🥦🥦🥦
*TUSHIYA...(LIFE STORY)*
🥦🥦🥦*Shafi na 23-24* by *Sanaah Shahada*
✏📖 *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
🥦
"Alhaji ya shagwaba yarinyar nan dan kawai yana tausayinta kan rashin uwa, idan kuma ba a yi da gaske ba zata lalace yana kallo" Ta tashi ta shiga kitchen jin abincin da ta dora kamar yana kama wuta (mai aiki bata dafa mata abincin mijinta kamar yadda bata gyara mata dakin mijinta)***
Gudu sosai take yi ikon Allah ne kawai ya kai ta unguwar su Asma'u. Tun kafin ta yi parking ta dauko waya ta kirata, sau uku tana katsewa bata daga ba ta daki sikiyari da hannunta "Oh my God!" Ta ce kana ta sake kira, sai da ta kusa katsewa aka daga.
Kafin ta ce wani abu Khadija ta katse ta da cewa "Haba Asma'u ina kikaje kika bar waya tana ring?"Murya 'kasa-'kasa Asma'u ta amsa "Kin san fa Ummata bata san ina da waya ba, dole sai ina kiyayewa, yanzu ma bandaki na shiga na amsa. Ya aka yi?"
Khadija ta yi tsaki "Ina cikin damuwa yanzu haka ma ina kofar gidanku ki fito, kuma ma ya kamata na sauya miki waya na ga screen din wannan ya fashe."
Ba dan tana tsoron Ummanta ba da ihu zata saka ta daka tsalle, cikin murna ta ce "Ga ni nan fitowa yau damuwarki zata zo 'karshe na san ko akan waye, ga ni nan dai"
Fitowa ta yi daga bandakin tana wanke kafafunta da sauran ruwan butar, kamar da gaske wani abu ta yi a bandakin, ta kalli ummata da take gyara zobon da take yi na siyarwa ta ce "Umma bari in shiga gidan Aunty Ummi tun dazu ta aiko na zo na manta sai yanzun a bandaki na tuno"
Umma ta d'ago ta ce "Ki gaida ta ki ce ina mata sannu.
Khadija tana ganin fitowarta itama ta fito daga motar suka tsaya.
Ta kalli Asma'u da raunin da ya mamaye muryarta tun dazu ta ce "Yau Boby ya min wulakanci marar misaltuwa Asma'u, sai dai duk da haka zuciyata ko girgiza ba tayi ba akan soyayyarsa, zan iya yin komai a kanshi, zan shata layi da kowa a kan shi, ba zan iya barwa Bushira shi ba. Ki taimakeni. Ya zan yi?"
Asma'u ta dafa kafad'arta "Ba kin ce Aunty Babba ta ce ki nemeta ba? Ya kuka yi da ita?""A da dai na yanke shawarar shareta amma yanzu dole zan nemeta, taho mu tafi gidanta kawai"
Asma'u sam bata yi tunanin komai ba ta shiga mota suka tafi.
***
A falon Aunty Babba suka sameta zaune da wani saurayi wanda ya kafe Asma'u da ido duk motsin da zata yi sai sun had'a idanu, sai ta ji tana nadamar zuwanta gidan.Auntyn ta kalli saurayin kamar ta san shi ne damuwar Asma'u ta ce "Oya my Boy tashi ka tafi ka barmu da baki na" Ta dawo da dubanta gare su "He is my first and only. Sunan shi Saloman."
Ya tashi ya fita yana jifan Asma'u da murmushin da taji kamar ta kashe kanta dan takaicinsa.
Bayan fitarshi suka mata bayanin abinda ya faru. Ta yi dariya hade da tafa hannu ta ce "Hey oh god! Boby wannan ya ta'bo wuta, zan kai ku wajen wani malami irin na addini naku yana share kukan duk wata damuwa." Ta mike tsaye "Yanzu bari na 'kara baki maganin damuwan da take zama a zuciyanki, za ki daina jin komai idan kika sha maganin nan" ta shiga wani daki da yake fuskantarsu.
Asma'u ta kalli Khady ta ce "Khady anya kuwa ba za mu bar matar nan ba kuwa? Ni dai jikina yana bani kamar akwai matsala "
Khady da idonta ya rufe wajen neman mafita a damuwarta ta 'karfafa mata guiwa da cewa "Ba haka bane Asma'u, matar nan fa taimakonmu zata yi, ni jikina ya bani warakar damuwata ce ita"
Shigowarta ne ya katse musu maganar ta mikowa Khadija makamantan magungunan da ta bata a baya.
