🌳🌳🌳
TUSHIYA... *(Life story)*
🌳🌳🌳By
Hasanaah Zakariyya Maidaru *(Sanaah Shahada)*✏📖 *FIKHRAH WRITERS ASSOCIATION*
Page 7-8
Tagumi hannu bi-biyu ta yi ta zubawa Bushira da ke ta dariyarta cikin waya, da alamun babu abinda ya dameta.
"Ya kamata fa ki saki ranki kada ki je ki kona rayuwarki a kan wata aba soyayya Safiyya, ke da alama ma ko tunanin jarrabawar da take tunkaro ki bakya yi" Bushira ta ce bayan ta katse wayar.
Da kyar Safiyya ta kakalo yaken da ta cefeta da shi kokarinta na nuna kulawa, kana ta ce "Babu abinda yake iyuwa matukar aka zare nutsuwa,koda ma an yi to kuwa sakamakon ma ba zai yi armashi ba."
"Kina nufin akan wannan matsalar za ki nunawa jarrabawarki ko in kula? Kada fa ki manta da burin mahaifinki a kan karatunki, likita babba yake son ki zama kafin ya miki aure"
"Ba na jin wannan dadddan burin na Abbana zai cika, koda ma soyayya bata masa mahangurba ba." Safiyya ta ce.
"To wai ma wa kike so ne?" Bushira ta tambayeta.
"Wani bawan Allah ne"
"Mu kuma sauran bayin uban waye? Kin ga idan ba zaki fada min ba ki rabu da ni!"
Dariya ce ta kufce mata, ta dafa kafadarta ta ce"To al masifatu! Kuma bayin Allah ne to. Ba zan iya fada miki waye ba a yanzu, amma dai kin san shi, yanzu ba ni shawara ya zanyi? In fad'a masa?"
Bushira ta yi tsaki ta janyo wayarta cikin sauri Safiyya ta dafe mata hannu "Dan Allah kada ki d'auki wayar nan ki saurare ni ko zan ji sanyi"
"To ai gwara na bude chat dina da jin wannan nonsense din wallahi!! Ashe ma guy din bai san da zamanki ba"
Safiyya ta zaro idanu waje kamar wadda aka zagarwa uwa ta ce"Bushira har chat kike? Kina s.s.2?"
"To mi ye? Haramun ne?"
"A'a ba haramun ba ne, amma dai su Abba bai sani ba ko?"
"Idan ya sani sai me? Waya ma zai sauya min muna shiga S S 3, dalla malama ki waye, har yanzu kanki na tukunya yasin"
Safiyya ta yi ajiyar zuciya "Ki kula da duniya dai yar uwa! Bari na koma gida, amma dan Allah ki taya ni addu'a kinji!"
Suka mike a kusan tare. Bushira ta janyo wani karamin mayafi ta yafa "Mu je dama na dade ban shiga cikin gida ba"
Safiyya ta kalleta "Amma dai da sauya wannan shigar kika yi ko ki saka babban Hijabi"
"Babu wani hijabi da zan saka kuma a haka zan je"
Bata ce mata komai ba suka fito, Safiyya ta yi sallama da Mama ta ce anjima da daddare zata shigo.
*** *** ***
'Bangaren Alhaji Babba suka nufa Bushira bata gaida kowa ba a gidan, haka ta kad'a kai ta yi wucewarta.
Alhaji yana zaune a kan darduma ta karasa wajensa ta ce "Sannu Alhaji"Ya kawo mata duka da sandar hannunsa "Anki a yi sannu! Mutuniyar kawai! Ba na ce kada ki kara zuwar min da wannan shigar kafiran ba? Ki kiyaye ni Hansatu"
Bushira ta cuno baki gaba jin ya kirata da sunan da tafi tsana wai Hansatu! ta fara gunguni "Kai dama wallahi sai takurawa mutum, ka cinye rayuwarka kana neman shiga ta wasu"
"Bude baki ki zage ni kawai mara kunya!"
"Ni ba zaginka zan yi ba ai" ta ce rai a 'bace.
"Ai gunguni rabin zagi ne, zan yi maganinki ne aurar da ke za a mu huta"
Ita da Safiyya suka kalle shi a tsorace.
"Tab di jan!" Bushira ta ce tana wurga masa harara.
"Aure kuma Alhaji!" Safiyya ta tambaye shi.
"Eh shi! Ko bata isa ba?"
Safiyya ta girgiza kai.
Yabi ce ta shigo tana cewa "Da alama yau mutumiyarka ta shigo Alhaji, kai ko gajiya baka yi da halinta, inda sabo ai an saba"
"Gajiyar da na yi da halin nata yasa zan sauke alkawarin da na daukarwa kai na ko mu ma ma huta".
Yabi ta zauna cikin sanyin jiki ta ce"Ba yanzu ya kamata a taso da maganar nan ba Alhaji"
Bushira ta mike ita ko kadan bata dauki maganar da gaske ba, ta zira eye piece dinta ta kalli Alhaji ta ce"In Allah ya yarda ba zan kara zuwa gidanka ba sai ka neme ni, kuma ka nemi wadda zaka aurar ba dai ni ba."
Yabi ta kamo hannunta "Ke dai ba za ki sauya ba takwara. Zo ki zauna kusa da ni"
"Barni na tafi gidanmu tunda baya son gani na, kullum idan na zo sai ya min fad'a kamar ni na kawo laifi duniya" ta fara hawaye.
"Rabu da ita Hansatu!" Ya kalli Bushira "Ki fi ruwa tafiya dan Allah, kuma baban naki zai zo ya same ni."
Ta kunna wa'ka a wayarta ta fita tana share hawaye.
Ba zato ba tsammani ta ji ta yi karo da wani da sauri ta d'aga kanta ta ga wanene.
'Ramadan!' Ta ce a zuciyarta.Ta bud'e baki zata yi magana ya wanke ta mari "Ke wacce irin dabba ce! Tun da na shigo soron nan nake cewa ki matsa, amma dan tsabar iskanci kin toshe kunnuwa ba kya jin mutane."
Marin da ya mata shi ya sa kunnen eye piece din d'aya ya fita wannan yasa ta ji abinda ya ce sosai.
Ta dafe gun da hannu hawayenta ya karu ta bud'e baki zata yi magana ya kara mata wani.
"Kina bude min wannan bakin rashin kunyar wallahi sai na bab-ballaki in zubar da banza!"
Ya shigewarsa ciki ya barta tsaye dafe da kunci.
Ta bi bayansa da kallo ta jinjina kai ta goge hawayen ta saki wani murmushi kamar ba marinta yayi ba.
'Mu je zuwa' ta ce a zuciyarta ta murza ''yan yatsunta.
"Ya na ga fuskarki ta kumbura Bushira, me ya same ki har idonunki ma sun yi ja?" Mama ce take tambayarta daga shigarta gida.
Bushira ta shafa fusksr tata kamar tana son jin me ya sameta din, ta yi murmushi da gefen kumatu ta lumshe ido.
Mama ta yi saroro tana kallonta da ta gaji da jiran amsar da bata ga alamun fitowarta ba, sai ta ce"Tambayarki fa nake kin min shiru kina murmushi"
Har yanzu da murmushin a fuskarta ta ce"Dan ki tabbatar bani da damuwa ne mama, yanayin sanyi ne tun safe na tashi fuskata a kumbure baki kula bane."
Mama ta janyota ta rungumeta tana cewa"Bana son damuwarki ne sam!"
Next page loading...
YOU ARE READING
TUSHIYA...
General FictionBushira yarinyar da ta taso cikin wata bahaguwar rayuwar da ta kasa gane ganta.