Page One

3.4K 155 9
                                    

💔💔KARKA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)

Ummu Subay'a

Wattpad : Ummu Subaya

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝🏻

  Bismillahir Rahmanir Raheem

                0⃣1⃣

A hankali suke takawa kamar basason tafiar, 'yan mata biyune sanye da dogayen Hijab iri daya daga gani daga islamiya suke

"Wai nikam Maryam meyasa baxaki bawa Usman dama bane, wlh yana sonki ssai"

Wadda aka kira da Maryam ta harari wacce ta mata magana

"Wai nikam Zuhra makanta kikayine, ki dubeni up and down na miki kama da mai sauraran Usman, aka gaya miki ni kece mai xubda ajinta ta wani makalewa matsiyaci idan anyi magana kice soyayya ce"

Murmushi Zuhra tayi tace

"Maryam kenan wannan shi ake kira True love, da talaucinshi na ganshi kuma nake sonshi, kuma ya cancanci asoshi ai"

Tsaki Maryam taja tace

" wlh wataran sai kinyi danasani akan wannan xabin naki, abunda yafi bakantamin ma ga talauci ga xafin ran tsiya, anya Taheer nan ba sihiri ya mikiba kuwa"

Daria Zuhra ta saka tace

"Sihirin soyayya ba, wlh kwarewanshi a soyayya shi ya mantar dani komai da kowa bana ganin kowa sai shi"

Baki Maryam ta tabe tace

"Allah ya wadaran naka ya lalace nidai Maryam wlh ko mai wankin gidana baxan dauki Taheer ba balle kuma miji, duk da wannan kyaunshi wlh baxai tsayeniba"

Kai Zuhra ta kada tace

"Abincin wani guban wani nidai a haka nakeson abuna"

A daidai lokacin suka iso kofar gidansu Maryam, Maryam ta bude gate dinsu tace

"Gobe kiyi tafiarki lesson kada ki jirani don baxan samu damar xuwaba, xanje gidan Anty Aina'u"

Harara Zuhra ta watsa mata tace

"Yanxu xuwan gidan Anty Aina'un ne xai hanaki xuwa lesson, kuma a hakan kike cewa sai kinyi masters"

Daria Maryam tasa tace

"Thank God ba aure nace xanyiba kinga bbu dalilin daxai hanani Master's, amma wadda tasa aure a gabanta da alamu  daga secondary nan ma ta gama karatunta"

Tafia Zuhra ta shiga yi

"Naga yau da magana kike nemata, ai aure baya hana karatu duk xanyisu, ki gaidamin da Umma"

Shigewa cikin gidansu Maryam tayi tace

"Zataji nima ki gaidamin Momy"

Zuhra bata tanka mata ba taci gaba da tafiarta cikin natsuwa

*******************************

Dattijuwace da baxata wuce shekara 50 ba xaune a makeken falo wadda kayan alatun xamani ya kawata falon, gefenta wata matashiyace da baxata wuce shekara 20 ba tana shan ice cream

Duban yarinyar dattijuwar tayi

"Khausar baxaki ajiye ice cream nan kije kici abinci mai nauyiba"

A shagwabe Khausar tace

"Ni Super Nani baxanci abinciba sai Baby ya dawo muci tare"

Murmushi Dattijuwar tayi tace

"Ba yanxu Shattema xai dawo ba sai 10pm, yanada C.S"

Karka GujeniWhere stories live. Discover now