Part 17

1.4K 188 8
                                    

Kallo daya zakamin kasan cewa akwai abinda nake jira ko kuma yake damuna, ina Zaune Kan gado Mintina kadan se na kalli wayata, Anty dake kan stool din vanity table tana gyaran wardrobe ashe tana Lura da abubuwan da nake.

Sake duban wayar Nayi a Karo na babu adadi tareda sake kunna data amma babu wani message Daga gurin mukhtar, Kwana biu kenan banji daga gareshi ba, babu kira, babu text gashi pride ya hanani kiranshi. Har yau zancen da nake muku na kammalla NECO na kuma kamar yadda Anty tai min alkawari gata tazo shekaran jiya, yau da safe taje ta dakko ni saboda Mameh ta tafi saudiyya jiya.

Har yanxu mukhtar bai fada min cewa Yana so na ba, Sede babu Abinda ya canza zani daga kiranshi, caring dinshi wanda ya saka zuciya ta budewa baki daya tayi masa kyakyawan masauki, ni kaina ina mamakin yadda zuciyata tayi melting da wuri haka, ina son shi Irin so me tsanani nan, saboda mukhtar deserve to be loved. Ko awa daya mukai da mutum se yasan mukhtar is a very special person kamar yadda nake special a gurin sa, Abinda yake damuna tsoro nake Kada ace mukhtar ba sona yake ba kada ace kanwa ya daukeni tabbas idan haka ta Faru nasan am no more, zuciya ta fashewa zatayi saboda inajin idan na rabu da mukhtar .......i don't wants to imagine it ma kawai. To tun ranar da Anty Taxo gaba daya bai kirani ba ranar kam na axabtu ga ego da pride sun hanani naji yadda yake, jiya ma haka dalilin da yasa murnar zuwan Anty ma kadan nayi saboda Baki daya na kasa nutsuwa inajin zuciyata da gangar jiki na kamar an zazzare musu kuzarin dake cikin su.

Baby..... Baby

Da sauri na kalli Anty wadda ta baro Kan stool din ashe tazo inda nake, bansani ba wai tana tayi min hira amma na mata shiru hakan yasa ta sakko zuwa inda nake ta taba ni, da sauri na dubeta itama kallona take, dauke kaina nayi ina murmushi hakan yasa tayi murmushi ta zauna gefe na tareda fadin

Baby if you miss him, call him why so much pride?

Ta fada Tana miko min wayata dake gefe na, abinka da rashin gaskiya take na duburburce na fara fadin

Ni?.... wa? .......kai Anty

Dariya tayi ta sake gyara zamanta Tana fadin

Baby shekarar ki nawa?

Sha bakwai

Na fada ina dauke kaina saboda gaze dinta yana sawa inajin kamar banida gaskiya

Baby, ni na haifeki dukda ban zauna dake ba amma nasan idan kina cikin damuwa, yanzu fada min waye shi? A ina kuka hadu?

Kafin nayi wani abu Hanifa ta shigo tana fadin

Anty badai bakisan uncle mukhtar ba, amma gaskiya Adda da uncle bashir sun yaudareki

Anty wadda Ke ta murmushin jin dadi ta kalleni ta kalli Hanifa sannan tace

Baby Manya, Bari zan nemi bashir din da safe Tunda kinki fada min.

Da sauri nace

Anty Allah Karki biye Hanifa, ba soyayya muke ba

Hanifa na dariya tace

Kai Adda, uncle mukhtar din kike denying

Pillow na wullo mata ina fadin

Gidan mu zan tafi tunda kun hade min Kai

Suna dariya dukkansu Sega daddy ya shigo, kallonsu yayi kafin ya kalle ni yace

Nadia Kada ki cemin Ke sukewa dariya haka?

Sake turo Baki nayi nace

Gidan mu zan tafi

Murmushi yayi kafin yace

Kyallesu daughter yi hakuri kinji?

Mikewa Anty tayi tai kissing goshi na tace

A sauke pride dinnan a Kira Abinda zuciya Ke so, seda safenku.

MATSALARMU A YAU! Where stories live. Discover now