part 05

1.6K 193 3
                                    


Duk yadda Hammad yaso fahimtar da Mameh akan illar Abinda suke ta kasa fahimtar komai, kullum yaxo sede tace

Karka damu Hammad don Mami muke neman kudi saboda Kada ta tashi taji kuncin rayuwa.

Wannan yasa Hammad ya tattara su ya watsar dasu Baki daya nashi kawai idanu, Sede dukda haka idan yaga Mami tayi ba daidai ba Yana hukuntata ko kuma ya tsawatar mata.

Bangaren kawancen Mami da bilkisu, abin kullum gaba yake, seda ta kai idan driver dayake Kai Mami school yazo to se ya biya an dauki bilki tukun, haka islamiyyar da ake mata a gida taje ta gayyato bilki so daga Wannan lokacin ya zamana tare ake musu karatu, da yake suna da kai yasa malamin baya shan wahala sosae.

Ranar wata Monday an tashi da wani Irin zafi, sosae ake zafi saboda ana tsakiyar March ne. Gidan babu kowa Mameh taje enugu conference, Baba ya tafi Minna workshop, Hammad ya tafi school se ita kadai ta dawo a school, tana nan Zaune ta Fara jiyo ringing din land-line din gidan, da gudu ta nufi gurin tayi picking. Sallama tayi sannan tace

Wa ake nema?

Daga Dayan bangaren akace

Ina babanki? Ruqayya ce ko

Eh Itace, baba ya tafi.... Inama

Se tayi shiru alamun Bata sani ba

Mamanki fa?

Ta tafi enugu

Hammad fa?

School shikuma ni kadai ce fa

Ta fada sounding ta gaji da tambayoyin da yake mata

Tohm, idan Hammad ya dawo kice Baffa Nasiru ya Kira wai hajiyan jimeta ta rasu.

Abinka da yaro se tace

Tohm zan fada

Ta kifar da wayar ta cigaba da wasanta. Hammad se yamma ya dawo, shima straight daki ya wuce yayi wanka sannan ya shigo main gidan, Tana zaune Tana assignment, kallonta yayi ya girgixa Kai sannan ya kwalla kiran

Binta.....Binta

Na'am ta fada Tana fitowa daga daki, se lokacin Mami ta lura dashi tace

Yaya Hammad ka dawo?

Dan murmushi yayi yace

Na dawo Mami, kinci abinci?

Kanta ta gyada ta cigaba da assignment dinta, gefenta ya zauna haka kurum yake jin rashin jin dadi Tun safe ga faduwar gaba da yake ta fama da ita, Binta ta karaso dauke da plate taf da abinci Don Hammad akwai ci ba karya, se bottled water da tumbler dayake dama yan gayu ne tunda suna da kudi gasu yan Boko so even at that time idan Kaje xakaga everything is different, haka nima na tashi na samesu da gayunsu da kudi da suke son su Tarawa Mami.

Sede hammad yayi nak da abinci sannan Mami ta tuna sakon da aka bata hakan yasa tace

yaya hammad

Dagowa yayi yace

Ya akai Kiyi isha'i ki kwanta gobe akwai school

Kanta ta gyada tace

Dazu na dawo daga school akace na fada maka wai hajiyan jimeta ta rasu

Inji wa?

Ya fada immediately tana rufe bakinta

Wai Baffa...... Na manta nima

Da sauri ya mike ya nufi inda land-line din take ya fara dialing wani number ai kuwa aka tabbatar masa hajiya Abu ta rasu, kamar yaro haka Hammad ya koma daki Yana kuka saboda shikam Yana sonta, shi ne jikanta namiji na farko hakan yasa take sonshi shima kuma yana sonta don kusan duk zamansa a gurinta Yafi yawa Tun daga yaye ta karbe shi Sede time to time yaje gidansu, kuma dawawarshi Kano ya sa Mameh da hasiya suka dan fara shiri.

Washegari da asuba yakai Mami gidansu bilki sannan yace binta taje gida Bayan sati ta dawo saboda he feels insecure ya Barsu su biyu. A jimeta kuwa anyi kukan rashin hajiya saboda yadda take Mutuniyar arziki, babu Wanda yasan number da Za'a samu sakina ko mahmud Tunda land-line ce, su kuma basui tunanin kiran office dinshi ba Tunda dole zaiyi reporting ya isa gurin assignment din nasa, kawai concluding akai aka tashi driver Yaje ya taho dashi, yayinda akace abar sakina kawai. Haka driver ya gama zagayen shi a Minna amma ya rasa a ina zai samu Mahmud haka ya dawo jimeta lokacin anyi sadakar uku.

