*🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
*Gabatarwa:-* Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW) tare da AlayenSa.
Kamar yanda na fara wannan littafin da IzininSa, ina fatan kammalashi da amincewarSa (Allah maɗaukakin sarki)*GARGAƊI:-* Wannan labarin ƙirƙirrarre ne ba da gaske ba ne. Dan haka ban yarda wani ko wata su juya min labari ta ko wace siga ba. Duk wanda ya cire sunana ko ya ƙara wani abu ba da izinina ba *ALLAH YA ISA BAN YAFE BA.* Dan haka a kiyaye.
*GODIYA:-* Bayan na miƙa godiya ga Allah maɗaukakin sarki, dole na miƙa godiyata ga ƙungiyar *NAGARTA WRITERS* saboda sun cancanci yabo da godiya. Allah Ya saka masu da alkhairi a kan namijin ƙoƙarinsu.
*JINJINA:-* Dole na miƙa saƙon jinjina ga ƙawayen albarka *RAZ (Rabiatu sk msh and Zarah bb)* Allah ya bar zumunci ya ƙara mana haɗin kai.
*SAƘON GAISUWA:-* Ina gaishe da masoyana maza da mata, wanda na sani da wanda ban sani ba. Ku sani cewa Amrah mai ƙaunar duk wani masoyanta ne wanda ta sani da wanda bata sani ba. Fatana a kullum shi ne Allah Ya ƙara mana son junanmu.
*ALBISHIRINKU:-* Ina mai maku albishir da cewa gani tafe da wannnan littafi mai ƙunshe da soyayya da ban tausayi, kamar yanda masoyana suke yawan cewa bana masu littafin soyayya to yau gashi nan ina fatan zaku faɗakartu kuma zaku amfana da duk abin da zaku karanta a ciki.
0⃣1⃣
_Ranar talata, karfe 4:25 na yamma._
Sanye take cikin zureriyar hijabi ruwan ƙasa mai hannu. Hannunta wanda ta fiddo wajen hijabin riƙe yake da wata makimanciyar jaka, a ɗayan hannun kuma wayarta ce ƙirar Samsung S7 edge.
A hankali cike da natsuwa take taku har ta isa bakin gate ɗin Islamiyar tasu.
Ɗalibai ne ke shiga manya da yara, maza da mata.
Ɗaga kanta ta yi a dai-dai saman gate ɗin ta kalli rubutun da aka yi wanda fenti ne fari sai rubutun kalar tsanwa an rubuta *MADRASATUL-AMRAH BNT ABDALLAH.* Da larabci aka yi rubutun sai kuma daga ƙasa aka rubuta da hausa.
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa bayan ta gama karantawa ta gyaɗa kai hawaye na zirara daga idanuwanta.
Cikin makarantar ta nufa kai tsaye ta nufi ajinsu mai suna *FASLUL-KHAMIS (ALIYU BN ABI ƊALIB)*
Jiki a mace ta zauna kujerar gaba wadda ita ce kujerarsu. Saurin goge hawayenta ta yi jin Jidda na faɗin "To uwar hawaye. Wani abun ne hala?"
Murmushi ta ƙirƙiro tare da faɗin "Babu komai Jidda. Me kika gani?"
"Fuskarki na gani kamar kin yi kuka. Kuma na san baya miki wahala dama." Jidda ta faɗa bayan ta dawo bisa kujerar ita ma ta zauna.
"Ko kaɗan ban yi kuka ba. Iskan nan da ake ne ina hanya ƙura da ƙasa suka buɗaɗe ni har cikin ido. Shi yasa idona ya canza launi, kuma ga raɗaɗi da yake yi min."
"Allah sarki! Ba laifi kam ana iska. Allah Ya kyauta. Yau kin makara, lafiya dai ko?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Na yi lecture ne 2-4, ina dawowa a makare ko abinci ban tsaya na ci ba na taho Kuma gashi ma ashe malam bai shigo ba."
Kafin Jidda ta bata amsa sai ga wani malami ya shigo hannunshi riƙe da Umdatul-ahkam.
Bayan ya yi sallama sun amsa ne suka gaishe shi tare da fito da littattafansu suka buɗo dai-dai inda zasu tashi.
Ɗaya bayan ɗaya sai da kowa ta karanto inda aka masu baya sannan malamin mai suna Malam Yusuf ya yi masu ƙari kasantuwar ya ga mafi rinjaye sun fahimci darasin da ya gabata.
Yana fita Mallam mai Fiqhu ya shigo shima ya masu darasin sannan aka tashi daga makarantar.
Bayan sun fita sai da budurwar ta sake ɗaga dara daran idanuwanta ta kalli sunan Islamiyyar cike da tausayi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta tafi gida. A zuciyarta tana mai tsananin ƙagara ranar jumu'a ta yi.
