Part 23

1.5K 190 13
                                    


Gaba daya yanzu na tabbatar duk karya Nake zancen am tough, am strict baki daya karya ne, na yadda na kuma Yi surrender cewar zan karba koma menene ya faru cikin rayuwata.

Ranar asabar ce bamuda lecture Baki daya Daga ni har Rafee'ah, muna Zaune a daki muna kallo cikin system dina se mukaji knocking, ni na Mike na bude ba tareda na tambayi waye ba, shreyya na gani tsaye tayi kyau cikin wata gown hadaddiyar gaske, color orange da silver, murmushi take min sosae kafin daga bisani kuma ta hade rai, Nikam dariya ta bani hakan yasa na bata hanya ta shige kafin na biyo bayanta. Shreyya course mate dita ce wadda muka saba da ita some months back, yar Mumbai ce Tana zaune a 4th floor, musulma ce Tana so na, duk wannan rashin kula mutanen nawa seda tasan yadda tayi muka saba har dakinta nake zuwa.

Haba Nadia, har yanxu Baku shirya ba, Bayan kunsan party din after 4 ne ko

Ta fada Tana zama gefen Rafeey, kaina na dafe ashe fa yau birthday din ta, kuma xa'ayi party don har na fadawa Anty kuma Tace muje amma mu kama kanmu

Sorry dear, Bari mu shirya, Rafeey tashi mu fita.

Wardrobe dinmu na duba na dakko mana wasu gowns suma masu kyau Anty ce ta kawo mana daga US lokacinda Taxo ganin mu. Daga sama tayi mana cif se ta kasa ne ta bude sose, tawa royal blue ce, Rafee'ah kuma fuschia pink ce powder kadai na shafa itakuwa Rafeey seda tayi touching fuskarta kafin muka sakko zuwa wani food court inda akai reserving saboda party din, anyi decorating gurin yayi kyau mutane da yawa sunje kowa yayi kyau, Tunda na shiga naji ni wani iri saboda ban Saba Zuwa ireiren garinnan ba, Amma haka nayi composing kaina muka zauna, babu yadda batayi ba akan na raka ta su gaisa da guest dinta nace

Just go Dan Allah, bana jin dadi ne.

Tab duk naci Irin nawa bansan shreyya ta fini ba seda nabi bayanta mukaje tana ta introducing dina mawa friends dinta, muna tsaye kuwa sega saurayinta yazo all the way from Goa dayake anan yake aiki kuma Dan can ne, kyakyawa ba indiye sunyi matching sosae, ta gefenshi mutane biyu ne Wanda ban kalli inda suke ba, sede gabana faduwa yake tayi, tare suka karaso inda muke tsaye hakan yasa na dago idona saboda abinda shreyya Tace dani, akan na dago naga jaan dinta sunyi matching, Memakon idona ya daura kan wanda aka saka ni se yayi gefe take naji numfashi na yana neman daukewa, wannan fararen idanun na gani sun zuba akaina, damke hannun shreyya nayi Ashe har sun karaso inda muke Inacan na fada duniyar tunani, seda naji anyi squeezing hannu na kafin nayi snapping out daga duniyar da na Lula. Gaisawa mukai kafin aka yanka cake da sauransu dukda komai a daddafe nakeyi.

Ana gama komai na dubi shreyya nace

Zan tafi, kaina ciwo yake min

Kai ta girgixa tace

Idan kin tafi gifts din wazai kwasa?

Don dole haka na koma na Zaune ga tsabar wulakanci Irin na Rafee'ah tabi wani saurayinta ko ince friend as she call him, shi kuma daga Bangladesh yake, sun Dan fita wajen court din don shan iska.

Ina nan Zaune baki daya kwakwalwar kaina ta toshe na rasa tunanin da zanyi hakan yasa na dakko wayata ina dannawa se jin sallama nayi, da sauri na dago kaina as expected wannan gayen ne me ido.... Lol, zama yayi opposite dina Yana fadin

Namaste

Duk yadda zuciyata Ke son amsawa haka na dake na dauke kaina don bansan me nake ji ba,

Barka da warhaka yan mata

Ya fada cikin yarenahi na hausa

Barka dae

Na fada ina kallonshi, bazaa kirashi dogo ba don mukhtar Yafi shi tsayi hakan nan shidin ba gajere bane, Sede fari ne Wanda shi ne abinda ya taimaka masa da anyi ruwan muni a gurin, idanunsa ne kadai me kyau Wanda shi ne Ke fuzgar hankalin duk wata mace da ta bari tayi katari dasu.

MATSALARMU A YAU! Where stories live. Discover now