💔💔KAR KA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)Ummu Subay'a
Wattpad : Ummu Subaya
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝🏻
0⃣6⃣"Ka bude kunnenka dakyau Shattema, Falmata xaka aura daman ka bani xabi kuma na xaba maka, sai kafara shirin xuwa xance, kuma ka goge soyayyar Khausar a xuciarka baka bbu Khausar har abada, inason har ta Allah ta kasance a gareni kada Khausar tasan bani na haifeta ba"
Dafe xuciarsa dake masa radadi Shattema yayi yace
"Shikenan Super Nani yadda kikace haka xa'ayi, xan auri Falmata tunda itace xa6inki amma duk abunda ya sameni son Khausar ne sila, baxan taba iya goge son da ya ginu tun yarinta ba, naso Khausar tun ban san meye Soba"
Rashin iya jurar jin kalaman Shattema su suka saka Nani mikewa daga cushion da suke xaune tace
"Yanxu kuma dakasan meye so ai saka cireshi, don akan faranta maka baxan sanya Khausar cikin kunciba, baxan sanya Khausar kukaba, baxan sanyata ta dinga kukan maraiciba tayiwa wasu balle ita, ban xama daya daga masu son kaiba Shattema, kuma baxan xama akanka ba, kayi hakuri kawai ka karbi Falmata, Allah ya sanya alkhairi"
Idon Shattema ne ya kada yayi ja, ssai tausayin dan nata ya kamata, hijab dinta ta saka a sanyaye tace
"Zanje gidan Yakura mu tattauna maganar, daga nan xan wuce gwaxari nayiwa matar mai gadi barka ta haihu jiya"
Kwantar da kanshi Shattema yayi yace
"A dawo lfy"
Ficewa Nani tayi jiki a sanyaye
Washegari Nani ta matsawa Shattema lallai sai ta tafi xance, badon ran Shattema yasoba da daddare ya shirya cikin shadda baki wadda akayiwa aiki da gold xare , yayi matukar kyau ssai
A corridor ya hadu da Khausar, tana kallonsa ta washe baki
"Baby irin wannan Black da kyau ina xan makale, wannan damuwar kyaun"
Murmushin gefen baki Shattema yayi yace
"A sama xaki makale, ina xuwa haka"
Gyara tsayuwarta tayi tace
"Kai dai xan tambaya, nikam wajenka xani"
Wristwatch dake makale a hannunsa ya duba 8:09 yace
"Xanje gidan Goggo Yakura ne"
"Ya Bukar ya dawone"
Khausar tayi tambayar tana dubanshi
"Bai dawoba, xanje gun Falmatane"
Take dukkan walwala da murmushin kan fuskar Khausar ya dauke, ta hada fuska ssai tace
"Zance xaka kenan?"
Kai ya daga mata yana karantar fuskarta
Baki ta tabe ta juya xata koma inda ta fito rai a hade
Cikin xafin nama Shattema ya rikota yace
"Ke meyayi xafi"
Sam Khausar ta gaxa controlling kan ta, kuka ta saka ta fada kirjin Shattema tace
"Banaso kayi aure Baby, banason wata mace ta rabeka, pls kada kaje gun Falmata wlh na tsaneta"
Ido Shattema ya xare da mamaki yace
"Meyasa bakyaso nayi aure? Meyasa bakyason na ra6i wata"
Kwantar da kanta tayi kan kirjinshi tace