Page Fourteen to Eighteen

3.2K 184 65
                                    

💔💔KAR KA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)

Ummu Subay'a

Wattpad : Ummu Subaya

Dedicated
Meerna Parrot
(Every where you go)

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝🏻


1⃣4⃣

BAYAN SHEKARA BIYAR

Wata yarinyace mai xubin larabawa da baxata wuce shekara 6 ba ta shiga cikin garden da gudu, ta boye a bayan bishiyar kwakwa tana murmushi

Shattema ne ya shigo Garden din daure da bakin kyale a idanunshi yana dubata, karon dayayi da bishiyar gwaiba ce tasashi Kunce kyalen a idonshi, ya hau dubata

"Babyn Baby ina kike"

Murmushi Zahra tayi ta leko Shattema, karab suka hada ido, dariya tasa ta ruga da gudu cikin gida, murmushi yayi shima ya bita da gudu

A falo ya kamata ya dagata sama yana daria

"Wana kama?"

Itama Zahra dariar tasa tace

"Babyn Baby kayi ojoro, ka cire kyalen"

Direta yayi akan cushion ya xauna gefenta yace

"Ke kika koyamin ai daxun na ganki lokacin da kika cire kyalen kan ki kamani"

Rufe idonta Zahra tayi da tafin hannunta irin kunyar nan, janye hannunta Shattema yayi yace

"Su Babyn Baby wai kunyar Baby akeji yau kuma"

Jikin shi ta hau ta kwanta tace

"Da fatan Babyn Baby bai manta da xuwa Thanksgiving day gobeba"

Jan hancinta Shattema yayi yace

"Ban manta ba Baby, amma sai naje hospital daga can sai na wuce"

Baki Zahra ta tura

"Nidai a'a kawai gobe ka fasa xuwan aiki mu tafi tare"

Shima Shattema bakinsa ya tura yadda Zahra tayi

"Tare xamu tafi na ajiyeka sai na biya wajen aiki sai na dawo"

Daria Zahra ta saka tace

"To na amince Baby"

Washegari Shattema ya shirya Zahra cikin uniform dinta ya hada mata breakfast dinta da lunch dinta ya xuba mata a flask

Xaunar da ita yayi akan cinyarsa ya shiga feeding dinta, kadan taci ta kwa6e fuska

"Baby am ok"

Shima Shattema kwa6e fuskar yace

"Me kikaci har kin koshi, pls Baby bude bakinki kici kinga xamuyi late"

A shagwa6e Zahra tace

"Abincin baiyi dadi ssai ba Baby, kaga Ameera tana kawo abinci mai dadi kuma momyntane ke dafa mata ba Daddynta ba ni kawai ka kawomin Momy tana dafamin abinci mai dadi"

Ajiye spoon din hannunsa Shattema yayi, ya mayarda kwallan dake kokarin xuba daga idanunsa

"Ki daure kici wannan xan dauko chief ya dinga dafa miki abinci mai dadi"

" ni banason chief ni Momy nakeso"

Ta karashe maganar tanason yin kuka

Yake Shattema yayi yace

"Ya isa Baby insha Allah xan kawo miki Momy"

Salle Zahra tayi a jikin Shattema

"Dat's My baby"

Karka GujeniWhere stories live. Discover now