TUSHIYA...Shafi na 19-20

192 22 10
                                    

🌳🌳🌳
   *TUSHIYA...(Life story)*
      🌳🌳🌳

  By *Sanaah Shahada*

✏📖 *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*Ina yabawa da yabawarku fatan za a min afuwar jinkirin zuwan wannan page.*

  Shafi na *19-20*

  🌳
Mama tana bayan gida ta ji karaf! An bude kofar aka maida da karfi aka rufe, sallama take tsammanin ji har ta fara fad'a a zuciyarta 'ko wanne d'an iska ne yake neman karya mana kofar gidan?' Har ta fito tana ta fada a zuciyarta ta duba soro bata ga kowa ba sai ta nufi bakin randar robarsu zata ajiye buta ta ji sallamar Umar.

   "Ina yini mama" Ya gaida ta had'e da tsugunnawa.

   Babu yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar.

   "Ashe ka dawo, ya Gumel din?" Ta tambaye shi.

   "Eh mun samu hutun semester ne. Mama mai ya samu Bushira na ga ta shigo gida cikin wani yanayi?" Ya tambayeta.

   "Bushira kuma? Ai bata dawo daga makaranta ba"

  Ya girgiza kai "Yanzu na ga shigowarta gaskiya dai ba lafiya ba, har ture ni fa ta yi amma bata ganni ba"

   Ai bata 'karasa jin maganar ba ta saki butar ta yi d'akin Bushira tana 'kwala mata kira.

  A kwance ta sameta yadda ta saba kwanciyarta rub da ciki. Ta tsaya a kanta tana kiranta ko motsi bata yi ba.

  Ta sa hannu ta birkito ta ta ga barci take yi sosai. Ta dinga girgiza ta, da kyar ta babbare idonta ta bud'e cikin wata murya mai kama da rad'a ta ce "Yaa aka yiii maaama?

    "Me yake damunki ne Bushira? " Mama ta tambayeta.

    Wata sabuwar muryar ta sake arowa daban da waccan ta ce "Hajiii-jiya maa-ma" Ta kai karshen maganar da kufcewa daga hannun maman ta kwanta a kan katifar.

   Kasa'ke mama ta yi da damuwa a fuskarta ta fita.

   Umar har yanzu yana tsaye yana dannawa waya ta fito.

  "Ashe hajijiya ce ta kama ta Umar. Taimaka ka samo mata goriba a gidan Sabuwa mana"

   Ya yamutsa fuska "Ai layin gidan Mati mijin Nene? Tab! Warin layin amai zai sanya ni wallahi!"

  "Kenan ba zaka je ba?"

  Ya girgiza kai "Ba haka bane, bari na kira miki su Hasana su siyo miki" Yana gama fadin haka ya fita.

   "Ai dama na san ban isa na aikeka ba d'an iska mara kunya" Mama ta fad'a tana komawa d'akin Bushira.

   ***
Safiyya ce zaune tana karatun alkur'ani. Tana gamawa ta d'aga hannunta sama tana cewa "Ya Allah kai ne Allah, ni baiwarka ce mai rauni. Allah na karbi jarrabawa ta da hannu biyu Allah ka bani ikon cinyewa. Allah ka saukaka min abinda nake ji a 'kirjina, kai kad'ai zan kaiwa kuka na Allah." Ta rufe da salatin annabi.

  Tana ajiye Alkur'anin a gefenta Ramadan ya shigo cikin shigar aiki.

   Ta gefe ya kalleta ya ce"Ina Yaabi ta je?"

  Kanta yana 'kasa tana kokawa da abinda yake tasowa daga 'kasan zuciyarta. Kafin ta daidaita nutsuwarta ta ji ya daka mata tsawa.

  "Ba magana nake miki ba!"

  "Ta shiga wajen Alhaji Baba" ta amsa.

  Ya yi tsaki "Ke dai sokuwa ce wallahi! Idan ta fito ga magungunta ki bata" Ya ajiye bakar leda a gabanta.

  Ya juya zai fita ta daure ta yaki zuciyarta ta ce "Yaya dan Allah ka biya min karatu na zan bada hadda yau"

   Ya juyo a hankali ya zuba mata idanu, itama shi take kallo tsawan sakankuna ta sakaye ta janye idanunta.

  "Ina ne?" Ya tambayeta.

"Shafin farko na suratun Ahzab" Kamar mai rada ta amsa.

   Ya kalli agogon hannunsa kana ya maida dubansa kanta "Aya nawa to?"

   'Jarababbe' tace a zuciyarta. A fili kuma ta ce "Shafi nake badawa"

  Bai ce komai ba ya fara biya mata.

   Alkur'anin gefenta ta dauka da sauri ta bude bata ma san wacce sura ta bude ba. Ta fara sauraronsa.

