi asibiti." Inji Abban Bushira.

   Kafin Umar ya dawo Ramadan ya yi masa 'yan dabaru irin nasu na likitoci amma bai farka ba. Safiyya addu'a take ta tofa mishi har Umar ya dawo aka kama shi aka fita da shi.

   Safiyya ta kafa murfin motar zata shiga ta bisu.

Ramadan ya ce mata "Koma gida mu ma yanzu za mu dawo"

  Ramadan, Kawu Hussain da Abban Bushira ne suka tafi tare da Alhaji.

  Gidan sai ya dawo kamar gidan mutuwa kowa jikinsa ya yi sanyi, Allah ya so Yaabi bata nan ta tafi gaisuwa 'kauyensu 'yar 'kanwarta ce ta rasu.

  ****
"Wai me yasa duk gidan nan ni aka tsana mama? Mai yasa ba za a aurawa Ramadan wata yarinyar ba tunda akwai a gidan, dole sai ni? Ni ba shi nake so ba kuma ba zan aure shi ba" ta karasa maganar tata da kuka ta kifo akan kafadar mama.

  Mama ta fara rarrashinta tana buga bayanta "Ki kwantar da hankalinki Ramadan dai ba wani ba, ba za ki aure shi ba ai idan sun san wata basu san wata ba. Boby za ki aura tunda shi ranki yake so"

  Ta dako da murna ta ce "Allah mama?"

   "Wannan tabbas ne ke dai ki bar daga hankalinki kin ji? Ki ce masa ma ya turo iyayensa zuwa gobe"

   Ta saki Mama ta daka tsalle ta 'kara "Allah na gode maka! Ai kuwa zan fada masa yanzu ma kuwa. Na gode Mama! Ta manna mata kiss a kumatu ta ruga dakinta da gudu"

  "Wai 'kanwata da gaske ki ke ko wasa?"

  "Wallahi da gaske Yaayana. Shi yasa ma na ce ba zan fad'a maka a waya ba sai gani ga ka"

  Ya yi murmushin jin dadi "To ya maganar Ramadan kuma? Fasawa aka yi ko ke kika tirje aka sakar miki?"

  Ta 'bata fuska "Za ka 'bata min farin ciki na haka kawai, ina ruwanka da wani tunda kai dai ka yi winning ai shikkenan"

   Boby ya yi dariyar da yake matukar birgeta da ita ya ce"Na daina Beby! Bari na kai ki gida na je na fada a gida an ce da zafi-zafi ake bugun karfe."
Ta yi dariya.
Har kofar gida ya kai ta.
Ta kama murfin motar zata fita ya ce "'kanwata ba ki ji ba"
  Ta dawo da hankalinta gare shi ba tare da ta ce komai ba ta zuba masa idanu.
  "INA SON KI!"
Ta yi murmushi tare da juya idanu ta ce "INA SON YAAYANA!" Ta bude kofar ta fita tana dariya tana daga masa hannu har ya fita daga layin.
  Juyowar da zata yi ta ga Ramadan a bayanta rungume da hannu. Gabanta ya fad'i ta sunkuyar da kai ta bi gefen shi ta zata wuce.
  "Ina son ki!" Kamar haka ta ji ya fad'a a hankali da sauri ta kalle shi ta ga ko waya yake ko ma dai ya haukace ne.
  Bata alamun ko daya ba sai ba kafe ta da idanu da yayi.
  Kunyarsa wadda bata taba ji ba ta rikito mata, ta ce "Ka yi hakuri yaya"
  Bai nuna alamun ya ji abinda tace ba ya tafi ya barta a tsaye a wajen sai da taga ya shige gida itama ta juya ta nufi nasu gidan da wani sabon tunani a zuciyarta.
  #

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now