Suka tashi za su tafi suna mata godiya ta ce zata musu bayanin duk yadda suka yi da malamin.***
Yau taro ake a *Gidan gaado* saboda bikin su Bushira ya kusa.Da kyar Abbanta ya lallabata ita da ummanta suka yarda suka je wajen taron.
Bayan an bude taro da addu'a Alhaji Baba ya kalli Ramadan bayan ya yi gyaran murya ya ce "Ramadan wannan taron akan ku aka tara shi, kana sane da bikinku saura kwana takwas ko?"
Ramadan ya gyad'a kai, alamun yana sane
"Yauwa Alhamdulillah. Wanne shirye-shirye ka ke yi?" Alhaji Baba ya tambaye shi."Na had'a lefe akwati uku suna wajen Baba, sadaki kuma Baban ne zai bada"
Alhaji Baba ya yi dan yi tari kana ya ce "Wajen zama fa? Ko a nan zaka zauna?"
Ramadan ya girgiza kai "Ina da fili amma yanzu zan zauna a gidan haya kafin daga baya na gine gidan"
Ban da harara da tsaki babu abinda Bushira da ummanta su ke.
Umman Bushira ta yi caraf ta ce "Wai wa za a aura masa da lefe kwati uku a gidan haya? Ina fata dai ba 'yata ba dan ba wani ya haifa min ita ba."
Alhaji ya daga mata hannu "Ba dake nake magana ba! Ina magana da 'ya'ya da jikokina ne, ban zo kan ki ba tukunna"
Bushira ta mike zata fice wani saurayi ya shigo yana cewa wai ana sallama da Alhaji a waje wani mutum.
"Ka je ka ce yana uziri ko waye ya dawo anjima ko gobe, ka ji Sule?" Inji Kawu Mamman.
Saurayin da aka kira da Sule ya koma ya fadi sakon, ba dadewa sai ga shi ya dawo "Mutumin ya ce dan Allah Alhaji ya je ba zai dade ba wai kuma a kan hanya yake"
Kawu Mamman ya bude baki zai yi magana Alhaji ya daga masa hannu .
"Jeka ka ce ina zuwa"Alhaji yana fita ba dadewa Bushira ta bi bayansa.
Ganin fitarta aka fara 'kus-'kus a falon.
Ana cikin haka sai ga Bushira ta dawo da gudu tana kuka tana nuna kofar gida.
Gaba dayansu suka mike suna tambayarta menene.
Ta kasa magana kuka kurum take tana nuna 'kofa.
Safiyya ta kamata tana girgiza ta "Bushira menene? Ki nutsu ki fada mana mana" Itama kuka take.
"Alhaji Baba ya fadi a waje" Bushira ta fada tana nuna kofa.
Mata da maza gaba daya suka yi waje kowa hankalinsa a tashe.
Yashe suka ga Alhaji a soro da leda a hannu.
Mazan suka dauko shi zuwa falo shi kuma Ramadan ya fara kokarin ceto rayuwarsa.Tsawon mintuna talatin da bakwai Alhaji yana cikin suma har Ramadan ya fara cewa a dauke shi su tafi asibiti sai kawai Alhaji ya ja dogon numfashi tare da bude idanu yana rarrabashi a tsakaninsu kamar yau ya fara ganinsu.
Ya yi alama a daga shi Ramadan ya nufi daga shi Alhaji ya masa nuni da ya dakata, gaba daya suka kalli juna da alamar tambaya. Shi kuma ya yi sabalo yana kallon Alhajin.
Kawu Hassan ya daga shi.
Alhaji ya mikawa Ramadan ledar da ya riketa tam a hannunsa."Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ramadan yake maimaitawa tare da zama dabas! Hotunan suka watse a 'kasa.
"Me mu ke gani haka? Ramadan menene wannan?" Babansa ya ce tare da masa mari irin barin makauniyar nan har sai da hawaye ya fito daga jajayen idanunshi.
Safiyya ta sunkuyar da kai hawaye na ta kwaranyo mata. Bata fatan ta sake hada ido da mummunan hoton da take gani a gabanta.
' *Dama ace mummunan mafarki take*'#Comment#
YOU ARE READING
TUSHIYA...
General FictionBushira yarinyar da ta taso cikin wata bahaguwar rayuwar da ta kasa gane ganta.