💔💔KAR KA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)Ummu Subay'a
Wattpad : Ummu Subaya
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
0⃣2⃣
"Super Son ban yarda da wannan wayon ba, ni baxaka daureni da jijiyoyin jikina ba, kawai Mallam idan xakaje ka nemo mata da kanka kaje ka nemo"
Cewar Nani dake xaune akan cushion yayinda Shattema ke kwance ya dora kansa akan cinyarta
"Super Nani nifa har yanxu ban samu wacce nakeso ba, kawai ki dubi wacce ta dace dani ki auramin"
Cewar Shattema yana latsa wayarsa
Karar saukowar Khausar ne ya hana Nani magana, shi kuma Shattema ya xuba ido a inda yake sammanin bayyanarta
Sanye take da Navy blue Hijab mai hannu har gwiwarta, ga side bag data makala a gefen kafadarta bbu wani make up a fuskarta sai xallan kyaunta da kuma murmushin da ta kawata fuskarta dashi
Cikin sanyin muryanta tace
"Super Nani xan wuce"
Dubanta Nani tayi tace
"To Super Khausar sai kin dawo"
Shattema daya xuba mata ido yana jinjina sanyin hali irinta Khausar yace
"Baby jeki bedroom dina ki daukomin keyn Motata sai na kaiki"
Murmushinta mai matukar kyau ta sakar masa tace
"Xanfi kowa farin ciki idan har ka kaini, amma na yafe xanje da kaina yanxu lokacin hutawarkace ka huta lfy"
Harararta Shattema yayi yace
"Baby kinga banason wannan manyancenkin, ki wuce ki dauko min abunda na aikeki"
Murmushi Nani tayi tace
"Kema Super Khausar da neman magana kike, mutuminda kinsan ba'an sashi ba'an hanashi har sai kin tsaya bata lokacinki"
Daria Khausar tasa ta haura bedroom din Shattema
Bata wani jima ba ta fito dauke da keyn, mikewa Shattema yayi yama Nani peck a goshi, itama Khausar tayi mata suka fice
Da murmushi Nani ta rakasu, meye kuma ta tunane sai ga hawaye ya fara sintiri akan fuskarta, tissue ta dauka ta goge hawayen a hankali tace
"Ya Allah ka taimakeni kada abunda nake xargi ya xama gaskia"
A natse Shattema ke tuki yayinda kira'ar Sheak Faris Abbad ke tashi a hankali, ga kuma kamshin tularensa dana Khausar wadda ya hadu da sanyin AC sai ya bada wani yanayi mai dadi, jefi jefi Shattema ke satar kallon Khausar wadda ta limshe idonta takebin kira'ar a hankali
Wani abu ta tuna yasata bude idonta ta dubi Shattema dake kallon hanya tace
"Baby pls wannan karon ka daure ka rakani orphanage house nan muyi celebrating birthday na a can, kaga kullum sai dai na sameka a hospital baka taba rakaniba"
Sanda ya yanka junction na shiga Unimaid kan ya dubi Khausar
"Hakan xai saki farin ciki Baby?"
Murmushi tayi tace
"Xai sani farin ciki ssai Baby, kuma idan kaje dole imaninka ya karu idan kaga jariran yara na kuka bbu mahaifiyarsu, ga yara gwanin ban sha'awa basu taba jin dumin Mahaifiyarsu ba, basu samu kulawa irin wadda Nani ta bamuba"