***
Da sallamarta ta shiga gidansu wanda yake ba wani babba sosai ba, sai dai daka ga gidan ka san suna da rufin asirinsu bakin gwargwado.
Wata matashiyar mata wadda ba zata wuce shekara talatin da biyar (35) ba ta amsa sallamar tana murmushi ta ce "Maryama an dawo?"
"Na dawo Mama. Aiki ake?" Ta tambaye ta bayan ta ƙarisa shiga Kitchen ɗin.
"Wallahi kuwa. Abbanki ne ya kirani wai yana son tuwon dare, shi ne fa na tashi da azama na ɗora masa. Har ma na gama tuwon miya ce ta rage." Maman tata ta faɗa tana zuba man-ja a tukunya.
"Kawo na ƙarisa miki Mama." Maryama ta cire hijabinta ta rataye a kan ƙofar kitchen ɗin haɗe da jingine jakarta jikin bangon kitchen.
"A'a Maryama. Ke da kika dawo daga makaranta? Na tabbata a gajiye kike, saboda ko abincin rana baki ci ba kina dawowa daga lecture kika yi shirin islamiya. Je ki cire Uniform ki zo kafin nan na zuba miki abinci."
"Wallahi Mama bana jin yunwa. Ki kawo na miki tun da dai ba wani aiki nake ba. Kullum ina makaranta ke ce kike yin komai. Dan Allah ki bari ni ma yau na samu wannan ladar."
Mama ta murmusa ta ce "Tun da dai kin matsa gashi nan ki ƙarisa. Allah Ya miki albarka ke ma Ya haɗa ki da wanda zasu kyautata miki kamar yanda kike kyautata min."
"Amin Mama." Ta faɗa haɗe da karɓar ludayin miyar ta kwashe jajjagen tarugu da albasa da daddawa dake cikin turmi.
Cike da natsuwa Maryama ta kammala miyar busasshiyar kuɓewa ta barta a buɗe dan kar ta rufe ta tsinke.
Hijabi da jikarta ta ɗauka sannan ta nufi ɗakinta domin gabatar da sallar magrib.
Bayan ta gama ta zauna ta yi adhkar har lokacin isha'i ya yi sannan ta fito sanye da dogon hijabi har kasa ta nufi ɗakin Abbanta.
Zaune yake shi da Mamanta sai kuma ƙaninta zaune a kasa.
Cikin ladabi ta gaishe da Abban nata sannan ta ce "Sannu da hutawa Mama." Ta zauna a ƙasa kusa da Muhammad.
"Yauwa Maryama. Ai ke ke da sannu." Ta mata murmushi.
"Yaya Maryama sannu da aiki." Muhammad ɗan kimanin shekara goma sha biyu ya faɗa.
"Yauwa ɗan albarka. Ya tahfiz ɗin?" Ta tambayeshi.
"Akwai wahala Yaya. Ko yau na sha zana duba bayana ki gani." Ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaga rigarshi ta baya.
"Ba sai ka ɗaga min ba dan ba tausayinka zan ji ba. Ban san me ya sa ba Muhammad baka son karatu." Ta faɗa bayan ta haɗe fuskarta babu alamun wasa.
Cikin sigar a tausaya masa ya ce "Ina fa karatu Yaya. Malamin namu ne..." Ta yi saurin dakatar da shi,
"Kar ka ma malaminku sharri. Idan baka masa laifi ba ai ba zai dake ka ba. Ka ringa karatu sosai kuma ka guji aikata laifi ka ga idan akwai malamin da zai taɓa lafiyarka."
Shiru ya yi kafin ya yi dariya abinku ga ƙaramin yaro ya ce "Kuma fa Yaya kin yi gaskiya. Kin ga Haneef shugaban ajinmu ba'a dukansa saboda kullum sai ya bayar da harda babu tangarɗa. Kuma baya laifi ko kaɗan."
"Ka gani ba. Kai ma sai ka yi koyi da shi ai, idan baka son duka." Ta faɗa tana masa murmushi.
"To Yaya. Bacci nake ji ma." Ya yi hamma.
"Bara na kawo mana tuwo sannan kaci ka yi bacci ko?" Ta miƙe tsaye.
Mama ta ce "Ai ni dai kawaici na yi dan na ga kuna fira da Muhammad. Yunwa nake ji wallahi."
Abba ya ce "To ai gashi nan zata kawo yanzu" Ya murmusa.
Ta nufi kitchen tana murmushi.
Misalin karfe tara suka kwanta kamar yanda suka saba da wuri suke kwanciya bacci gidan.
*RANAR JUMU'AH 10th January 2015*
Ranar da Maryama ke tsumaye ke nan. Ranar data matsu ta yi har tana ganin tsayin wannan ranar.
Pinky durling💗
YOU ARE READING
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."