💔💔KAR KA GUJENI💔💔
(Soyayya, Yaudara, Cin Amana, Hallaci)Ummu Subay'a
Wattpad : Ummu Subaya
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION🤝🏻
0⃣5⃣WANI ALAKANE KE TSAKANIN SHATTEMA DA KHAUSAR
Senator Barma Banki dan siyayane wadda yake rike da mukamin dan majalisan dattijai
Matarsa daya Dr Fateema tana aiki a asibiti
Suna xaune ne a garin Abuja, yaronsu daya Shattema
Tun daga Fateema ta haifi Shattema ta fara ciwon ciki ma tsanani aka fitar da ita kasan waje a can aka juya mata mahaifanta don idan ta kuma daukar ciki xa'a samu matsala babba
Bbu yadda batayi da mijinta ya kara aure don ya samu xuri'a mai yawa ba amma yaki yace Allah yasawa Shattema albarka
Danginsa bbu wadda yasan da zancen hakama danginta su biyunsu suka rufe kayansu, suka dau son dunia suka dorawa Shattema
Watarana Dr Fateema ta karbi haihuwar wata mata, matar na haihuwa ta mutu, aka bincika bbu kowa nata har gidan TV aka nuna hotonta bbu wadda yaxo yace ya santa, ga jaririyarta nata xabga kuka, tausayin yarinyar ya kama Dr Fateema ta nemi hukuma ta rattaba hannu ta dauki yarinyar
Ssai Senator Barma yaji dadin haka, yanajinta kamar diyar da ya Haifa, tana cika kwana bakwai aka rada mata suna Khausar
Murna Shattema ya shigayi ya samu Baby, sai yaxo yayita kallonta yana cewa Baby, haka ya dinga kiranta baby, ssai yakesonta komai Baby komai Baby
Sam Senator Barma yaki Fateema ta shayar da ita yace yana gudun bacin rana, don dole ta dinga bata madara
Sanarwa danginsu sukayi kuma senator Barma ya gargadesu da kada wadda ya fada mata idan ta girma, hadda Shattema ma aka bugawa warning
Lokacinda Khausar tayi wayo itama kominta Baby, idan xai tafi makaranta yasa kuka sai ta bishi, sun shaku ssai duk inda kaga Shattema xakaga Khausar, baida aboki sai ita, itama batada kawa sai shi
Rasuwar Senator Barma ne yasasu tattara suka koma Maiduguri gaba daya, ssai Nani yadda suke kiran Fateema take kula dasu
Shattema na gama secondary ya samu makaranta a India shida Bukar dan kanwar Abbansu Yakura
Sam Shattema yaki tafia wai xaiyi karatunshi a Unimaid bayason ya tafi ya bar Babynshi, sanda Nani ta mai Jan ido kan ya amince da tafiar a bisa dole
Har xaxxabi Khausar tayi da suka tafi, kullum gasu manne da waya suna hira, shakuwarsu har tsoro yake bawa Nani, tana addu'a Allah yasa kada ya xama soyayya don batason abunda xai saka Khausar tasan ba ita ta haifeta ba
Shattema na kammala karatunshi ya aka bashi aiki a wani asibiti dake India amma don Khausar yaki karban aikin ya dawo abinsa Nigeria
Yana dawowa abokin Babansa ya sama mishi aiki a wani asibiti dake Abuja shima yaki karba don Khausar
A Maiduguri ya samu aiki shida Bukar a asibiti daya
Lokacin Khausar ta fara karatu a Unimaid tana karanta Law don tana sha'awar xama Barrister
Tun Khausar na karama Allah ya dora mata son marayu da taimakawa gajiyayyu da tausayawa maisu wahala
Duk kudin da Nani take bata gidan marayu take kaiwa, tun gidan marayun suna daukarta a bakuwa har ta xama 'yar gida kowa ya Santa
Duk lokacin da Birthday ta yayi xata saya abubuwa masu amfani takai asibiti da gidan marayu
Khausar doguwace amma na ssai ba farace tas, tanada idanuwa farare matsakaita, hancinta dogo mai matukar kyau, lips dinta masu matukar daukan hankali fararen hakoranta su suke karawa fuskarta kyau musammsn idan tayi murmushi, tanada sanyin hali da wuya kaga bacin ranta kullum fuskarta kayace yake da murmushi