  Muryarsa ba karamin dadi take mata ba ba yama idan yana karatu cikin kira'ar Mahir yana burgeta sosai.

  Sai da ya biya mata sau uku kafin ya dakata ya kalleta ya ce"Ya isa ko?"

   Ta d'aga kai "Na gode yaya"

  Bai ce komai ba ya nuna mata ledar da ya ajiye a gefen kujera tun shigiwarsa "Ga magunguna nan ki bawa Yaabi idan ta fito, na rubuta mata yadda zata sha su"

   Kafin ta ce wani abu ya juya zai fita.

   "Yaya ka siyo mana kayan makarantar islamiyyar? Nawa sai yagewa suke yi "

    Ya juyo ya kalleta ya saki 'karamin tsaki "Na manta amma idan na dawo zan taho muku da shi"

   "A dawo lafiya" ta ce
Bai amsa ba amma ya daga mata hannu ya fice.

    Sunkuyar da kanta ta yi bata san dalili ba ta ji hawaye yana kwaranyo mata, can 'kasan zuciyarta yana mata wani irin bugu.

   ***
"Safiya ina kuma za ki kike saka hijabi?" Yaabi ta tambayeta.

   "Zan shiga gidan kawu ne wajen Bushira, tun ranar da aka sanya auren su ban shiga ba ita kuwa kin san ba zata shigo ba"

  Yaabi ta ta'be baki kana ta ce "Ita ta sani wannan kuma aure dai ba fashi sai an yi"

   Safiyya ta yi dariya "Ke da zaki rarrasheta ba kya ce haka ba"  ta sanya takalmanta "sai na dawo Yaabi"

   Yadda ta yi tunani haka ta sameta kwance kan katifa

     Ta d'an dake ta tana zama "Wash Allah! Amarya har barcin dadi ki ke ne?"

    Ta mata banza.

"Na san fa ba barci ki ke ba Bushira, gwara ki tashi" Safiyya ta ce mata.

   "Kin zo ki tayani ba'kin ciki ne ko dan ki tuna min na kusa zama amaryar wancan banzan?" Bushira ta fad'a tana juyowa hade da kokarin tashi "Idan akwai abinda na tsani ji a wannan duniyar yanzu wallahi yabi bayan maganar nan" sai hawaye shar-shar.

   Safiyya ta dafa ta cikin sigar rarashi ta ce mata "Dan Allah ki kwantar da hankalinki Bushira ki rungumi kaddarar ki, ba komai kake so kake samu ba abubuwa suna zuwar mana sabanin tunaninmu, na san baki taba tunanin hakan zata faru ba, amma cikin ikon Allah ga abinda zai faru"

    Bushira ta ture mata hannu daga kafad'arta "Babu ruwan wata 'kaddara a nan kawai son zuciya ne irin na Alhaji da rashin son farin ciki na saboda ya tsane ni"

  Safiyya ta girgiza kai tana maida hannunta kan kafadar tata "Kin manta Allah (S.W.T) ya fad'a a wurare daban-daban a cikin alkur'ani kan cewa zai jarrabe mu da abubuwa daban-daban ta hanya mabam-banta a rayuwarmu kuma ma yana daga cikin cikar imani yadda da kaddara mai kyau da maras kyau idan ta same mu.
   Allah ya fada ba kowanne mutum yake jarraba ba sai manya a cikinmu. Ta hanyar yadda da kaddara za ki samu kankarar zunubanki. Kuma a duk inda..."

   "Da Allah malama dakata! Wallahi ba zaki zo ki cika ni da wa'azinki ba, ki barni na ji da abinda yake kona zuciyata yanzu haka."

   Murmushin ya'ke Safiyya ta yi kana ta mike tsaye ta ce"Tunda haka ki ka ce ni zan tafi, amma ba zan fasa ce miki ki nutsu kada ki cutar da rayuwarki ba"

    Bushira ta daga mata hannu ta ce"Eh to na ji jeki malama!"
   
   Haka suka rabu baram-baram kowa rai a bace.

  ***
    Da daddare Ramadan ya shirya domin fara zuwa wajen Bushira saboda lokaci kara kusantowa yake, ya kamata su yi mai iyuwa.

    Hasaanah ya tura bayan ya shirya yace ta je ta fad'awa Bushira yana 'kofar gida ta fito.

    Da Hasaanah ta fad'a mata sakon ji ta yi kamar ta shake ta,sai dai take wani tunani ya ziyarce sai ta saki murmushi ta ce mata ta je ga ta nan zuwa.

  "Mama zan fita Ramadan yana kira na" Bushira ta leka d'aki tana fad'a mata.

   Daga ciki mama ta ce"Wacce uwar zai baki da yake kiranki?"

   "Kada ki damu, kedai bari na dawo" ta yi hanyar waje tana murza murmushi da ban san dalilinsa ba a lebanta.

 TUSHIYA...Where stories live. Discover now