Bayan sati daya suka dawo Rana daya inda wannnan mummunan labarin ya iskesu, Mameh kuka Seka ce babarta ce ta rasu, haka suka garzaya jimeta, shi yayi karfin halin rarrashinta amma zuciyarsa Allah kadai yasan yadda yake jinta, babbar damuwar baiga gawar hajiya ba, if he can remember vividly last zuwan da yayi almost 3 months back kenan baije ya ganta ba, dukuwa da yawan complain din da take sosae akan rashin zuwansa amma sede yace aiki yayi mishi yawa, Sede Aiken kudi kamar me, wannan abin Ke sake taba zuciyarshi.

A kalla yanzu Mami nada shekaru Sha uku, shekara biyar kenan da rasuwar hajiya, ta zama yanmata bakace she's 13 ba saboda tanada garin jiki, komai nata inshape haka take. Kana ganinta kaga bafulatana ga tsayi ga kyau me daukar ido, sede batada hasken fulani, fatar Mameh Ke gareta, kowacce uwa ta gari da zarar 'yarta ta kai wannan mamakin ake saka mata sabon kula amma banda Mameh lokacin duniya ta Kara samuwa daga ita har Baba, Mameh ta samu aiki da NGO don haka likafa ta cigaba, babu zama yau anje sensitization, gobe mobilization jibi advocating haka Rayuwarta take, gashi Hammad tuni ya fara aiki har ya tafi masters dinshi Ukraine inda Baba da kanshi ya aika shi, se kuma ya'ya da aka dakko wajen su biyar duka Maza, Salim dan sister sakina ne, yana karatu a BUK yana radiography, Asim dan Baffa na yola ne shima BUK yake, Hafiz brother Hammad needs, Idrith shi kuma abokin Hafiz ne shi ya dawo dashi gidan, se Mujahid shikuma last born dinsu sakina ne ita take sponsoring dinsa. Gaba daya a gidan suke a quarters dinsu amma kullum suna cikin main gidan Wanda Mami ce kawai saboda Binta ta dade da aure, kuma ba'a sake kawo wata ba haka take Rayuwarta cikin Maza se wani sa'in tayi zamanta daki, Bata san komai ba, gashi dama mu yan zamanin yanzu mun fisu wayewa amma can se ayiwa yarinya aure she doesn't mean what it means by auren unlike mu da social media ta bude idanunmu.

Ranar Saturday Mameh na Zaune Sega Umman bilki tazo, da murna ta tarbe ta tace

Kiyi hkri Wallahi aiki ne Ke hanani zama Balle in leko ku, nagode da abin arziki sosae

Laa babu komai ai yiwa kaine

Umman bilki ta fada

Af kinga wannan dankunnen na siyowa bilkisu da Mami, gashi kar na manta

Mameh ta fada tana ciro karamin box daga hand bag dinta ta mikawa Umma wadda tsananin mamakin ganin gold me kyau na tsakiya yasa ta kasa fadin komai, one good side na Mameh kenan tana da kyauta sosae, abinda tayiwa bilkisu bazai taba faduwa ba

Haba Maman Mami gwal fa, abin ai se yayi yawa

Dariya Mameh tayi tace

Ni Keda godiya, bazan taba biyanku Abinda kukai wa Mami ba, nagode Allah ya saka da alkhairi.

Dama nazo akan wani zance ne

Gyara zamansu sukai baki daya suka fuskanci juna

Wanne fa?

Mameh ta tambaya

Akan zaman Mami ne cikin mazan gidannan se nake ganin Tunda Baku zama me zai hana ki samo wadda zata na zama da ita, Tunda wanda take tare dasu babu muharramin ta.

Hakane Umman bilki, nima nayi wannan tunanin Amma se naga ai abinci kawai suke shigowa ci, kinga bata fita balle ayi mata wani abin, bana son tana cudanya da wasu su bata min ita, amma zanyi tunani nagode sosae.

Haka suka cigaba da hira sannan Umma ta tafi, ta rasa gane wanne irin aiki suke haka da basuda time din kula da Yarinya kwaya daya, da haka ta isa gida zuciyrta na ayyana mata Anya hakan zai haifar da da me ido?

Nima haka nace saboda yanzu familyn su Nadia dukda bansan wacece ita ba ya fara bani tsoro. Na kagu naji Nadia ta karasa labarinta, kuma haka?

Shatuuu ♥️

MATSALARMU A YAU! Where stories live. Discover now