part 53/54

3.6K 143 1
                                    


[3/23, 7:31 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝K̥ͦḀͦRྂUྂW̆Ă CིE💝ི...... 53/54*


     _wrítíng вч_
*👄hαвíєвαh luv👄*

    _єdítíng вч_
*💅ѕαdnαf💅*


💝💝💝💝💝💝💝💝💝

*ᑕ* ikin wani irin taku mai diri wanda kamar zai fasa gurin  yake nufarta, baya2 take a rude tana bashi hakuri ."don Allah katsaya kaji, ba'abinda kake tunani bane.. Wani wawan naushi yakaima bakinta wanda ya haddasa hakwarenta biyu suka fita, damko gashin kanta yayi yahada da bango tare shake mata wuya da dayan hannun ...  Lokaci daya jini yafara zuba daga bakinta kamannin fuskanta suka fara sauyawa.
Shima yazid fuskansa kaurewa yayi, idonsa yay jaa don matukar bacin rea. "Meyasa kikamin basaja i'ya zubaida!?, meyasa kika zomin amatsayin kamila bayan ke tamba daddiya ce! Fasika!, mazina ciya!, maciya amana!... Meyasa kikamin hakaaa!!!!??." Wani jakin mari yakifa mata har saubiyar saida kumatun ya fashi. Wani azababben ihu tasaki wanda saida duka gidan yadauka.
Kamar a mafarki zahra kejin ihu, a hankali tabude ido nuwanta dasukayi jaa suna mata nauyi.  Gefe guda take jiyo sautin kuka gakuma kakkausar muryan yazid natashi.  Kokarin mikewa tafara, amma dasauri takoma takwanta sakamakon wani ubun radadi dataji gabanta na mata.
Muryan zubaida taji cikin wahala da galaibaita tana cewa ..."zan mutu...zaka kasheni...don Allah kiyi..hakuri ....momyna..balaifina bane.. Laifin iyaye nane...suna sana diyyar shigana karuwanci...!".
Zaro i'do zahra tayi *Karuwanci!?*, zubaida mai hijabi!."
Innalillahiwainnailaihirrajiun." Da kyar tatashi tana shije lips tashiga dakin yazid. Wayarshi taga kan kado karasawa tayi tana tafiya kamar 'yar kaciya tadauka takira layin mami. Saida tai kusan tsinkewa sannan Miami ta daga duk a tunaninta yazid ne. Cikin kidimewa zahra tace "mami dan Allah kizo,,,,kizo yanzu ya yazid zaiyi kisa."   A zabire mami tatashi daga kwancen datake "kisa kuma zarah?." "Eh....Miami,,,don Allah kizo yanzu.." Daga haka takashe wayar. Mami gyalenta kawai tazara tafice daga dakin.. Driver tashiga kwallama kira yazo aguje suka tafi gidan yazid.
Acikin mota mami takira wayar faruq ,bugu daya yadaga yaraka kunnashi tare da sallama ...ko amsa sallamar batai ba tace "faruq kasameni gidan mahaukacin abokin naka, don zaikashe 'yar mutane.." Daga haka tai kit takatse kiran..
Makullin motarsa kawai yadauka yafita yashiga yatafi.

Acan kam yazid sai dukan hauka yakema zuby sumanta biyu tana farfadowa haka kuma yaci gaba da jibgarta. Zahra kam koda tagama waya da mami dakinta takoma takwanta ..zuwan Yusuf kawai take jira tabar wannan masi faffen gidan.

A guje motarsu mami  shigo gidan  dagudu driver nta yashiga fαlσn mami nabiye dashi . dakyar kake jiyo murya zubaida dake wahalallen ihu duk murчαntα tagama dashewa. Haurawa sama yayi yabi direction din dakejiyo ihun still mami nabiye dashi.
Dagudu yashige cikin dakin ganin zubaida kwance kamar gawa shima yazid baibar jibganta ba. Dagyar driver n ya fizgeshi ya hankad'a shi gefe .."bakada hankali ne yazid,,, kisan kai zakayi?."  Gadan2 yazid yakara nufosu yana kokarin fizgo ta, wani uwar tsawa mami tadaka masa wanda i'ta tayi sanafiyyar  farfadowar zubaida.
Ba ihu ba ,hawaye, amma daka ganta kaga wanda yashiga bala'i da tashin hankali.
Rarimar wayarta tayi dagudu tashige bathroom tasa key.
Anyi sa'akwa tana kunne bata mutuba, dailing no. Din Momy tayi bugu biyu tadaga .."sai a sannan wani bala'in kuka yazoma zubaida. Akidime Momy ke tambayarta.."Momy don Allah kizo...yazid zai kasheni..wllh kasheni zaiyi momy..kizo."   Katse wayar Momy tayi tashiga neman layin daddyn zuby. Kintafiya kiran yayi  don haka tazari mayafinta tafita driver yaja suka tafi.
Gidan mama tace yafara kaita, ko get din ba'a budeba Momy tafita dagudu tashiga tana kwalama mama kira.
Duk suna zaune dining suna break suka jiyo ihon momy..  Arman ne yafara  isa gunta yana tambaya lpy. Janshi Momy tafarayi tana magannanu wasuma bazaka ganeba "arman kazo muje,,kazo muje..zubaida ta...zai kashemin ita...don Allah kazo ka kwaceta..."
"Momy waye zai kasheta!?." "Mijinta..mijinta arman..kazo muje.."
Ficewa sukayi mama ma tadauko maya finta tabisu.

💝KARUWA CE💝Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz