Page Three

951 78 3
                                        

💔💔KAR KA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)

Ummu Subay'a

Wattpad : Ummu Subaya

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝🏻

 
                0⃣3⃣

Khausar na karasowa Shattema ya tashi tsaye yace

"Baby wannan kyaun yayi yawa ssai"

Murmushi tayi mai kayatarwa tace

"Nagode Baby"

Key motarsa ya mika mata ta Karba, suka jera kamar Wata da Zahra

Suna Isa parking space ya dubeta

"Baby kefa xakiyi driving dinmu yau banajin driving"

Fari tayi da ido tadanyi Salle

"Yeeeeh Happy me, yau xanyi driving Baby, ina xamu fara xuwa Hospital ko orphanage"

" mu fara xuwa hospital din xanfi"

Cewar Shattema yana shiga motar, itama Khausar Motar ta bude ta shige

Kai tsaye Hospital suka nufa, suna isa Shattema ya kira cleaners sukaxo suka kwashi abubuwan da suka kawo Ward Ward suka shiga bi suka rabawa patients abubuwan da suka kawo da musu ya jiki

Lokacinda suka shiga ward one ganin irin halinda patients ke ciki yasa Khausar sa kuka mai tsanani, tausayinsune ya kamata, duk wani bangaren data duba bbu dadi, daga masu oxygen sai kuma masu juye juye saboda axabar radadin da suke sha

Rungume Shattema Khausar tayi tana sheshsheka, rabata da jikinsa Shattema yayi ya kama hannunta ya fitar da ita daga ward din, abubuwan da suka kawo ya nawa wata nurse taje ta rabawa wadda ke jinyarsu

Tundaga hospital Khausar keta kuka har sanda suka kusan gidan Marayu kan Shattema ya gangara gefen titi yayi parking, handkerchief dinsa ya cire ya shiga share mata hawaye

"Pls Baby kukan nan ya isa, wancan karon ina kin min alkawari baxaki sake kuka ba idan kin shiga ward one"

Cikin muryan kuka Khausar tace

"Kayi hakuri Baby nima ban san lokacin da kuka yaxomin ba, kawai na tsinci kaina inayine, a duk lokacinda nayi toxali da majinyata hankalina na tashi tausayinsu na kamani, sai inga lallai mu muna butulcewa Allah daya bamu rai da lfy tare da arxiki amma a hakan muke sa6a mishi muke yadda mukaga dama muke wasa da ibada muke hana jikkunanmu bauta mishi, bama tunanin haduwarmu dashi bama tunanin akwai  ranar tonun asiriba bama tuna akwai mu.........."

Kukane yaci karfinta ya hanata karasa maganarta

Rintse idanuwanshi Shattema yayi maganganun Khausar na bin xuciarshi

Kuka tayi mai isarta bai hanata ba tunda yasan koya hanata xaita cinta a cikine, sanda ya tabbatar ta ji sanyi a ranta kan ya share mata hawayenta yaja tada motar ya hau kan titi shima idonsa yayi ja ssai

"Baby ina bidar ganin kayataccen murmushin nan"

Murmushin tayi mai matukar burgewa amma bata ce komai ba har suka shiga gidan marayun

Tsayawa kallon ikon Allah kawai Shattema yayi yana kallon yadda yaran marayun da manyansu da kana nan su suka kewaye Khausar suna mata oyoyo, ita kuma tanata daukar kananansu tana dagawa sama, yayinda fuskarta ke dauke da murmushinta na Al'ada kamar ba ita ta gama kuka yanxuba

Office na shugaban orphanage din suka isa, itama da murnan ta ta taresu, gabatarda Shattema Khausar ta mata

"Momy wannan shine Yayana Dr Shattema, Baby ga shugaban orphanage Momy Rukayyat"

Karka GujeniWhere stories live. Discover now